870 | GEN 30:39 | sai su yi barbara a gaban rassan. Sai kuwa su haifi ƙanana masu zāne dabbare-dabbare, ko babare-babare ko masu zāne-zāne. |
882 | GEN 31:8 | In ya ce, ‘Dabbare-dabbare ne za su zama ladanka,’ sai dukan garkunan su haifi dabbare-dabbare, in kuma ya ce, ‘Masu zāne-zāne ne za su zama ladanka,’ sai dukan garkunan su haifi ƙananan masu zāne-zāne. |
1030 | GEN 35:18 | Yayinda take jan numfashinta na ƙarshe, sai ta ba wa ɗanta suna Ben-Oni. Amma mahaifinsa ya kira shi Benyamin. |
1080 | GEN 36:39 | Sa’ad da Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya rasu, Hadad ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Fau, kuma sunan matarsa Mehetabel ce ’yar Matired, jikanyar Me-Zahab. |
1518 | GEN 50:11 | Sa’ad da Kan’aniyawa waɗanda suke zama a can suka ga makokin a masussukan Atad, sai suka ce, “Masarawa suna bikin makoki na musamman.” Shi ya sa ake kira wannan wurin da yake kusa da Urdun, Abel-Mizrayim. |
2021 | EXO 18:21 | Amma ka zaɓi mutane masu iyawa daga dukan mutane, maza masu tsoron Allah, amintattu, masu ƙin rashawa, ka sanya su shugabanni na dubbai, ɗari-ɗari, hamsin-hamsin da goma-goma. |
2025 | EXO 18:25 | Ya zaɓi mutane masu iyawa daga cikin dukan Isra’ila, ya naɗa su shugabannin mutane, shugabanni a kan dubbai, ɗari-ɗari, hamsin-hamsin da goma-goma. |
2375 | EXO 29:38 | “Ga abin da za ka miƙa a bisa bagaden kowace rana. ’Yan raguna biyu masu shekara ɗaya-ɗaya. |
2554 | EXO 35:22 | Duk waɗanda suke da niyya, maza da mata, gaba ɗaya, suka kawo kayan ado na zinariya na kowane iri. ’Yan kunne, da ƙawane, da mundaye, da kayayyakin zinariya iri-iri. Dukansu suka miƙa zinariyarsu a matsayin hadaya ga Ubangiji. |
2567 | EXO 35:35 | Ya cika su da fasaha don yin kowane irin aikin sana’a, zāne-zāne, ɗinke-ɗinke shuɗi, shunayya da jan zare, da lallausan lilin, da kuma masu yin saƙa, sun gwaninta ƙwarai cikin kowane irin aikin hannu da kuma zāne-zāne. |
2752 | LEV 1:6 | Zai feɗe hadaya ta ƙonawar, yă yayyanka shi gunduwa-gunduwa. |
3790 | NUM 4:46 | Saboda haka, Musa, Haruna da shugabannin Isra’ila, suka ƙidaya dukan Lawiyawa kabila-kabila da kuma iyali-iyali. |
3939 | NUM 7:88 | Jimillar dabbobi don hadaya ta salama, ta kai shanu ashirin huɗu, raguna sittin, bunsurai sittin da kuma ’yan raguna sittin, dukansu bana ɗaya-ɗaya. Waɗannan su ne hadayu saboda keɓewar bagade, bayan an shafe shi. |
4811 | NUM 33:49 | A can filayen Mowab, suka yi sansani kusa da Urdun ɗaura da Bet-Yeshimot har zuwa Abel-Shittim. |
4827 | NUM 34:9 | tă ci gaba zuwa Zifron, sa’an nan tă ƙarasa a Hazar-Enan. Wannan ce za tă zama iyakarku a arewa. |
4909 | DEU 1:15 | Saboda haka na ɗauko shugabannin kabilanku masu hikima, waɗanda suka saba da ma’amala da jama’a, na sa su shugabanni a gabanku, waɗansu suka zama shugabanni a kan dubu-dubu, waɗansu a kan ɗari-ɗari, waɗansu a kan hamsin-hamsin, waɗansu kuma a kan goma-goma. Na sa su zama shugabanni a kabilanku. |
