29 | GEN 1:29 | Sa’an nan Allah ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da ’ya’ya masu kwaya da suke a fāɗin duniya, da dukan itatuwa masu ba da ’ya’ya, don su zama abinci a gare ku. |
202 | GEN 8:18 | Sai Nuhu ya fito tare da matarsa da ’ya’yansa maza da matan ’ya’yansa, |
207 | GEN 9:1 | Sa’an nan Allah ya sa wa Nuhu da ’ya’yansa maza albarka, yana ce musu, “Ku haifi ’ya’ya, ku ƙaru, ku kuma cika duniya. |
214 | GEN 9:8 | Sai Allah ya ce wa Nuhu da ’ya’yansa, |
596 | GEN 24:4 | Amma za ka tafi ƙasata da kuma cikin ’yan’uwana, ka samo mata saboda ɗana Ishaku.” |
622 | GEN 24:30 | Nan da nan da ya ga zoben hancin da woroworo a hannuwan ’yar’uwansa, ya kuma ji Rebeka ta faɗa abin da mutumin ya ce mata, sai ya fita zuwa wurin mutumin, ya same shi yana tsaye wajen raƙuma kusa da rijiyar. |
651 | GEN 24:59 | Saboda haka suka sallame Rebeka, ’yar’uwarsu, duk da uwar goyonta da bawan Ibrahim da mutanensa. |
809 | GEN 29:13 | Nan da nan, da Laban ya sami labari game da Yaƙub, ɗan ’yar’uwarsa, ya gaggauta yă sadu da shi. Sai ya rungume shi ya sumbace shi, ya kuma kawo shi gidansa, a can kuwa Yaƙub ya faɗa masa dukan waɗannan abubuwa. |
832 | GEN 30:1 | Sa’ad da Rahila ta ga cewa ba tă haifa wa Yaƙub ’ya’ya ba, sai ta fara kishin ’yar’uwarta. Saboda haka ta ce wa Yaƙub, “Ka ba ni ’ya’ya, ko kuwa in mutu!” |
834 | GEN 30:3 | Sa’an nan ta ce, “Ga Bilha, mai baiwata, ka kwana da ita don tă haifa mini ’ya’ya, ta gare ta kuwa ni ma in gina iyali.” |
839 | GEN 30:8 | Sai Rahila ta ce, “Na yi kokawa sosai da ’yar’uwata, na kuwa yi nasara.” Saboda haka ta kira shi Naftali. |
857 | GEN 30:26 | Ba ni matana da ’ya’yana, waɗanda na bauta maka dominsu, zan kuwa tafi. Ka dai san yadda na bauta maka.” |
917 | GEN 31:43 | Laban ya amsa wa Yaƙub, “Matan, ’ya’yana ne, ’ya’yansu, ’ya’yana ne, garkunan kuma garkunana ne. Dukan abin da kake gani, nawa ne. Duk da haka me zan yi a rana ta yau ga waɗannan ’ya’yana mata, ko kuma ga ’ya’yan da suka haifa? |
975 | GEN 33:14 | Saboda haka bari ranka yă daɗe yă sha gaban bawansa, ni kuma in tafi a hankali bisa ga saurin abin da ake kora a gabana da kuma saurin ’ya’yan, sai na iso wurinka ranka yă daɗe, a Seyir.” |
1010 | GEN 34:29 | Suka kwashe dukan dukiyarsu da dukan matansu da ’ya’yansu, suka kwashe kome da yake cikin gidaje. |
1086 | GEN 37:2 | Wannan shi ne labarin zuriyar Yaƙub. Yusuf, saurayi ne mai shekara goma sha bakwai. Shi da ’yan’uwansa, wato, ’ya’yan Bilha maza da kuma ’ya’yan Zilfa maza, matan mahaifinsa suna kiwon garkuna tare. Sai Yusuf ya kawo wa mahaifinsu rahoto marar kyau game da ’yan’uwansa. |
1089 | GEN 37:5 | Sai Yusuf ya yi mafarki, sa’ad da ya faɗa wa ’yan’uwansa, suka ƙara ƙin jininsa. |
1094 | GEN 37:10 | Sa’ad da ya faɗa wa mahaifinsa da kuma ’yan’uwansa, sai mahaifinsa ya kwaɓe shi ya ce, “Wanne irin mafarki ne haka da ka yi? Kana nufin ni da mahaifiyarka da ’yan’uwanka za mu zo gabanka mu rusuna maka?” |
