638 | GEN 24:46 | “Ta yi sauri ta saukar da tulun daga kafaɗarta ta ce, ‘Sha, zan kuma ba wa raƙumanka su ma.’ Sai na sha, ta kuma shayar da raƙumana su ma. |
1595 | EXO 3:15 | Allah ya kuma ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Ubangiji, Allah na kakanninka, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub, ya aiko ni wurinku.’ Wannan shi ne sunana har abada, sunan da za a tuna da ni daga tsara zuwa tsara ke nan. |
1596 | EXO 3:16 | “Tafi ka tattara dattawan Isra’ila, ka ce musu, ‘Ubangiji, Allah na kakanninku, Allah na Ibrahim, Ishaku da Yaƙub, ya bayyana a gare ni ya ce, Na lura da ku, na kuma ga abubuwan da ake yi muku a Masar. |
1598 | EXO 3:18 | “Dattawan Isra’ila za su saurare ka. Sa’an nan da kai da dattawan Isra’ila, za ku tafi wurin sarkin Masar, ku ce masa, ‘Ubangiji, Allah na Ibraniyawa, ya sadu da mu. Bari mu yi tafiyar kwana uku zuwa cikin hamada domin mu yi hadaya wa Ubangiji Allahnmu.’ |
1702 | EXO 7:16 | Sa’an nan ka ce masa, ‘Ubangiji, Allah na Ibraniyawa, ya aiko ni in faɗa maka, Ka bar mutanena su tafi domin su yi mini sujada a hamada. Amma har yanzu ba ka yi biyayya ba. |
1893 | EXO 14:3 | Fir’auna zai yi tsammani, ‘Aha, Isra’ilawa sun rikice cikin ƙasar, hamada kuwa ta yimƙe su.’ |
2451 | EXO 32:12 | Don me za ka sa Masarawa su ce, ‘Ai, da mugun nufi ne ya fito da su don yă shafe su daga fuskar duniya’? Ka juya daga fushinka mai zafi, ka ji tausayi, kada ka kawo masifa a kan mutanenka. |
3251 | LEV 17:15 | “ ‘Kowa, ko haifaffe ɗan ƙasa ko baƙo, da ya ci wani abin da aka sami a mace, ko naman jeji ya yayyage, dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma; sa’an nan zai tsarkake. |
3346 | LEV 20:27 | “ ‘Namiji, ko ta macen da yake mai duba, ko maita a cikinku dole a kashe. Za ku jajjefe su da duwatsu; alhakin jininsu zai zauna a kansu.’ ” |
3502 | LEV 25:32 | “ ‘Kullum, Lawiyawa suna da izini su fanshi gidajensu a biranen Lawiyawa waɗanda suka mallaka. |
3837 | NUM 6:13 | “ ‘To, ga doka saboda Banazare sa’ad da kwanakin keɓewarsa suka gama. Za a kawo shi a bakin ƙofar Tentin Sujada. |
4176 | NUM 15:22 | “ ‘To, in ku a matsayin jama’a, da gangan kuka ƙi kiyaye waɗannan ƙa’idodi da Ubangiji ya ba wa Musa ba, |
4424 | NUM 23:7 | Sai Bala’am ya furta abin da Allah ya faɗa masa ya ce, “Balak ya kawo ni daga Aram, sarkin Mowab ya kawo ni daga gabashin duwatsu. Ya ce, ‘Zo, ka la’anta mini Yaƙub; zo, ka tsine Isra’ila.’ |
6669 | JDG 6:13 | Gideyon ya ce, “Ranka yă daɗe, in Ubangiji yana tare da mu, me ya sa waɗannan abubuwa suka faru da mu? Ina dukan abubuwan al’ajabinsa waɗanda kakanninmu suka gaya mana game su sa’ad da suka ce, ‘Ashe, ba Ubangiji ne ya fitar da mu daga Masar ba?’ Amma yanzu Ubangiji ya rabu da mu ya kuma sa mu hannun Midiyawa.” |
7439 | 1SA 10:19 | Amma yanzu kun ƙi Allahnku wanda ya cece ku daga dukan masifu da wahaloli. Kuka ce, ‘Sam, a naɗa mana sarki.’ Saboda haka yanzu sai ku zo gaban Ubangiji kabila-kabila da iyali-iyali.” |
7456 | 1SA 11:9 | Suka ce wa ’yan aikan da suka zo, “Ku faɗa wa mutanen Yabesh Gileyad, ‘Gobe, kafin rana tă yi zafi, za ku sami ceto.’ ” Sa’ad da ’yan aikan suka tafi, suka ba da saƙon nan ga mutanen Yabesh, sai suka farin ciki. |
7700 | 1SA 18:22 | Sai Shawulu ya umarci ma’aikatansa cewa, “Ku yi magana da Dawuda asirce ku ce, ‘Duba, sarki yana farin ciki da kai, dukan ma’aikatansa kuma suna sonka, ka yarda ka zama surukinsa.’ ” |
7753 | 1SA 20:21 | Sa’an nan zan aiki yaro in ce masa, ‘Je ka nemo kibiyoyin.’ In na ce masa, ‘Duba, kibiyoyin suna wannan gefen da kake, kawo su,’ sai ka fito, wato, tabbatacce muddin Ubangiji yana raye, ka tsira, ba wani hatsari. |
