Wildebeest analysis examples for:   hau-hausa   Word.’    February 11, 2023 at 18:42    Script wb_pprint_html.py   by Ulf Hermjakob

59  GEN 3:3  amma Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga ’ya’yan itacen da yake tsakiyar lambu, kada kuma ku taɓa shi, in ba haka ba kuwa za ku mutu.’
311  GEN 12:12  Sa’ad da Masarawa suka ganki, za su ce, ‘Wannan matarsa ce.’ Za su kuwa kashe ni, su bar ki da rai.
360  GEN 14:23  cewa ba zan karɓi kome da yake naka ba, ko zare ko maɗaurin takalma, don kada ka ce, ‘Na azurta Abram.’
507  GEN 20:11  Ibrahim ya ce, “Na ce a raina, ‘Tabbatacce babu tsoron Allah a wannan wuri, za su kuwa kashe ni saboda matata.’
630  GEN 24:38  amma ka tafi wajen gidan mahaifina da kuma dangina, ka ɗauko wa ɗana mata.’
633  GEN 24:41  Ta haka za ka kuɓuta daga rantsuwata sa’ad da ka tafi wurin dangina, ko ma sun ƙi su ba ka ita, za ka kuɓuta daga rantsuwata.’
636  GEN 24:44  in ta ce, “Ka sha, zan kuma ba wa raƙumanka ma,” bari tă zama wadda Ubangiji ya zaɓar wa ɗan maigidana.’
637  GEN 24:45  “Kafin in gama addu’ar, a zuciyata, sai ga Rebeka ta fito da tulunta a kafaɗarta. Ta gangara zuwa rijiyar ta ɗebo ruwa, na kuma ce mata, ‘Ina roƙonki ki ba ni ɗan ruwa daga tulunki.’
638  GEN 24:46  “Ta yi sauri ta saukar da tulun daga kafaɗarta ta ce, ‘Sha, zan kuma ba wa raƙumanka su ma.’ Sai na sha, ta kuma shayar da raƙumana su ma.
639  GEN 24:47  “Na tambaye ta, ‘Ke ’yar wane ne?’ “Ta ce, ‘’Yar Betuwel ɗan Nahor, wanda Milka ta haifa masa.’ “Sai na sa mata zobe a hancinta, woroworo kuma a hannuwata,
721  GEN 26:28  Suka amsa, “Mun ga a zahiri cewa Ubangiji yana tare da kai; saboda haka muka ce, ‘Dole rantsuwa ta kasance tsakaninmu da kai.’ Bari mu yi yarjejjeniya da kai
735  GEN 27:7  ‘Kawo mini nama ka shirya mini abinci mai daɗi don in ci, in sa maka albarka a gaban Ubangiji kafin in mutu.’
885  GEN 31:11  Sai mala’ikan Allah ya ce mini a mafarkin, ‘Yaƙub.’ Sai na amsa na ce, ‘Ga ni.’
887  GEN 31:13  Ni ne Allah na Betel, inda ka zuba wa al’amudi mai, da kuma inda ka yi mini alkawari. Yanzu ka bar wannan ƙasa nan take, ka koma ƙasarka ta ainihi.’
903  GEN 31:29  Ina da iko in cuce ka; amma jiya da dare Allahn mahaifinka ya faɗa mini, ‘Ka yi hankali kada ka faɗa wa Yaƙub wani abu ko mai kyau ko marar kyau.’
934  GEN 32:6  Ina da shanu da jakuna, tumaki da awaki, bayi maza da mata. Yanzu ina aika da wannan saƙo zuwa ga ranka yă daɗe, don in sami tagomashi a idanunka.’
938  GEN 32:10  Sa’an nan Yaƙub ya yi addu’a, “Ya Allah na mahaifina Ibrahim, Allah na mahaifina Ishaku. Ya Ubangiji kai da ka ce mini, ‘Koma ƙasarka zuwa wurin danginka, zan kuma sa ka yi albarka.’
941  GEN 32:13  Amma ka riga ka faɗa, ‘Tabbatacce zan sa ka yi albarka. Zan kuma sa zuriyarka su zama kamar yashin teku da ba a iya ƙirgawa.’
