23346 | MAT 5:43 | “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka,ka kuma ƙi abokin gābanka.’ |
23706 | MAT 15:4 | Gama Allah ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,kuma duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole a kashe shi.’ |
23759 | MAT 16:18 | Ina kuwa gaya maka, kai ne Bitrus,a kan wannan dutse zan gina ikkilisiyata, kuma ƙofofin Hadesba za su rinjaye ta ba. |
24244 | MAT 27:46 | Wajen sa’a ta tara, Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi,lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”). |
24895 | MRK 14:72 | Nan da nan zakara ya yi cara sau na biyu. Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi masa cewa, “Kafin zakara yă yi cara sau biyu,za ka yi mūsun sanina sau uku.” Sai ya fashe da kuka. |