7754 | 1SA 20:22 | Amma in na ce wa yaron, ‘Duba, kibiyoyin suna gaba da kai,’ sai ka tafi, gama Ubangiji ya sallame ka. |
8527 | 2SA 19:14 | Ku kuma ce wa Amasa, ‘Ashe, kai ba jikina ba ne da jinina? Allah yă hukunta ni, da hukunci mai tsanani, idan daga yanzu ba ka zama komandan sojojina a maimakon Yowab ba.’ ” |
9142 | 1KI 11:31 | Sa’an nan ya ce wa Yerobowam, “Ɗauki gida goma wa kanka, gama abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce ke nan, ‘Duba, zan yage masarauta daga hannun Solomon in ba ka kabilu goma. |
10051 | 2KI 18:23 | “ ‘Yanzu, ka zo ku shirya da shugabana, sarkin Assuriya. Zan ba ka dawakai dubu biyu, in za ka sami mahayansu! |
18548 | ISA 41:27 | Ni ne na farkon da ya ce wa Sihiyona, ‘Duba, ga su nan!’ Na ba wa Urushalima saƙon labari mai daɗi. |
18691 | ISA 48:7 | Yanzu an halicce su, ba da daɗewa ba; ba ku riga kun ji game da su kafin yau ba. Saboda haka ba za ku ce, ‘I, na san da su ba.’ |
19075 | JER 3:4 | Yanzu ba kin kira ni, ‘Mahaifina, abokina daga ƙuruciyata ba, |
19172 | JER 6:14 | Sukan ɗaura mikin mutanena sai ka ce mikin ba shi da matsala. Suna cewa, ‘Lafiya, Lafiya,’ alhali kuwa ba lafiya. |
19541 | JER 22:18 | Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, “Ba za su yi kuka dominsa ba, ‘Kaito, ɗan’uwana! Kaito, ’yar’uwata!’ Ba za su yi kuka dominsa ba, ‘Kaito, maigidana! Kaito, darajarsa!’ |
20148 | JER 47:6 | “Za ku yi kuka kuna cewa, ‘Wayyo, takobin Ubangiji sai yaushe za ka huta? Ka koma kubenka; ka huta, ka yi shiru.’ |
20151 | JER 48:2 | Ba za a ƙara yabi Mowab ba; a Heshbon mutane za su shirya mata maƙarƙashiya. ‘Zo, mu tafi mu kawo ƙarshe ga wannan al’umma.’ Ke kuma, ya Madmen za ki yi shiru; takobi zai fafare ki. |
20880 | EZK 16:49 | “ ‘To, fa, ga zunubin ’yar’uwarki Sodom. Ita da ’ya’yanta mata sun yi girman kai, sun ƙoshi fiye da kima kuma ba su kula da wani abu ba; ba su taimaki matalauta da kuma masu bukata ba. |
21022 | EZK 21:14 | “Ɗan mutum, yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, “ ‘Takobi, takobi, wasasshe da kuma gogagge, |
21041 | EZK 21:33 | “Kai kuma, ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa game da Ammonawa da kuma zarginsu. “ ‘Takobi, takobi, an ja don kisa, an goge don cinyewa yana haske kamar walƙiya! |
21203 | EZK 27:13 | “ ‘Girka, Tubal da Meshek sun yi kasuwanci da ke; sun sayi kayanki suka biya da bayi da kuma abubuwan da aka yi da tagulla. |
21213 | EZK 27:23 | “ ‘Haran, Kanne da Eden da kuma ’yan kasuwan Sheba, Assuriya da Kilmad sun yi ciniki da ke. |
23270 | MAT 3:9 | Kada ma ku yi tunani a ranku cewa, ‘Ai, Ibrahim ne mahaifinmu.’ Ina gaya muku cewa Allah zai iya tā da ’ya’ya wa Ibrahim daga cikin duwatsun nan. |
23406 | MAT 7:21 | “Ba duk mai ce mini, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ne zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda yake aikata nufin Ubana da yake sama. |
23407 | MAT 7:22 | Da yawa za su ce mini a wannan rana, ‘Ubangiji, Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci a cikin sunanka ba, ba kuma a cikin sunanka ne muka fitar da aljanu, muka yi abubuwan banmamaki da yawa ba?’ |
23546 | MAT 11:18 | Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo ba ya ciye-ciye, ba ya shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ai, yana da aljani.’ |
23874 | MAT 20:13 | “Amma ya amsa wa ɗayansu ya ce, ‘Aboki, ban cuce ka ba. Ba ka yarda ka yi aiki a kan dinari guda ba? |