947  GEN 32:19  Sai ku ce, ‘Na bawanka Yaƙub ne. Kyauta ce wa maigidana Isuwa, yana kuma tafe a bayanmu.’
949  GEN 32:21  Ku kuma tabbata kun ce, ‘Bawanka Yaƙub yana tafe a bayanmu.’” Gama Yaƙub ya yi tunani cewa, “Zan kwantar da ran Isuwa da waɗannan kyautai, kafin mu sadu fuska da fuska, wataƙila yă karɓe shi.”
1101  GEN 37:17  Mutumin ya amsa, “Sun yi gaba daga nan. Na ji su suna cewa, ‘Bari mu je Dotan.’” Saboda haka Yusuf ya bi bayan ’yan’uwansa, ya kuwa same su kusa da Dotan.
1142  GEN 38:22  Saboda haka sai ya koma zuwa wurin Yahuda ya ce, “Ban same ta ba. Ban da haka ma, mutanen da suke zama a can, sun ce, ‘Ba a taɓa kasance da wata karuwar haikali a nan ba.’
1188  GEN 40:15  Gama da ƙarfi ne aka ɗauke ni daga ƙasar Ibraniyawa, ko a nan ma ban yi wani abin da ya cancanci a sa ni cikin kurkuku ba.’
1192  GEN 40:19  Cikin kwana uku, Fir’auna zai fid da kai, yă rataye ka a kan itace. Tsuntsaye kuwa za su ci naman jikinka.’
1287  GEN 42:34  Amma ku kawo mini ƙaramin ɗan’uwanku domin in san cewa ku ba ’yan leƙen asiri ba ne, amma mutane ne masu gaskiya. Sa’an nan zan mayar muku da ɗan’uwanku, ku kuma iya yin sana’a a ƙasar.’
1294  GEN 43:3  Amma Yahuda ya ce masa, “Mutumin ya gargaɗe mu sosai cewa, ‘Ba za ku sāke ganin fuskata ba sai in ɗan’uwanku yana tare da ku.’
1296  GEN 43:5  Amma in ba za ka aika da shi ba, ba za mu gangara ba, gama mutumin ya ce mana, ‘Ba za ku sāke ganin fuskata ba sai ko in ɗan’uwanku yana tare da ku.’
1330  GEN 44:5  Ba da wannan kwaf ne maigidana yake sha daga ciki yana kuma yin amfani da shi don duba? Wannan mugun abu ne da kuka yi.’
1345  GEN 44:20  Muka kuwa amsa, ‘Muna da mahaifi tsoho, akwai kuma ɗa matashi, wanda aka haifa masa cikin tsufarsa. Ɗan’uwansa ya rasu, shi ne kuwa ɗa kaɗai na mahaifiyarsa da ya rage, mahaifinsa kuwa yana ƙaunarsa.’
1346  GEN 44:21  “Sai ka ce wa bayinka, ‘Ku kawo mini shi don in gan shi da kaina.’
1347  GEN 44:22  Muka kuwa ce wa ranka yă daɗe, ‘Saurayin ba zai iya barin mahaifinsa ba, gama in ya bar shi, mahaifinsa zai mutu.’
1348  GEN 44:23  Amma ka faɗa wa bayinka, ‘Sai kun kawo ƙaramin ɗan’uwanku tare da ku, in ba haka ba, ba za ku sāke ganin fuskata ba.’
1350  GEN 44:25  “Sai mahaifinmu ya ce, ‘Ku koma ku sayo ƙarin abinci.’
1351  GEN 44:26  Amma muka ce, ‘Ba za mu iya gangarawa ba, sai in ƙaramin ɗan’uwanmu yana tare da mu. Ba za mu iya ganin fuskar mutumin ba, sai ƙaramin ɗan’uwanmu yana tare mu.’
1354  GEN 44:29  In kun ɗauki wannan daga wurina shi ma wani abu ya same shi, za ku kawo furfura kaina zuwa kabari cikin baƙin ciki.’
