9361 | 1KI 18:17 | Sa’ad da Ahab ya ga Iliya, sai ya ce masa, “Kai ne wannan, kai mai tā-da-na-zaune-tsaye a Isra’ila?” |
9362 | 1KI 18:18 | Iliya ya amsa, ya ce, “Ban tā-da-na-zaune-tsaye a Isra’ila ba. Amma kai da iyalin mahaifinka, ku kuka tā-da-na-zaune-tsaye. Ka ƙyale umarnai Ubangiji, ka bi Ba’al. |
13573 | JOB 30:12 | A hannun damana ’yan tā-da-na-zaune-tsaye sun tayar; sun sa tarko a ƙafafuna, sun yi shirin hallaka ni. |
14179 | PSA 18:49 | wanda yakan cece ni daga abokan gābana. Ana girmama ka bisa abokan gābana; daga masu tā-da-na-zaune-tsaye ka kuɓutar da ni. |
16556 | PRO 3:31 | Kada ka ji kishin mai tā-da-na-zaune-tsaye ko ka yi sha’awar aikata ayyukansu. |
16624 | PRO 6:14 | wanda yake ƙulla mugunta da ruɗu a cikin zuciyarsa, kullum yana tā-da-na-zaune-tsaye |
16629 | PRO 6:19 | mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi, da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa. |
16939 | PRO 16:29 | Mutum mai tā-da-na-zaune-tsaye yakan ruɗi maƙwabcinsa ya kai shi a hanyar da ba ta da kyau. |
17151 | PRO 24:2 | gama leɓunansu suna maganar tā-da-na-zaune-tsaye ne. |
27306 | ACT 9:21 | Dukan waɗanda suka ji shi suka yi mamaki suka ce, “Ba shi ne mutumin da ya tā-da-na-zaune-tsaye a kan masu kira bisa ga wannan sunan a Urushalima ba? Ba ya zo nan ne don yă kai su a matsayin ’yan kurkuku ga manyan firistoci ba?” |
27842 | ACT 24:5 | “Mun tarar da wannan mutum fitinanne ne, yana tā-da-na-zaune-tsaye a tsakanin Yahudawa ko’ina a duniya. Shi shugaban ɗarikar Nazarawa |