1101 | GEN 37:17 | Mutumin ya amsa, “Sun yi gaba daga nan. Na ji su suna cewa, ‘Bari mu je Dotan.’ ” Saboda haka Yusuf ya bi bayan ’yan’uwansa, ya kuwa same su kusa da Dotan. |
1107 | GEN 37:23 | Saboda haka sa’ad da Yusuf ya zo wurin ’yan’uwansa, sai suka tuɓe masa rigarsa, rigan nan mai gwanin kyau da ya sa, |
1110 | GEN 37:26 | Yahuda ya ce wa ’yan’uwansa, “Me zai amfane mu in muka kashe ɗan’uwanmu muka ɓoye jininsa? |
1260 | GEN 42:7 | Nan da nan da Yusuf ya ga ’yan’uwansa, sai ya gane su, amma ya yi kamar baƙo, ya kuma yi musu magana da tsawa. Ya tambaya, “Daga ina kuka fito?” Suka amsa, “Daga ƙasar Kan’ana, don mu saya abinci.” |
1261 | GEN 42:8 | Ko da yake Yusuf ya gane ’yan’uwansa, su ba su gane shi ba. |
1266 | GEN 42:13 | Amma suka amsa suka ce, “Bayinka dā su goma sha biyu ne, ’yan’uwa, ’ya’yan mutum guda maza, wanda yake zama a ƙasar Kan’ana. Ƙaraminmu yanzu yana tare da mahaifinmu, ɗayan kuma ya rasu.” |
1281 | GEN 42:28 | Sai ya ce wa ’yan’uwansa, “An mayar mini da azurfata. Ga shi a cikin buhuna.” Zuciyarsu ta karai, suka dubi juna suna rawan jiki, suka ce, “Mene ne wannan da Allah ya yi mana?” |
1362 | GEN 45:3 | Yusuf kuwa ya ce wa ’yan’uwansa, “Ni ne Yusuf! Mahaifina yana nan da rai har yanzu?” Amma ’yan’uwansa ba su iya amsa masa ba, gama sun firgita ƙwarai a gabansa. |
1363 | GEN 45:4 | Sa’an nan Yusuf ya ce wa ’yan’uwansa, “Ku zo kusa da ni.” Da suka yi haka, sai ya ce, “Ni ne ɗan’uwanku Yusuf, wannan da kuka sayar zuwa Masar! |
1374 | GEN 45:15 | Ya sumbaci dukan ’yan’uwansa, ya kuma yi kuka a kansu. Bayan haka sai ’yan’uwansa suka yi masa magana. |
1376 | GEN 45:17 | Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Faɗa wa ’yan’uwanka, ‘Yi wannan; ku jibge dabbobinku ku koma zuwa ƙasar Kan’ana, |
1383 | GEN 45:24 | Sa’an nan ya sallami ’yan’uwansa, yayinda suke barin wurin ya ce musu, “Kada ku yi faɗa a hanya!” |
1422 | GEN 47:1 | Yusuf ya tafi yă faɗa wa Fir’auna, “Mahaifina da ’yan’uwana, tare da garkunansu da shanunsu da kome da suke da shi, sun zo daga ƙasar Kan’ana, suna kuwa a Goshen yanzu.” |
1423 | GEN 47:2 | Sai ya zaɓi mutum biyar daga cikin ’yan’uwansa, ya gabatar da su a gaban Fir’auna. |
1424 | GEN 47:3 | Fir’auna ya tambayi ’yan’uwan, “Mece ce sana’arku?” Suka amsa wa Fir’auna suka ce, “Bayinka makiyaya ne, kamar yadda kakanninmu suke.” |
1474 | GEN 48:22 | Kuma gare ka, a matsayi wanda yake kan ’yan’uwanka, na ba da gonar da na karɓe daga Amoriyawa da takobi da kuma bakana.” |
1531 | GEN 50:24 | Sai Yusuf ya ce wa ’yan’uwansa, “Ina gab da mutuwa. Amma tabbatacce Allah zai taimake ku, yă fid da ku daga wannan ƙasa zuwa ƙasar da ya alkawarta da rantsuwa wa Ibrahim, Ishaku da kuma Yaƙub.” |
2082 | EXO 21:4 | In maigidansa ya yi masa aure, ta kuwa haifa masa ’ya’ya maza ko mata, matan da ’ya’yan, za su zama na maigidan, sai mutumin kaɗai zai tafi ’yantacce. |
2083 | EXO 21:5 | “Amma in bawan ya furta ya ce, ‘Ina ƙaunar maigidana, da matata, da ’ya’yana, ba na so kuma in ’yantu,’ |