5006 | DEU 3:29 | Sai muka zauna a kwari kusa da Bet-Feyor. |
5656 | DEU 28:43 | Baƙin da suke tare da ku, za su yi ta ƙaruwa, ku kuwa za ku yi ta komawa baya-baya. |
5992 | JOS 7:14 | “ ‘Da safe ku zo kabila-kabila. Kabilar da Ubangiji ya ware, za tă zo gaba gida-gida; gidan da Ubangiji ya ware, za su zo gaba iyali-iyali. Iyalin kuma da Ubangiji ya ware, za su zo gaba mutum bayan mutum. |
6132 | JOS 11:23 | Yoshuwa kuwa ya ƙwace dukan ƙasar yadda Ubangiji ya umarci Musa, ya ba da ita ta zama ƙasar gādo ga Isra’ilawa, kabila-kabila. Ta haka ƙasar ta huta daga yaƙi. |
6139 | JOS 12:7 | Waɗannan su ne sarakuna da kuma ƙasashen da Yoshuwa da Isra’ilawa suka ci da yaƙi a yammancin Urdun, daga Ba’al-Gad a Kwarin Lebanon zuwa Dutsen Halak wanda ya miƙe zuwa Seyir. Yoshuwa ya raba ƙasarsu ta zama gādo ga Isra’ilawa bisa ga yadda aka raba su kabila-kabila. |
6305 | JOS 18:10 | Sai Yoshuwa ya yi musu ƙuri’a a gaban Ubangiji, a nan ne ya raba wa Isra’ilawa ƙasar bisa ga yadda aka raba su kabila-kabila. |
6307 | JOS 18:12 | Daga gefen arewa, iyakarsu ta kama ne daga Urdun, ta wuce arewa a gangaren Yeriko, ta nufi yamma cikin ƙasar kan tudu, ta fito a jejin Bet-Awen. |
6308 | JOS 18:13 | Daga can ta ƙetare zuwa gangaren Luz a kudu (wato, Betel), ta wuce zuwa Atarot Adda a tudun arewa na kwarin Bet-Horon. |
6344 | JOS 19:21 | Remet, En Gannim, En Hadda da Bet-Fazez. |
6361 | JOS 19:38 | Yiron, Migdal El, Horem, Bet-Anat da Bet-Shemesh. Garuruwa goma sha tara ke nan da ƙauyukansu. |
6631 | JDG 5:6 | “A zamanin Shamgar ɗan Anat, a zamanin Yayel, an yashe dukan hanyoyi; matafiye suka bi hanyoyin da suka yi kona-kona. |
6720 | JDG 7:24 | Gideyon ya aiki manzanni zuwa dukan ƙasar tudu ta Efraim cewa, “Ku gangaro ku yaƙi Midiyawa ku ƙwace ruwan Urdun gaba da su har zuwa Bet-Bara.” Saboda haka aka kira dukan mutanen Efraim suka ƙwace ruwan Urdun har zuwa Bet-Bara. |
6802 | JDG 9:46 | Da jin haka, sai ’yan ƙasa a hasumiyar Shekem suka shiga wurin mafaka a hankalin El-Berit. |
6864 | JDG 11:33 | Ya hallaka birane ashirin tun daga Arower zuwa yankin Minnit, har zuwa Abel-Keramim. Haka Isra’ila ta cinye Ammonawa ƙaf. |
6930 | JDG 14:19 | Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko masa da iko. Sai ya fita ya gangara zuwa Ashkelon, ya kashe mutanensu talatin, ya kwashe kayansu ya kuma ba da rigunarsu ga waɗanda suka bayyana kacici-kacicin. Cike da fushi, ya haura zuwa gidan mahaifinsa. |
7023 | JDG 18:28 | Ba wanda zai cece su domin suna nesa da Bet-Sidon kuma ba sa hulɗa da kowa. Birnin yana a kwari kusa da Bet-Rekob. Mutanen Dan suka sāke gina birnin suka zauna a can. |
7345 | 1SA 6:12 | Sai shanun suka miƙe zuwa Bet-Shemesh. Suka bi hanya daidai, ba su juya dama ko hagu ba. Shugabannin Filistiyawa suka bi har zuwa iyakar ƙasar Bet-Shemesh. |