23900 | MAT 21:5 | “Ku ce wa Diyar Sihiyona, ‘Duba, sarkinki yana zuwa gare ki, mai tawali’u yana a kan jaki, a kan aholaki, ɗan jaki.’ ” |
23920 | MAT 21:25 | Baftismar Yohanna, daga ina ta fito? Daga sama ce, ko daga mutane?” Sai suka tattauna a junansu suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama,’ zai ce, ‘To, me ya sa ba mu gaskata shi ba?’ |
23923 | MAT 21:28 | “Me kuka gani? An yi wani mutum wanda yake da ’ya’ya biyu maza. Sai ya je wajen ɗan farin ya ce, ‘Ɗana, yau tafi gonar inabi ka yi aiki.’ |
23953 | MAT 22:12 | Ya yi tambaya ya ce, ‘Aboki, yaya ka shigo nan ba tare da rigar aure ba?’ Mutumin ya rasa ta cewa. |
24049 | MAT 24:23 | A lokacin in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko, ‘Ga shi can!’ Kada ku gaskata. |
24097 | MAT 25:20 | Mutumin da ya karɓi talenti biyar, ya kawo ƙarin talenti biyar. Ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talenti biyar. Ga shi, na yi ribar biyar.’ |
24098 | MAT 25:21 | “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’ |
24099 | MAT 25:22 | “Mutumin da yake da talenti biyu, shi ma ya zo ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talenti biyu; ga shi, na yi ribar biyu.’ |
24100 | MAT 25:23 | “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’ |
24101 | MAT 25:24 | “Sa’an nan mutumin da ya karɓi talenti ɗaya ya zo. Ya ce, ‘Maigida, na san cewa kai mutum ne mai wuyan sha’ani, kana girbi inda ba ka shuka ba, kana kuma tara inda ba ka yafa iri ba. |
24114 | MAT 25:37 | “Sa’an nan masu adalci za su amsa masa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka da yunwa muka ciyar da kai, ko da ƙishirwa muka ba ka abin sha? |
24121 | MAT 25:44 | “Su ma za su amsa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka cikin yunwa ko ƙishirwa ko baƙo ko cikin bukatar tufafi ko cikin rashin lafiya ko cikin kurkuku, ba mu taimake ka ba?’ |
24338 | MRK 2:9 | Wanne ya fi sauƙi, a ce wa shanyayyen, ‘An gafarta zunubanka,’ ko a ce, ‘Tashi, ɗauki tabarmarka ka yi tafiya’? |
24740 | MRK 11:31 | Sai suka tattauna a junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai ce, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’ |
24807 | MRK 13:21 | A lokacin nan, in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko kuwa, ‘Duba, ga shi can!’ Kada ku gaskata. |
25102 | LUK 3:8 | Ku yi ayyukan da suka dace da tuba. Kada ma ku yi tunani za ku iya ce wa kanku, ‘Ai, muna da mahaifinmu Ibrahim.’ Ina gaya muku cewa daga cikin duwatsun nan Allah zai iya tā da ’ya’ya wa Ibrahim. |
25155 | LUK 4:23 | Yesu ya ce musu, “Tabbatacce, na san za ku faɗa mini karin maganan nan, ‘Likita, warkar da kanka! Ka kuma yi abin da muka ji ka yi a Kafarnahum, a nan garinka.’ ” |
25199 | LUK 5:23 | Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuma a ce, ‘Tashi, ka yi tafiya’? |
25215 | LUK 5:39 | Kuma ba wanda yakan so shan sabon ruwan inabi bayan ya sha tsohon, don yakan ce, ‘Ai, tsohon ya fi kyau.’ ” |
25261 | LUK 6:46 | “Don me kuke ce da ni, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ amma ba kwa yin abin da na faɗa? |
25297 | LUK 7:33 | Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo, ba ya cin burodi, ba ya shan ruwan inabi, sai kuka ce, ‘Ai, yana da aljani.’ |
25445 | LUK 10:13 | “ ‘Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida!’ Ai, da a ce a Taya da Sidon ne aka yi ayyukan banmamaki da aka yi a cikinku, da tuni sun tuba, suna zama cikin rigar makoki da toka. |
25479 | LUK 11:5 | Sa’an nan ya ce musu, “Da a ce ɗayanku yana da aboki, sa’an nan ya je wurinsa da tsakar dare ya ce, ‘Aboki, ranta mini burodi guda uku, |