1370  GEN 45:11  Zan tanada maka a nan, domin akwai saura shekaru biyar na yunwa masu zuwa. In ba haka ba, kai da gidanka da dukan mallakarka za ku zama gajiyayyu.’
1377  GEN 45:18  Ku kawo mahaifinku da iyalanku zuwa wurina. Zan ba ku mafi kyau na ƙasar Masar, za ku kuwa ci moriyar ƙasar.’
1379  GEN 45:20  Kada ku damu da mallakarku, gama mafi kyau na Masar za su zama naku.’
1419  GEN 46:32  Mutanen fa, makiyaya ne; suna kiwon dabbobi, sun kuma zo tare da garkunansu da shanunsa da kuma kome da suka mallaka.’
1421  GEN 46:34  Ku amsa, ‘Bayinka suna kiwon dabbobi ne, tun muna samari har zuwa yanzu, kamar yadda kakanninmu suka yi.’ Ta haka za a bar ku ku zauna a yankin Goshen, gama Masarawa suna ƙyamar makiyaya.”
1456  GEN 48:4  ya kuma ce mini, ‘Zan sa ka yi ta haihuwa ka kuma riɓaɓɓanya, za ka ƙaru a yawa. Zan mai da kai al’ummar mutane, zan kuma ba ka wannan ƙasa tă zama madawwamiyar mallaka ga zuriyarka a bayanka.’
1472  GEN 48:20  Ya albarkace su a wannan rana ya ce, “A cikin sunanku Isra’ila zai sa wannan albarka ‘Bari Allah yă sa ku zama kamar Efraim da Manasse.’” Saboda haka ya sa Efraim gaban Manasse.
1512  GEN 50:5  ‘Mahaifina ya sa na yi rantsuwa, ya kuma ce, “Ina gab da mutuwa, ka binne ni a kabarin da na haƙa wa kaina a ƙasar Kan’ana.” Yanzu fa bari in haura in binne mahaifina, sa’an nan in dawo.’
1524  GEN 50:17  Ga abin da za ku ce wa Yusuf, ‘Na roƙe ka, ka gafarta wa ’yan’uwanka zunubai da laifofin da suka aikata na abubuwa marasa kyau da suka yi maka.’ Yanzu muna roƙonka ka gafarta zunuban bayin Allah na mahaifinka.” Sa’ad da saƙonsu ya zo masa, sai Yusuf ya yi kuka.
1594  EXO 3:14  Allah ya ce wa Musa, “NI NE wanda NINE. Abin da za ka faɗa wa Isra’ilawa ke nan cewa, ‘NI NE, ya aiko ni wurinku.’
1595  EXO 3:15  Allah ya kuma ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Ubangiji, Allah na kakanninka, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub, ya aiko ni wurinku.’ Wannan shi ne sunana har abada, sunan da za a tuna da ni daga tsara zuwa tsara ke nan.
1597  EXO 3:17  Na kuma yi alkawari, zan fitar da ku daga azabarku a Masar zuwa ƙasar Kan’aniyawa, Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa, ƙasa mai zub da madara da zuma.’
1598  EXO 3:18  “Dattawan Isra’ila za su saurare ka. Sa’an nan da kai da dattawan Isra’ila, za ku tafi wurin sarkin Masar, ku ce masa, ‘Ubangiji, Allah na Ibraniyawa, ya sadu da mu. Bari mu yi tafiyar kwana uku zuwa cikin hamada domin mu yi hadaya wa Ubangiji Allahnmu.’
1625  EXO 4:23  na gaya maka, “Ka bar ɗana yă tafi domin yă yi mini sujada.” Amma ka ƙi ka bari yă tafi, saboda haka zan kashe ɗan farinka.’
1634  EXO 5:1  Daga bisani sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna suka ce, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Bari mutanena su tafi domin su yi mini biki a hamada.’
1641  EXO 5:8  Ku kuma bukace su su yi tubula daidai yawan tubalin da suka saba yi, kada ku rage. Ragwaye ne, shi ya sa suke kuka cewa, ‘Bari mu tafi mu yi hadaya ga Allahnmu.’