7351 | 1SA 6:18 | Filistiyawa kuma suka aika da siffofin ɓeraye biyar na zinariya. Yawan ɓerayen sun yi daidai da yawan garuruwan sarakunan nan biyar na Filistiyawa. Garuruwan sun ƙunshi waɗanda aka gina katangar birni kewaye da su, da kuma ƙauyukansu. Babban dutsen da suka ajiye akwatin alkawarin Ubangiji, ya zama shaida har wa yau a filin Yoshuwa a Bet-Shemesh. |
7365 | 1SA 7:11 | Isra’ilawa suka fito a guje daga Mizfa suka fafari Filistiyawa suka yi ta karkashe su a hanya har kwarin Bet-Kar. |
7383 | 1SA 8:12 | Zai sa waɗansu su zama shugabannin mutum dubu-dubu da kuma na hamsin-hamsin. Waɗansu za su yi masa noma da girbi. Waɗansu za su ƙera masa makaman yaƙi da kayayyaki don keken yaƙinsa. |
7384 | 1SA 8:13 | Zai sa ’ya’yanku mata yin aikin turare da dafe-dafe da kuma toye-toye. |
7391 | 1SA 8:20 | Ta haka za mu zama kamar sauran ƙasashe, mu kasance da sarkin da zai bi da mu, yă tafi tare da mu zuwa yaƙe-yaƙe. |
7533 | 1SA 14:23 | Haka Ubangiji ya kuɓutar da Isra’ila a wannan rana. Yaƙin kuwa ya ci gaba har gaba da Bet-Awen. |
7559 | 1SA 14:49 | ’Ya’yan Shawulu maza su ne, Yonatan, Ishbi, da Malki-Shuwa. Sunan babban ’yarsa ita ce Merab, ƙaramar kuma Mikal. |
7694 | 1SA 18:16 | Amma dukan Isra’ila da Yahuda suka ƙaunaci Dawuda gama yana bin da su a yaƙe-yaƙensu. |
7972 | 1SA 29:2 | Sa’ad da sarakuna Filistiyawa suke wucewa da rundunarsu na mutum ɗari-ɗari da na dubu-dubu. Dawuda da mutanensa suna biye a baya tare da Akish. |
8014 | 1SA 31:2 | Filistiyawa suka abka wa Shawulu da ’ya’yansa maza, suka kashe ’ya’yan Shawulu. Yonatan da Abinadab da Malki-Shuwa. |
8022 | 1SA 31:10 | Suka ajiye makaman Shawulu a cikin haikalin gumakan Ashtarot. Suka kafa gawarsa a kan katanga Bet-Shan. |
8137 | 2SA 5:2 | A dā da Shawulu yake sarauta a bisanmu, kai ne kake bi Isra’ilawa zuwa yaƙe-yaƙensu. Ubangiji kuwa ya ce maka, ‘Za ka zama makiyayi mutanena Isra’ila, za ka kuma zama sarkinsu.’ ” |
8482 | 2SA 18:1 | Dawuda ya tattara mutanen da suke tare da shi, ya naɗa musu komandodi na dubu-dubu, da na ɗari-ɗari. |
8485 | 2SA 18:4 | Sarki ya ce, “Zan yi duk abin da ya fi muku kyau.” Saboda haka sarki ya tsaya kusa da bakin ƙofa yayinda dukan mutane suke fitowa a ƙungiyar ɗari-ɗari da ta dubu-dubu. |
8506 | 2SA 18:25 | Mai tsaro ya tā da murya ya faɗa wa sarki. Sarki ya ce, “In shi kaɗai ne, ya kawo labari mai kyau ke nan.” Mutumin ya matso kusa-kusa. |
8892 | 1KI 5:25 | Solomon kuma ya ba wa Hiram mudu gari dubu ashirin na alkama a matsayin abinci domin gidansa, ya ƙara da garwa dubu ashirin na tataccen man zaitun. Solomon ya ci gaba da yin haka ga Hiram, shekara-shekara. |
8968 | 1KI 7:31 | A dakalin daga ciki, akwai bakin da yake da’ira, mai zurfi kamun guda. Bakin da’irar ne, yana da zāne-zānensa da ya kai kamu ɗaya da rabi. Kusa da bakin akwai zāne-zāne. Sassan dakalin murabba’i ne, ba da’ira ba ne. |