2298 | EXO 28:4 | Waɗannan su ne tufafin da za su ɗinka, ƙyallen maƙalawa a ƙirji, da efod, da taguwa, da doguwar riga, da rawani, da abin ɗamara. Za su yi wa ɗan’uwanka, Haruna da ’ya’yansa, waɗannan tsarkaka tufafi, don su zama firistoci masu yi mini hidima. |
2335 | EXO 28:41 | Bayan ka sa waɗannan riguna wa ɗan’uwanka Haruna da ’ya’yansa, ka shafe su da mai, ka kuma naɗa su. Ka keɓe su domin su yi mini hidima a matsayin firistoci. |
2345 | EXO 29:8 | Ka kawo ’ya’yansa, ka sa musu taguwoyi, |
2468 | EXO 32:29 | Sa’an nan Musa ya ce, “An keɓe ku ga Ubangiji a yau, gama kun yi gāba da ’ya’yanku da ’yan’uwanku, ya kuma albarkace ku a wannan rana.” |
2692 | EXO 39:27 | Suka saƙa doguwar riga da lallausan lilin don Haruna da ’ya’yansa, aikin gwani mai saƙa, |
2945 | LEV 8:27 | Ya sa waɗannan a hannuwan Haruna da ’ya’yansa, suka kuma kaɗa su a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa. |
2993 | LEV 10:15 | Cinyar da aka miƙa da kuma ƙirjin da aka kaɗa, dole a kawo su tare da ɓangarori kitsen hadayun da aka yi ta wuri wuta, don a kaɗa a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa. Wannan zai zama na kullayaumi gare ka da ’ya’yanka, yadda Ubangiji ya umarta.” |
3261 | LEV 18:9 | “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar’uwarka, ko ’yar mahaifinka ko ’yar mahaifiyarka, ko an haife ta a gida ɗaya da kai ko kuwa a wani wuri dabam. |
3336 | LEV 20:17 | “ ‘In mutum ya auri ’yar’uwarsa, ko ’yar mahaifinsa, ko kuwa ta mahaifiyarsa, suka kuma yi jima’i, abin kunya ne. Dole a raba su a idanun mutanensu. Ya ƙasƙantar da ’yar’uwarsa kuma za a nemi hakki daga gare shi. |
3383 | LEV 22:13 | Amma idan ’yar firist ta zama gwauruwa ko sakakkiya, ba ta da ’ya’ya, ta kuwa dawo don tă zauna a gidan mahaifinta kamar matashiya, za tă iya cin abincin. |
3511 | LEV 25:41 | Sa’an nan a sake shi da ’ya’yansa, yă kuma koma ga danginsa da mallakar kakanninsa. |
3547 | LEV 26:22 | Zan aika da mugayen namun jeji a kanku, za su kuwa kashe ’ya’yanku, su hallaka shanunku, su rage yawanku, ku zama kaɗan. Wannan zai sa a rasa mutane a kan hanyoyinku. |
3744 | NUM 3:51 | Sa’an nan Musa ya ba da kuɗin fansar ga Haruna da ’ya’yansa, yadda maganar Ubangiji ta umarce shi. |
3847 | NUM 6:23 | “Gaya wa Haruna da ’ya’yansa, ‘Ga yadda za ku albarkaci Isra’ilawa. Za ku ce musu, |
3953 | NUM 8:13 | Ka kuma sa Lawiyawa su tsaya a gaban Haruna da ’ya’yansa, sai ka miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji. |
3959 | NUM 8:19 | Cikin dukan Isra’ilawa, na ba da Lawiyawa kyauta ga Haruna da ’ya’yansa, su yi hidima a Tentin Sujada a madadin Isra’ilawa, su kuma yi kafara dominsu saboda kada annoba ta bugi Isra’ilawa sa’ad da suka je kusa da wuri mai tsarki.” |
4259 | NUM 18:1 | Ubangiji ya ce wa Haruna, “Kai da ’ya’yanka, da kuma iyalin mahaifinka za ku ɗauki hakkin abin da ya shafi Tentin Sujada, kai da ’ya’yanka kaɗai za ku ɗauki hakkin aikinku wanda ya shafi firistoci. |