1644  EXO 5:11  Ku tafi ku nemo wa kanku tattaka duk inda za ku samu, amma ba za a rage aikinku ba ko kaɗan.’
1650  EXO 5:17  Fir’auna ya ce, “Ku ragwaye ne! Shi ya sa kuke cewa, ‘Bari mu tafi mu yi hadaya wa Ubangiji.’
1664  EXO 6:8  Zan kuwa kawo ku a ƙasar da na rantse da hannun da na ɗaga sama, cewa zan ba wa Ibrahim, wa Ishaku, da kuma wa Yaƙub. Zan ba da ita gare ku gādo. Ni ne Ubangiji.’
1704  EXO 7:18  Kifi a ciki Nilu za su mutu, ruwan kuma zai yi ɗoyi; Masarawa ba za su iya shan ruwansa ba.’
1705  EXO 7:19  Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ce wa Haruna, ‘Ka ɗauki sandanka, ka miƙa hannunka kan ruwan Masar, kan kogunansu da rafuffukansu da kududdufansu da kuma dukan tafkunansu, za su zama jini.’ Jini zai kasance ko’ina a Masar, har ma a cikin abubuwan ajiyar ruwansu da aka yi da itace da kuma dutse.”
1715  EXO 7:29  Kwaɗin nan za su yi ta tsalle a kanka, da kan mutanenka, da kuma kan dukan bayinka.’
1716  EXO 8:1  Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ce wa Haruna, ‘Ka miƙa hannunka da sandanka bisa koguna da rafuffuka da kuma kududdufai, ka sa kwaɗi su fito su mamaye ƙasar Masar.’
1734  EXO 8:19  Zan sa iyaka tsakanin jama’ata da jama’arka. Gobe ne wannan mu’ujiza za tă auku.’
1747  EXO 9:4  Amma Ubangiji zai raba tsakanin dabbobin Isra’ila da na Masar, saboda kada wata dabbar Isra’ilawa ta mutu.’
1762  EXO 9:19  Yanzu, ka ba da umarni a dawo da shanunku da kuma kome da kuke da shi wanda yake a gona zuwa gida, gama ƙanƙarar za tă kashe kowane mutum ko dabba wadda take a gona wadda ba a kawo cikin gida ba, sa’ad da ta fāɗo.’
1784  EXO 10:6  Za su cika gidajenka, da na fadawanka, da na dukan Masarawa, abin da iyayenka da kakanninka ba su taɓa gani ba, tun daga ranar da suka sami kansu a duniya, har yă zuwa yau.’” Sa’an nan Musa ya juya, ya rabu da Fir’auna.
1814  EXO 11:7  Amma a cikin Isra’ilawa, ba karen da zai yi haushi wa mutum ko dabba.’ Ta haka za ku sani Ubangiji zai bambanta tsakanin Masar da Isra’ila.
1844  EXO 12:27  Sai ku faɗa musu, ‘Hadaya ce ta Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji, domin ya tsallake gidajen Isra’ilawa a Masar, lokacin da ya kashe Masarawa, amma bai taɓa gidajenmu ba.’” Sai mutane suka rusuna, suka yi sujada.
1876  EXO 13:8  A ranan nan kowa zai faɗa wa ɗanka, ‘Ina yin haka saboda abin da Ubangiji ya yi mini, sa’ad da na fita daga Masar.’
1883  EXO 13:15  Sa’ad da Fir’auna ya taurare zuciyarsa, bai yarda ya sallame mu ba, sai Ubangiji ya kashe dukan ’ya’yan farin ƙasar Masar, na mutum da na dabba, gaba ɗaya. Domin haka nake yin hadaya ga Ubangiji da ’ya’yan fari, maza, da suka fara buɗe mahaifa, amma nakan fanshi dukan ’ya’yan farina maza.’
1893  EXO 14:3  Fir’auna zai yi tsammani, ‘Aha, Isra’ilawa sun rikice cikin ƙasar, hamada kuwa ta yimƙe su.’
1930  EXO 15:9  Magabci ya yi fahariya, cewa ‘Zan fafare su, in ci musu. Zan raba ganima; abin da na so ya samu. Zan ja takobina hannuna kuwa zai hallaka su.’
