2062 | EXO 20:10 | amma rana ta bakwai Asabbaci ne ga Ubangiji, Allahnka. A ranar ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawa, ko baiwa, ko dabbarka, ko baƙon da yake zama tare da kai. |
2080 | EXO 21:2 | “In ka sayi mutumin Ibraniyawa a matsayin bawa, zai bauta maka shekara shida. Amma a shekara ta bakwai, za ka ’yantar da shi, yă tafi ’yantacce, ba tare da ya biya kome ba. |
2089 | EXO 21:11 | In bai tanada mata waɗannan abubuwa uku ba, sai tă tafi ’yantacciya, babu biyan kome. |
3262 | LEV 18:10 | “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar ɗanka ko ’yar ’yarka, wannan zai ƙasƙantar da kai. |
3348 | LEV 21:2 | sai dai na danginsa na kusa, kamar mahaifiyarsa ko mahaifinsa, ɗansa ko ’yarsa, ɗan’uwansa, |
5069 | DEU 5:14 | amma rana ta bakwai, Asabbaci ne ga Ubangiji Allahnka. A kanta ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawanka, ko baiwarka, ko saniyarka, ko jakinka, ko wani daga dabbobinka, ko baƙo a ƙofofinka, don bayinka maza da mata su ma su huta, kamar ka. |
5280 | DEU 13:7 | In ɗan’uwanka, ko ɗanka, ko ’yarka, ko matar da kake ƙauna, ko abokinka na kusa, a ɓoye ya ruɗe ka, yana cewa, “Mu je mu yi wa waɗansu alloli sujada” (allolin da ko kai, ko kakanninka ba su sani ba, |
6221 | JOS 15:17 | Otniyel ɗan Kenaz, ɗan’uwan Kaleb, ya ci Kiriyat Sefer da yaƙi; saboda haka Kaleb ya ba wa Aksa ’yarsa, ya kuwa aure ta. |
7192 | RUT 3:18 | Sai Na’omi ta ce, “Ki jira, ’yata, sai kin ga abin da zai faru. Gama mutumin ba zai huta ba sai an warware batun a yau.” |
7703 | 1SA 18:25 | Sai Shawulu ya ce, “Ku gaya wa Dawuda, ‘Sarki ba ya bukatan kuɗin auren ’yarsa, sai dai loɓar Filistiyawa domin ramako a kan abokan gābansa.’ ” Shawulu yana shiri ne domin Dawuda yă fāɗa a hannun Filistiyawa. |
7908 | 1SA 25:44 | Amma Shawulu ya aurar da Mikal, ’yarsa, matar Dawuda, ga Falti ɗan Layish wanda yake daga Gallim. |
9070 | 1KI 9:16 | (Fir’auna sarkin Masar ya kai wa Gezer hari, ya kuma ci ta da yaƙi. Ya sa mata wuta, ya kashe Kan’aniyawanta mazaunan wurin, ya kuma ba da ita a matsayin kyautar aure ga ’yarsa, matar Solomon. |
9926 | 2KI 14:26 | Ubangiji ya ga irin muguwar wahalar da ta shafi kowa a Isra’ila, ko bawa ko ’yantacce, babu mai taimakonsu. |
12743 | EST 2:15 | Sa’ad da lokaci ya yi da Esta (yarinyar da Mordekai ya ɗauka tamƙar ’yarsa, ’yar kawunsa Abihayil) za tă shiga wurin sarki, ba tă nemi a ba ta kome ba in ban da abin da Hegai, bābān sarki mai lura da gidan matan kulle, ya ba da shawara. Esta kuwa ta sami tagomashin kowa da ya ganta. |
21693 | EZK 44:25 | “ ‘Firist ba zai ƙazantar da kansa ta wurin zuwa kusa da gawa ba; amma, in gawar mahaifinsa ko mahaifiyarsa, ko ɗansa ko ’yarsa, ko ɗan’uwansa ko ’yar’uwarsa ce, to, ba zai ƙazantar da kansa ba. |
28576 | 1CO 7:21 | Kai bawa ne sa’ad da aka kira ka? Kada wannan yă dame ka, sai dai in kana iya samun ’yanci, sai ka yi amfani da wannan dama. |
28715 | 1CO 12:13 | Dukanmu an yi mana baftisma ta wurin Ruhu guda zuwa ga jiki guda, ko Yahudawa ko Hellenawa, bawa ko ’yantacce, an kuma ba wa dukanmu wannan Ruhu guda mu sha. |
29197 | GAL 3:28 | Babu bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, bawa da ’yantacce, namiji da ta mace, gama dukanku ɗaya ne cikin Kiristi Yesu. |
29595 | COL 3:11 | A wannan sabuwar rayuwa babu bambanci ko kai mutumin Al’ummai ne ko mutumin Yahuda, mai kaciya ne ko marar kaciya, baƙo, baƙauye, bawa ne ko ’yantacce, gama Kiristi shi ne kome, kuma yana cikin kome. |
30358 | JAS 1:25 | Amma duk mai duba cikakkiyar ƙa’idan nan ta ’yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai yă mance ba, sai dai mai yi ne yă zartar, to wannan shi za a yi wa albarka a cikin abin da yake yi. |
30372 | JAS 2:12 | Ku yi magana ku kuma yi aiki kamar waɗanda za a yi musu shari’a bisa ga doka mai ba da ’yanci, |
30482 | 1PE 2:16 | Ku yi rayuwa kamar mutanen da aka ’yantar, sai dai kada ku yi amfani da ’yancinku a matsayin hujjar aikata mugunta; ku yi rayuwa kamar bayin Allah. |
30586 | 2PE 2:19 | Suna yin musu alkawarin ’yanci, yayinda su kansu bayi ne ga aikin lalata gama mutum bawa ne ga duk abin da ya mallake shi. |