4566 | NUM 27:10 | In ba shi da ’yan’uwa, a ba da gādonsa ga ’yan’uwan mahaifinsa. |
4567 | NUM 27:11 | In mahaifinsa ba shi da ’yan’uwa, a ba da gādonsa ga danginsa na kusa, a kabilarsa don yă mallaka. Wannan ya zama ƙa’ida wa Isra’ilawa, yadda Ubangiji ya umarci Musa.’ ” |
4744 | NUM 32:24 | Ku gina birane domin matanku da ’ya’yanku, ku gina katanga kuma domin dabbobinku, amma fa ku cika abin da kuka yi alkawari.” |
4910 | DEU 1:16 | Na kuma umarci alƙalanku a wancan lokaci, na ce, “Ku yi adalci cikin shari’a tsakanin ’yan’uwanku, ko damuwar tana tsakanin ’yan’uwa Isra’ilawa ne, ko kuwa tsakanin Isra’ilawa da baƙin da suke zaune a cikinku. |
4944 | DEU 2:4 | Ka ba wa mutane waɗannan umarnai, ka ce, ‘Kuna gab da wucewa cikin yankin ’yan’uwanku, zuriyar Isuwa, wanda yake zama a Seyir. Za su ji tsoronku, amma ku yi hankali |
4948 | DEU 2:8 | Saboda haka muka ci gaba, muka wuce ’yan’uwanmu, zuriyar Isuwa, wanda yake zama a Seyir. Muka bar hanyar Araba, wadda ta haura daga Elat da Eziyon Geber, muka nufi wajen hamadar Mowab. |
4995 | DEU 3:18 | Na umarce ku a lokacin na ce, “Ubangiji Allahnku ya ba ku wannan ƙasa ku mallake ta. Dukan mayaƙanku za su haye da shirin yaƙi a gaban ’yan’uwanku, Isra’ilawa. |
4997 | DEU 3:20 | sai Ubangiji ya ba da hutu ga sauran ’yan’uwanku, yadda ya yi da ku, su ma suka sami ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba su, a ƙetaren Urdun, sa’an nan kowannenku zai komo ga mallakar da na ba ku.” |
5015 | DEU 4:9 | Ku kula, ku kuma lura da kanku sosai, don kada ku manta da abubuwan da idanunku suka gani, ko kuwa ku bari su fita daga zuciyarku muddin ranku. Ku koyar da su ga ’ya’yanku, da ’ya’yan ’ya’yanku. |
5090 | DEU 6:2 | saboda ku, ’ya’yanku, da kuma ’ya’yansu bayansu za su ji tsoron Ubangiji Allahnku muddin kuna rayuwa ta wurin kiyaye dukan ƙa’idodinsa da umarnan da na ba ku, da kuma don ku yi tsawon rai. |
5126 | DEU 7:13 | Zai ƙaunace ku, yă albarkace ku, yă kuma ƙara yawanku. Zai albarkaci ’ya’yanku, amfanin gonarku; hatsinku, sabon ruwan inabinku da kuma mai, ƙanana shanunku, da ’yan tumaki na tumakinku, a ƙasar da ya rantse wa kakanninku cewa zai ba ku. |
5229 | DEU 11:19 | Ku koyar da su ga ’ya’yanku, ku yi ta haddace su, sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi. |
5270 | DEU 12:28 | Ku yi hankali, ku yi biyayya da dukan waɗannan umarnan da nake ba ku, da kuma ’ya’yanku, don ku zauna lafiya, da ku da ’ya’yanku a bayanku, gama za ku riƙa aikata abin da yake daidai da kuma yake mai kyau a gaban Ubangiji Allahnku. |
5328 | DEU 15:7 | In akwai matalauci a cikin ’yan’uwanku, a duk wani daga cikin biranen da Ubangiji Allahnku yake ba ku, kada ku taurara zuciya, ko ku ƙi saki hannu ga ɗan’uwanku matalauci. |
5386 | DEU 17:20 | don kada yă ɗauki kansa ya fi ’yan’uwansa, yă kuma juya daga dokar zuwa dama, ko zuwa hagu. Sa’an nan shi da kuma zuriyarsa za su daɗe suna mulki a Isra’ila. |