9420 | 1KI 20:9 | Saboda haka ya ba wa ’yan aikan Ben-Hadad amsa, ya ce, “Ku faɗa wa ranka yă daɗe, sarki, ‘Bawanka zai yi dukan abin da ka bukaci da farko, amma wannan na ƙarshe ba zan iya yin ba.’ ” Suka tafi suka kai amsar wa Ben-Hadad. |
9911 | 2KI 14:11 | Amma Amaziya bai saurara ba, saboda haka Yehowash sarkin Isra’ila ya kai masa hari. Shi da Amaziya sarkin Yahuda suka fuskanci juna a Bet-Shemesh. |
9913 | 2KI 14:13 | Yehowash sarkin Isra’ila ya kama Amaziya sarkin Yahuda, ɗan Yowash, ɗan Ahaziya, a Bet-Shemesh. Sa’an nan Yehowash ya tafi Urushalima ya rushe katangar Urushalima daga Ƙofar Efraim har zuwa Ƙofar Kusurwa, ratarta ta kai wajen ƙafa ɗari shida. |
9925 | 2KI 14:25 | Shi ne ya maido da iyakokin Isra’ila daga Lebo Hamat zuwa Tekun Araba, bisa ga maganar Ubangiji, Allah na Isra’ila, da ya yi ta bakin bawansa Yunana ɗan Amittai, annabi daga Gat-Hefer. |
10306 | 1CH 1:50 | Sa’ad da Ba’al-Hanan ya mutu, Hadad ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Fau, sunan matarsa kuwa Mehetabel ’yar Matired, ’yar Me-Zahab. |
10355 | 1CH 2:45 | Ɗan Shammai shi ne Mawon, Mawon kuma shi ne mahaifin Bet-Zur. |
10361 | 1CH 2:51 | Salma mahaifin Betlehem, da kuma Haref mahaifin Bet-Gader. |
10385 | 1CH 3:20 | Akwai kuma waɗansu biyar, Hashuba, Ohel, Berekiya, Hasadiya da Yushab-Hesed. |
10403 | 1CH 4:14 | Meyonotai shi ne mahaifin Ofra. Serahiya shi ne mahaifin Yowab, mahaifin Ge-Harashim. An kira shi haka domin mutanensa masu sana’ar hannu ne. |
10409 | 1CH 4:20 | ’Ya’yan Shimon maza su ne, Amnon, Rinna, Ben-Hanan da Tilon. Zuriyar Ishi su ne, Zohet da Ben-Zohet. |
10563 | 1CH 7:24 | ’Yarsa ita ce Sheyera, wadda ta gina Bet-Horon na kwari da na tudu da kuma Uzzen-Sheyera. Zuriyarsa ita ce, |
10665 | 1CH 10:2 | Filistiyawa suka matsa sosai suna bin Shawulu da ’ya’yansa maza, suka kuma kashe ’ya’yansa maza Yonatan, Abinadab da Malki-Shuwa. |
10679 | 1CH 11:2 | A dā, ko a lokacin da Shawulu yake sarki, ai, kai ne kake shugabantar Isra’ila a yaƙe-yaƙe. Kuma Ubangiji Allahnka ya ce maka, ‘Za ka zama makiyayin mutanena Isra’ila, za ka kuma zama mai mulkinsu.’ ” |
10766 | 1CH 13:1 | Sai Dawuda ya tattauna da kowane ɗaya daga cikin shugabanninsa, shugabannin sojoji na dubu-dubu da na ɗari-ɗari. |
10903 | 1CH 18:8 | Daga Teba da Kun, garuruwan da suke ƙarƙashin Hadadezer, Dawuda ya kwashe tagulla da yawa sosai, wanda Solomon ya yi amfani don yă yi Tekun tagulla, ginshiƙai da kuma kayayyakin tagulla dabam-dabam. |
11216 | 2CH 1:17 | Suka shigo da kekunan yaƙi daga Masar a kan shekel ɗari shida-shida na azurfa, doki kuma a kan shekel ɗari da hamsin-hamsin. Suka kuma riƙa fitar da su ƙasashen waje zuwa dukan sarakunan Hittiyawa da na Arameyawa. |
11239 | 2CH 3:5 | Ya shafe babban zauren da fir, ya kuma rufe shi da zinariya mai kyau; ya yi masa ado da zāne-zānen itatuwan dabino da kuma jerin zāne-zāne. |