25573 | LUK 12:45 | Amma da a ce bawan ya yi tunani a zuciyarsa ya ce, ‘Ai, maigidana ya yi jinkirin dawowa,’ sa’an nan ya fara dūkan bayin, maza da mata, ya kuma shiga ci, da sha, har da buguwa. |
25613 | LUK 13:26 | “Sa’an nan za ku ce, ‘Haba, mu da muka ci, muka sha tare da kai, har ka yi koyarwa a cikin titi-titi namu.’ |
25669 | LUK 15:12 | Ƙaramin ya ce wa mahaifinsu, ‘Baba, ba ni rabon gādona.’ Sai mahaifin ya raba musu dukiyarsa. |
25674 | LUK 15:17 | “Da hankalinsa ya dawo, sai ya ce, ‘Kai, bayin mahaifina guda nawa ne, da suke da abinci fiye da isashe, ni kuma ina nan, zan mutu don yunwa! |
25678 | LUK 15:21 | “Sai ɗan ya ce masa, ‘Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi. Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba.’ |
25684 | LUK 15:27 | Bawan ya ce, ‘Ai, ɗan’uwanka ne ya dawo, shi ne mahaifinka ya yanka ɗan saniya mai ƙiba, gama ya yi murna ya karɓi ɗansa da ya dawo gida lafiyayye, ba abin da ya same shi.’ |
25688 | LUK 15:31 | “Sai mahaifin ya ce masa, ‘Ɗana, kullum kana nan tare da ni, kuma duk abin da nake da shi, naka ne. |
25713 | LUK 16:24 | Sai ya yi masa kira ya ce, ‘Baba, Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiki Lazarus ya sa ɗan yatsarsa a ruwa, ya ɗiga mini a harshe saboda in ji sanyi, domin ina shan azaba cikin wannan wuta.’ |
25716 | LUK 16:27 | “Ya amsa ya ce, ‘To, ina roƙonka, ya uba, ka aiki Lazarus zuwa gidan mahaifina, |
25768 | LUK 18:11 | Sai Bafarisiyen ya tashi tsaye, ya yi addu’a game da kansa yana cewa, ‘Allah, na gode maka, saboda ni ba kamar sauran mutane ba ne, wato, mafasa, masu aikata mugunta, masu zina, ko kuma kamar mai karɓar harajin nan. |
25770 | LUK 18:13 | “Amma mai karɓar harajin ya tsaya daga nesa. Bai ma iya ɗaga kansa sama ba, sai ya buga ƙirjinsa, yana cewa, ‘Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi ne.’ |
25817 | LUK 19:17 | “Maigidan ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawana mai kirki! Tun da ka yi aminci a kan abu ƙanƙani, ka yi riƙon birane goma.’ |
25846 | LUK 19:46 | Ya ce musu, “A rubuce, yake cewa, ‘Gidana, zai zama gidan addu’a,’amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’ ” |
25853 | LUK 20:5 | Sai suka yi shawara da junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai tambaya, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’ |
25903 | LUK 21:8 | Ya amsa ya ce, “Ku lura, kada ku kuma a ruɗe ku. Gama da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ai, ni ne shi,’ da kuma, ‘Lokaci ya yi kusa.’ Kada ku bi su. |
26676 | JHN 12:27 | “Yanzu kuwa na damu, amma me zan ce? ‘Uba, ka cece ni daga wannan sa’a’? A’a, ai, saboda wannan dalili ne musamman na zo. |
27359 | ACT 10:31 | ya ce, ‘Korneliyus, Allah ya ji addu’arka, ya kuma tuna da kyautanka ga matalauta. |
27383 | ACT 11:7 | Sa’an nan na ji wata murya tana ce mini, ‘Bitrus, ka tashi. Ka yanka ka ci.’ |
27384 | ACT 11:8 | “Na amsa na ce, ‘Sam, Ubangiji! Ban taɓa cin wani abu marar tsarki ko marar tsabta ba.’ |
27782 | ACT 22:10 | “Sai na yi tambaya, na ce, ‘Me zan yi, ya Ubangiji?’ “Ubangiji ya ce, ‘Tashi, ka tafi cikin Damaskus. A can za a faɗa maka duk abin da aka shirya za ka yi.’ |
27791 | ACT 22:19 | “Na amsa na ce, ‘Ubangiji, waɗannan mutane sun san cewa na bi majami’a-majami’a na jefa waɗanda suka gaskata da kai a cikin kurkuku, in kuma yin musu dūka. |
27905 | ACT 26:14 | Dukanmu muka fāɗi ƙasa, na kuwa ji wata murya tana ce mini da harshen Arameyik, ‘Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini? Yana da wuya ka shuri tsinken tsokanar dabba.’ |