5449 | DEU 20:20 | Amma fa, za ku iya sassare itatuwan da kuka sani ba sa ba da ’ya’ya, ku kuma yi amfani da su don ayyukan gina ƙawanyar, sai an ci birnin da yaƙi. |
5478 | DEU 22:6 | In kuka ga gidan tsuntsu kusa da hanya, ko a kan itace, ko kuma a ƙasa, mahaifiyar tsuntsun kuwa tana kwance a kan ’ya’yanta, ko kuwa a kan ƙwanta, kada ku kama mahaifiyar duk da ’ya’yan. |
5479 | DEU 22:7 | Za ku iya kwashe ’ya’yan, amma ku tabbata kun bar mahaifiyar tă tafi. Yin haka zai sa ku sami zaman lafiya da tsawon rai. |
5609 | DEU 27:22 | “La’ananne ne mutumin da ya kwana da ’yar’uwarsa, ’yar mahaifinsa ko ’yar mahaifiyarsa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” |
5719 | DEU 30:9 | Sa’an nan Ubangiji Allahnku zai mayar da ku masu arziki ƙwarai a cikin dukan aiki hannuwanku, da kuma cikin ’ya’yanku, da ’ya’yan shanunku, da kuma hatsin gonarku. Ubangiji zai sāke jin daɗinku yă sa ku yi arziki, kamar dai yadda ya ji daɗin kakanninku. |
5743 | DEU 31:13 | ’Ya’yansu, waɗanda ba su san wannan doka ba, dole su ji ta, su kuma koyi tsoron Ubangiji Allahnku muddin ranku a ƙasar da kuke haye Urdun ku ci gādonta.” |
5771 | DEU 32:11 | kamar gaggafar da take yawo a kan sheƙarta tana rufe ’ya’yanta, ta buɗe fikafikanta don tă kwashe su tă ɗauke su a kafaɗunta. |
5821 | DEU 33:9 | Ya yi zancen mahaifinsa da mahaifiyarsa ya ce, ‘Ban kula da su ba.’ Bai gane da ’yan’uwansa ba, ko yă yarda da ’ya’yansa, amma ya kiyaye maganarka ya tsare alkawarinka. |
5836 | DEU 33:24 | Game da Asher ya ce, “Mafi albarka na ’ya’yan, shi ne Asher; bari yă sami tagomashi daga ’yan’uwansa, bari kuma yă wanke ƙafafunsa a cikin mai. |
5867 | JOS 1:14 | Matanku, da yaranku, da kuma dabbobinku za su kasance a ƙasar da Musa ya ba ku a gabashin Urdun, amma dole mayaƙanku, su yi shirin yaƙi su haye, su yi gaba tare da ’yan’uwanku, za ku taimaki ’yan’uwanku |
5889 | JOS 2:18 | sai in kin ɗaura jan ƙyalle a tagar da kika zura mu, kuma sai in kin kawo mahaifinki da mahaifiyarki, da ’yan’uwanki, da dukan iyalinki cikin gidanki. |
6452 | JOS 22:24 | “A’a! Mun yi haka ne don tsoro, kada nan gaba ’ya’yanku su ce wa ’ya’yanmu, ‘Me ya haɗa ku da Ubangiji, Allah na Isra’ila? |
6455 | JOS 22:27 | Sai dai yă zama shaida tsakaninmu da ku, da kuma waɗanda za su zo a baya, cewa za mu yi wa Ubangiji sujada a wurinsa mai tsarki, za mu miƙa hadayunmu na ƙonawa, hadayu na zumunta. Sa’an nan, nan gaba ’ya’yanku ba za su ce wa ’ya’yanmu, ‘Ba ku da rabo a cikin Ubangiji ba.’ |
6761 | JDG 9:5 | Sai ya tafi gidan mahaifinsa a Ofra kuma a dutse guda ya kashe ’yan’uwansa, ’ya’yan Yerub-Ba’al. Amma Yotam, autan ɗan Yerub-Ba’al ya tsira ta wurin ɓuya. |
7009 | JDG 18:14 | Sa’an nan mutum biyar ɗin nan da suka leƙi asirin ƙasar Layish suka ce wa ’yan’uwansu, “Kun san cewa ɗaya daga cikin gidajen nan yana da efod, waɗansu allolin iyali, siffar da aka sassaƙa da kuma gunki na zubi? To, kun san abin da za ku yi.” |