11721 | 2CH 25:12 | Mayaƙan Yahuda suka kuma kama mutane dubu goma da rai, suka ɗauke su zuwa ƙwanƙolin dutsen, suka yi ta tunkuɗa su ƙasa suka yi kaca-kaca. |
11732 | 2CH 25:23 | Yehowash sarkin Isra’ila ya kama Amaziya sarkin Yahuda, ɗan Yowash, ɗan Ahaziya a Bet-Shemesh. Sa’an nan Yehowash ya kawo shi Urushalima ya farfasa katangar Urushalima daga Ƙofar Efraim har zuwa Ƙofar Kusurwa, wani sashe mai tsawon ƙafa ɗari shida. |
11865 | 2CH 31:6 | Mutanen Isra’ila da Yahuda waɗanda suke zama a garuruwan Yahuda, su ma suka kawo zakan shanu da na tumaki da kuma zakan abubuwa masu tsarki da aka keɓe ga Ubangiji Allahnsu, suka jibge su tsibi-tsibi. |
12336 | NEH 3:4 | Kusa da su kuma, Meremot ɗan Uriya, ɗan Hakkoz ne ya yi gyare-gyaren. Biye da shi kuma sai Meshullam ɗan Berekiya, ɗan Meshezabel ya yi gyare-gyare. Kusa da shi Zadok ɗan Ba’ana shi ma ya yi gyare-gyare. |
12339 | NEH 3:7 | Biye da su, mutanen Gibeyon da Mizfa Melatiya na Gibeyon da Yadon Meronot waɗanda suke ƙarƙashin ikon gwamnan Kewayen Kogin Yuferites ne suka yi gyare-gyaren. |
12349 | NEH 3:17 | Biye da shi, Lawiyawa a ƙarƙashin Rehum ɗan Bani ne suka yi gyare-gyaren. Kusa da su, Hashabiya mai mulkin rabin yankin Keyila ne ya yi gyare-gyaren don yankinsa. |
12350 | NEH 3:18 | Biye da shi, ’yan’uwansu Lawiyawa ne a ƙarƙashin Binnuyi ɗan Henadad, mai mulkin ɗayan rabin yankin Keyila suka yi gyare-gyaren. |
12361 | NEH 3:29 | Biye da su, Zadok ɗan Immer ya yi gyare-gyaren ɗaura da gidansa. Biye da shi, Shemahiya ɗan Shekaniya, mai tsaron Ƙofar Gabas ya yi gyare-gyare. |
12690 | NEH 13:15 | A waɗannan kwanaki, na ga mutane a Yahuda suna matse ruwan inabi a ranar Asabbaci suna kuma kawo hatsi suna labta su a kan jakuna, tare da ruwan inabi, ’ya’yan inabi, ɓaure da kaya iri-iri. Suna kuma kawowa dukan wannan cikin Urushalima a ranar Asabbaci. Saboda haka na gargaɗe su a kan sayar da abinci a wannan rana. |
12740 | EST 2:12 | Kafin a kai kowace yarinya wurin Sarki Zerzes, sai ta gama watanni goma sha biyu cif ana yin mata kwalliyar da aka tsara, akan ɗauki watanni shida ana shafa mata man mur, a ɗauki watanni shida kuma ana shafa mata man ƙanshi da kayan shafe-shafe. |
12758 | EST 3:7 | A shekara ta goma sha biyu ta Sarki Zerzes, a wata na farko, watan Nisan, sai suka jefa fur (wato, ƙuri’a) a gaban Haman don a zaɓi rana da watan da zai dace da ƙulle-ƙullen. Sai ƙuri’a ta fāɗa a kan wata na goma sha biyu, wato, watan Adar. |
12763 | EST 3:12 | Sa’an nan aka kira magatakardun sarki a rana ta goma sha uku na wata na fari. Suka rubuta dukan umarnin Haman a irin rubutun kowane lardi, kuma cikin harshen kowane mutane, zuwa ga shugabannin mahukuntai na sarki, da gwamnonin larduna dabam-dabam, da kuma hakiman mutane dabam-dabam. Aka rubuta waɗannan a sunan Sarki Zerzes da kansa, aka kuma hatimce da zobensa. |
12842 | EST 9:4 | Mordekai babban mutum ne a fada, sunansa ya kai ko’ina a lardunan, ikonsa ya yi ta ƙasaita gaba-gaba. |