1957  EXO 16:9  Sai Musa ya ce wa Haruna, “Ka faɗa wa dukan taron Isra’ila, ‘Ku zo gaban Ubangiji, gama ya ji gunaguninku.’
1960  EXO 16:12  “Na ji gunagunin Isra’ilawa. Ka faɗa musu, ‘A tsakanin fāɗuwar rana da almuru, za ku ci nama, da safe kuma za ku ƙoshi da burodi. Sa’an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku.’
1964  EXO 16:16  Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta, ‘Kowane mutum zai tattara bisa ga bukatarsa. Ku tara rabin gallon don mutum guda da yake cikin tentinku.’
1971  EXO 16:23  Shi kuma ya ce musu, “Wannan shi ne umarnin Ubangiji, ‘Gobe za tă zama ranar hutu, Asabbaci mai tsarki ga Ubangiji. Domin haka sai ku toya abin da kuke so ku toya, ku kuma dafa abin da kuke so ku dafa. Abin da ya rage ku ajiye har safe.’
1980  EXO 16:32  Musa ya ce, “Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta, ‘Ku auna mudu guda na Manna, a adana ta dukan zamananku, domin kowane zamani yă ga irin abincin da na ba ku ku ci a hamada, yayinda na fitar da ku daga Masar.’
2033  EXO 19:6  za ku zama firistoci masu tsarki da kuma al’umma keɓaɓɓiya a gare ni.’ Waɗannan su ne kalmomin da za ka faɗa wa Isra’ilawa.”
2040  EXO 19:13  Za a jajjefe shi da duwatsu, ko a harbe shi da kibiyoyi, ba hannun da zai taɓa shi. Mutum ko dabbar da ya taɓa, ba za a bar shi da rai ba.’ Lokacin da aka ji muryar ƙaho ne kawai za su iya taru a gindin dutsen.”
2050  EXO 19:23  Musa ya ce wa Ubangiji, “Mutanen ba za su hau Dutsen Sinai ba, gama kai da kanka ka gargaɗe mu, ‘Ku sa iyaka kewaye da dutsen ku kuma tsarkake shi.’
2078  EXO 20:26  Kada ku gina wa bagadena matakala, domin kada yayinda wani yana hawa, mutane su ga tsiraicinsa.’
2416  EXO 30:33  Duk wanda ya yi irin wannan mai, duk wanda kuma ya shafa shi a kan wani wanda yake ba firist ba, za a ware shi daga mutanensa.’
2438  EXO 31:17  Zai zama alama tsakanina da Isra’ilawa har abada, gama cikin kwana shida Ubangiji ya yi sama da ƙasa, a rana ta bakwai kuma ya daina aiki, ya kuma huta.’
2452  EXO 32:13  Ka tuna da bayinka Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, waɗanda ka rantse da kanka cewa, ‘Zan mai da zuriyarka kamar taurarin sama kuma zan ba wa zuriyarka wannan ƙasa wadda na yi musu alkawari, za tă kuma zama abin gādonsu har abada.’
2462  EXO 32:23  Sun ce mini, ‘Ka yi mana alloli waɗanda za su yi mana jagora, game da wannan Musa dai, wanda ya fito da mu daga Masar, ba mu san abin da ya faru da shi ba.’
2466  EXO 32:27  Sa’an nan ya ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Kowane mutum yă rataya takobinsa, yă kai yă kawo daga wannan gefe zuwa wancan cikin sansani, kowa yă kashe ɗan’uwansa, da abokinsa, da kuma maƙwabcinsa.’
2475  EXO 33:1  Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka bar wannan wuri, kai da mutanen da ka fito da su daga Masar, ka haura zuwa ƙasar da na alkawarta da rantsuwa wa Ibrahim, Ishaku da Yaƙub cewa, ‘Zan ba zuriyarka.’
2479  EXO 33:5  Gama Ubangiji ya riga ya ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Ku mutane ne masu taurinkai. In na yi tafiya da ku ko na ɗan lokaci, mai yiwuwa in hallaka ku. Yanzu sai ku tuɓe kayan adonku, zan kuwa yanke shawara a kan abin da zan yi da ku.’