7084 | JDG 20:28 | Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, kuwa yana hidima a gabansa.) Suka ce, “Mu sāke haura mu yi yaƙi da mutanen Benyamin ’yan’uwanmu, ko a’a?” Ubangiji ya ce, “Ku je, gama gobe zan ba da su a hannuwanku.” |
7110 | JDG 21:6 | To, Isra’ilawa suka yi juyayin ’yan’uwansu, mutanen Benyamin. “Yau an hallaka kabila daga cikin Isra’ila. |
7216 | 1SA 1:2 | Yana da mata biyu, ɗaya sunanta Hannatu, ɗayan kuwa ana kiranta Feninna. Ita Feninna tana da ’ya’ya, amma Hannatu ba ta da ’ya’ya. |
7595 | 1SA 15:33 | Amma Sama’ila ya ce, “Yadda takobinka ya sa mata suka rasa ’ya’ya, haka mahaifiyarka za tă zama marar ’ya’ya a cikin mata.” Sama’ila kuwa ya kashe Agag a Gilgal a gaban Ubangiji. |
7638 | 1SA 17:18 | Ka haɗa da waɗannan cuku guda goma, ka kai wa komandan rundunarsu. Ka ga lafiyar ’yan’uwanka, ka kawo mini labari daga wurinsu. |
8092 | 2SA 3:8 | Abner ya husata saboda abin da Ish-Boshet ya ce, sai ya ce, “Kana tsammani ni mai cin amana ne? Kana zato ni mai goyon bayan Yahuda ne? Tun farko na nuna aminci ga gidan babanka Shawulu, da ’yan’uwansa, da abokansa! Ban kuwa ba da kai a hannun Dawuda ba. Ga shi yanzu a kan mace za ka ga laifina? |
8555 | 2SA 19:42 | Nan take sai ga mutane Isra’ila suna zuwa wurin sarki, suna cewa, “Don me ’yan’uwanmu, mutanen Yahuda, suka saci sarki, suka kawo shi da iyalinsa a ƙetaren Urdun, tare da dukan mutanensa?” |
8729 | 1KI 1:9 | Wata rana Adoniya ya tafi Dutsen Zohelet kusa da En Rogel, inda ya yi hadayar tumaki, da shanun noma, da shanun da ake kiwo a gida. Ya kuma gayyaci ’yan’uwansa, wato, sauran ’ya’yan Sarki Dawuda, tare da dukan dattawan sarki da suka fito daga Yahuda, |
8941 | 1KI 7:4 | Aka kuma yi tagogi masu sandunan ƙarfe, jeri uku, kowace taga tana ɗaura da ’yar’uwarta, har jeri uku. |
9178 | 1KI 12:24 | ‘Ga abin da Ubangiji ya ce, “Kada ku haura don ku yi yaƙi da ’yan’uwanku, Isra’ilawa. Ku koma gida, kowannenku, gama wannan aikina ne.” ’ ” Saboda haka suka yi biyayya da maganar Ubangiji, suka sāke watse zuwa gida, yadda Ubangiji ya umarta. |
9200 | 1KI 13:13 | Sai ya ce wa ’ya’yansa, “Ku yi wa jakina shimfiɗa.” Da suka yi wa jakin shimfiɗa, sai ya hau. |
9214 | 1KI 13:27 | Sai annabin ya ce wa ’ya’yansa, “Ku yi wa jakina shimfiɗa.” Sai suka yi. |
9218 | 1KI 13:31 | Bayan an binne shi, sai ya ce wa ’ya’yansa, “Sa’ad da na mutu, ku binne ni a kabarin da aka binne mutumin Allah; ku kwantar da ƙasusuwana kusa da ƙasusuwansa. |
9418 | 1KI 20:7 | Sarkin Isra’ila ya tattara dukan dattawan ƙasar, ya ce musu, “Ku duba fa, wannan mutum yana neman tsokana! Sa’ad da ya aika in ba shi matana da ’ya’yana, azurfana da zinariyana, ban hana masa ba.” |
9786 | 2KI 9:26 | ‘Jiya na ga jinin Nabot da jinin ’ya’yansa, in ji Ubangiji, kuma ba shakka zan ɗauki fansa a wannan fili, in ji Ubangiji.’ Saboda haka, ka ɗauke shi ka jefar da shi a bisa wannan fegi, bisa ga faɗin Ubangiji. Saboda haka, ka ɗauke shi ka jefar a filin, in ji Ubangiji.” |
10502 | 1CH 6:29 | da kuma daga ’yan’uwansu, mutanen Merari, a hannun hagunsa. Etan ɗan Kishi, ɗan Abdi, ɗan Malluk, |