13370 | JOB 21:11 | Suna aika ’ya’yansu kamar garke; ’ya’yansu suna guje-guje da tsalle-tsalle. |
13940 | JOB 42:14 | ’Yar farko ya kira ta Yemima, ta biyun Keziya ta ukun Keren-Haffuk. |
14330 | PSA 29:5 | Muryar Ubangiji ta kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon. Ubangiji ya kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon kucu-kucu. |
14478 | PSA 37:7 | Ka natsu a gaban Ubangiji ka kuma jira da haƙuri gare shi; kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu, sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu. |
14684 | PSA 49:5 | Zan juye kunnena ga karin magana; da garaya zan ƙarfafa kacici-kacicina. |
14817 | PSA 57:8 | Zuciyata tana nan daram, ya Allah, zuciyata tana nan daram; zan rera in kuma yi kaɗe-kaɗe. |
14921 | PSA 65:11 | Ka kwarara ta da ruwa ka kuma baje kunyoyinta; ka sa ta yi laushi da yayyafi ka kuma albarkaci tsire-tsirenta. |
17640 | SNG 2:16 | Ƙaunataccena nawa ne ni kuma tasa ce; yana kiwon garkensa a cikin furannin bi-rana. |
17657 | SNG 4:5 | Nonanki biyu sun yi kamar bareyi biyu, kamar tagwayen barewa da suke kiwo a cikin furen bi-rana. |
17686 | SNG 6:2 | Ƙaunataccena ya gangara zuwa lambunsa, zuwa inda fangulan kayan yaji suke, don yă yi kiwo a cikin lambun don kuma yă tattara furen bi-rana. |
17687 | SNG 6:3 | Ni na ƙaunataccena ce, ƙaunataccena kuma nawa ne; yana kiwo a cikin furen bi-rana. |
17793 | ISA 3:16 | Ubangiji ya ce, “Matan Sihiyona suna da girman kai, suna tafiya da wuya a miƙe, da idanu masu yaudara, suna takawa ɗaya-ɗaya a hankali, da mundaye a ƙafafunsu, suna cas-cas. |
18038 | ISA 15:8 | Ƙugin kukansu ya kai ko’ina a iyakar Mowab; kururuwarsu ta kai har zuwa Eglayim, makokinsu ya kai har zuwa Beyer-Elim. |
18233 | ISA 27:12 | A wannan rana Ubangiji zai tankaɗe daga Yuferites mai gudu zuwa Rafin Masar, ku kuma, ya Isra’ilawa, za a tattara ku ɗaya-ɗaya. |
18267 | ISA 29:4 | Za a ƙasƙantar da ke, za ki ƙi yin magana daga ƙasa; maganarki za tă yi ƙasa-ƙasa daga ƙura. Muryarki za tă zama kamar fatalwa daga ƙasa; daga ƙura maganarki zai fito ƙasa-ƙasa. |
18860 | ISA 58:4 | Azuminku yakan ƙare a faɗa da kuma hargitsi, kuna ta naushin juna da mugayen naushe-naushe. Ba za ku iya azumi kamar yadda kuke yi a yau ku zaci za a ji muryarku can sama. |
18875 | ISA 59:5 | Suna ƙyanƙyashe ƙwan kāsā su kuma saƙa yanar gizo-gizo. Duk wanda ya ci ƙwansu zai mutu, kuma sa’ad da ƙwan ya fashe, zai ƙyanƙyashe kububuwa. |
19155 | JER 5:28 | suka kuma yi ƙiba, suka yi bul-bul. Mugayen ayyukansu ba su da iyaka; ba sa wa marayu shari’ar adalci, ba sa kāre ’yancin matalauta. |
19186 | JER 6:28 | Su duka masu taurinkai ne, ’yan tawaye, suna yawo suna baza jita-jita. Su tagulla ne da ƙarfe; dukansu lalatattu ne. |
19448 | JER 17:22 | Kada ku fitar da kayan gidajenku ko ku yi wani aiki a ranar Asabbaci mai tsarki, yadda na umarci kakanni-kakanninku. |