2486  EXO 33:12  Musa ya ce wa Ubangiji, “Kana ta faɗa mini cewa, ‘Ka jagoranci mutane nan,’ amma ba ka faɗa mini wanda zai tafi tare da ni ba. Ga shi ka ƙara ce mini, ‘Na san ka, na san sunanka, ka kuma sami tagomashi a wurina.’
2796  LEV 3:17  “ ‘Wannan dawwammamiyar farilla ce ga tsararraki masu zuwa, a inda za ku zauna. Ba za ku ci wani kitse ko wani jini ba.’
2844  LEV 5:13  Ta haka firist zai yi kafara dominsa saboda dukan waɗannan zunuban da ya yi, za a kuwa gafarta masa. Sauran hadayar za tă zama ta firist, kamar yadda yake bisa ga hadaya ta gari.’
2868  LEV 6:11  Kowane ɗa namiji cikin zuriyar Haruna zai iya cinsa. Wannan rabonsa ne na kullum na hadayar da aka yi ga Ubangiji da wuta. Wannan madawwamiyar doka ce cikin zamananku duka. Duk abin da ya taɓa hadayun zai tsarkaka.’
2901  LEV 7:21  Idan wani mutum ya taɓa abu marar tsarki, ko mutum ne, ko dabba ce, ko wani abu na banƙyama, ya kuma ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji, za a fid da mutumin daga cikin mutanensa.’
2907  LEV 7:27  Duk wanda ya ci jini, za a fid da mutumin daga mutanensa.’
2949  LEV 8:31  Sai Musa ya ce wa Haruna da ’ya’yansa maza, “Ku dafa naman a ƙofar Tentin Sujada, ku kuma ci shi a can tare da burodi daga kwandon naɗi, yadda na umarta, cewa, ‘Haruna da ’ya’yansa maza za su ci shi.’
2958  LEV 9:4  da bijimi da rago don hadayun salama, a yi hadaya da su ga Ubangiji, da hadaya ta gari da aka kwaɓa da mai, gama yau Ubangiji zai bayyana a gare ku.’
2981  LEV 10:3  Sai Musa ya ce Haruna, “Ga abin da Ubangiji yake nufi sa’ad da ya ce, “ ‘A cikin waɗanda suka kusace ni za a tabbata ni mai tsarki ne; a fuskar dukan mutane za a kuwa girmama ni.’” Haruna ya yi shiru.
3045  LEV 11:47  Dole ku bambanta tsakanin haramtacce da halaltacce, tsakanin halittu masu ran da za a iya ci da waɗanda ba za a iya ci ba.’
3053  LEV 12:8  In ba za tă iya kawo ɗan rago ba, sai ta kawo kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu, ɗaya domin hadaya ta ƙonawa ɗayan kuma domin hadaya don zunubi. Ta haka firist zai yi kafara dominta, za tă kuwa zama tsabtacciya.’
3147  LEV 14:35  dole maigidan ya tafi ya faɗa wa firist ya ce, ‘Na ga wani abu da ya yi kamar cutar fatar jikin da take a riga a cikin gidana.’
3200  LEV 15:31  “ ‘Ta haka za ka tsarkake Isra’ilawa daga rashin tsarkinsu, domin kada su mutu saboda rashin tsarkinsu ta wurin ƙazantar da wurin zamana wanda yake tsakiyarsu.’
3243  LEV 17:7  Kada kuma su ƙara yin hadayunsu ga gumaka masu siffar bunsurai waɗanda suka bauta wa. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a gare su wa tsararraki masu zuwa.’
3252  LEV 17:16  Amma in bai wanke rigunansa ya kuma yi wanka ba, alhaki zai kasance a kansa.’
3282  LEV 18:30  Ku kiyaye umarnaina kuma kada yi ku wata al’ada mai banƙyamar da aka yi kafin ku zo kuma kada ku ƙazantar da kanku da su. Ni ne Ubangiji Allahnku.’