339 | GEN 14:2 | suka tafi don su yaƙi Bera sarkin Sodom, Birsha sarkin Gomorra, Shinab sarkin Adma, Shemeber sarkin Zeboyim, da kuma sarkin Bela (wato, Zowar). |
340 | GEN 14:3 | Dukan waɗannan sarakuna na bayan nan suka haɗa kai a Kwarin Siddim (Teku Gishiri). |
354 | GEN 14:17 | Bayan Abram ya dawo daga cin Kedorlayomer da sarakunan da suka haɗa kai da shi a yaƙi, sai sarkin Sodom ya fito don yă tarye Abram a Kwarin Shabe (wato, Kwarin Sarki). |
1031 | GEN 35:19 | Ta haka Rahila ta rasu, aka kuma binne ta a hanya zuwa Efrata (wato, Betlehem). |
1042 | GEN 36:1 | Waɗannan su ne zuriyar Isuwa (wato, Edom). |
1459 | GEN 48:7 | Yayinda nake dawowa daga Faddan Aram, cikin baƙin cikina Rahila ta rasu a ƙasar Kan’ana yayinda muke kan hanya, ’yar rata daga Efrata. Saboda haka na binne ta a can kusa da hanya zuwa Efrata” (wato, Betlehem). |
1944 | EXO 15:23 | Da suka zo Mara, ba su iya shan ruwan ba saboda yana da ɗaci (shi ya sa ake kira wurin Mara). |
4109 | NUM 13:33 | Mun ga Nefilimawa a can (zuriyar Anak sun fito ne daga Nefilim). Sai muka ga kanmu kamar fāra ne kawai, haka kuwa muke a gare su.” |
6183 | JOS 13:27 | kuma a cikin kwari, Bet-Haram, Bet-Nimra, Sukkot da Zafon da kuma sauran masarautar Sihon sarkin Heshbon (gabashin Urdun, abin da ya kama har zuwa ƙarshen Tekun Kinneret). |
6187 | JOS 13:31 | da rabin Gileyad, da Ashtarot, Edireyi (biranen sarki Og a Bashan). Wannan shi ne rabon da zuriyar Makir ɗan Manasse suka samu, domin rabin ’ya’yan Makir maza, bisa ga iyalansu. |
6212 | JOS 15:8 | Sai kuma ta gangara zuwa Kwarin Ben Hinnom a gangaren kudancin birnin Yebusiyawa (wato, Urushalima). Daga can ta haura zuwa kan tudun a yammancin Kwarin Hinnom, a arewancin ƙarshen Kwarin Refayim. |
6213 | JOS 15:9 | Daga kan tudun, iyakar ta nufi maɓulɓular ruwa na Neftowa, ta ɓullo a garuruwan da suke a Dutsen Efron, ta gangara zuwa Ba’ala (wato, Kiriyat Yeyarim). |
6219 | JOS 15:15 | Daga can ya nufi Debir ya yi yaƙi da mutanen da suke zama a can (Dā sunan Debir, Kiriyat Sefer ne). |
6240 | JOS 15:36 | Sha’arayim, Aditayim, Gedera (Gederotayim ke nan). Garuruwa goma sha huɗu ke nan da ƙauyukansu. |
6288 | JOS 17:11 | A yanki tsakanin Issakar da Asher, Manasse yana da waɗannan wurare, Bet-Sheyan, Ibileyam da ƙauyukanta, da mazaunan Dor da ƙauyukanta, da mazaunan En Dor da ƙauyukanta, da mazaunan Ta’anak da ƙauyukanta, da mazaunan Megiddo da ƙauyukanta (Na uku cikin jerin shi ne Nafot). |
6522 | JDG 1:11 | Daga nan kuma suka ci gaba suka yaƙi mutanen da suke zaune a Debir (da ake kira a dā Kiriyat Sefer). |
8866 | 1KI 4:19 | Geber ɗan Uri, shi ne a Gileyad (ƙasar Sihon sarkin Amoriyawa da kuma Og sarkin Bashan). Shi ne kaɗai gwamna a bisa yankin. |
10283 | 1CH 1:27 | da Abram (wato, Ibrahim). |
10328 | 1CH 2:18 | Kaleb ɗan Hezron ya haifi yara ta wurin matarsa Azuba (da kuma ta wurin Yeriyot). Waɗannan su ne ’ya’yan Azuba maza. Yesher, Shobab da Ardon. |
10455 | 1CH 5:23 | Mutanen rabin kabilar Manasse sun yi yawa; suka zauna a ƙasar daga Bashan har zuwa Ba’al-Hermon, wato, zuwa Senir (Dutsen Hermon). |
10681 | 1CH 11:4 | Dawuda tare da dukan Isra’ilawa suka taka zuwa Urushalima (wato, Yebus). Yebusiyawan da suke zama a wurin |
11594 | 2CH 20:2 | Sai waɗansu mutane suka zo suka faɗa wa Yehoshafat, “Ga babban runduna tana zuwa a kanka daga Edom, daga ƙetaren Teku, daga Aram. Ta ma kai Hazazon Tamar” (wato, En Gedi). |
12093 | EZR 2:61 | Daga cikin firistoci kuma, zuriyar Hobahiya, Hakkoz da Barzillai (wanda ya auri diyar Barzillai mutumin Gileyad da ake kuma kira da wannan suna). |
12488 | NEH 7:63 | Na wajen firistoci kuwa su ne, Zuriyar Hobahiya, da ta Hakkoz, da ta Barzillai (wani mutumin da ya auri ’yar Barzillai mutumin Gileyad, aka kuma kira shi da wannan suna). |
12596 | NEH 11:4 | yayinda sauran mutane daga Yahuda da Benyamin suka zauna a Urushalima). Daga zuriyar Yahuda akwai, Atahiya ɗan Uzziya, ɗan Zakariya, ɗan Amariya, ɗan Shefatiya, ɗan Mahalalel, wani zuriyar Ferez; |
12864 | EST 9:26 | (Saboda haka, aka kira ranakun nan Furim, daga kalma fur). Saboda dukan abin da aka rubuta cikin wannan wasiƙa da kuma abin da suka gani, da abin da ya same su. |
13226 | JOB 15:19 | (waɗanda su ne masu ƙasar kafin baƙi su shigo ƙasar). |
18273 | ISA 29:10 | Ubangiji ya kawo muku barci mai nauyi, Ya rufe idanunku (annabawa); ya rufe kawunanku (masu duba). |
20929 | EZK 18:11 | (ko da yake mahaifin bai yi ko ɗaya daga cikinsu ba). “Yakan ci abinci a duwatsun tsafi. Yakan ƙazantar da matar maƙwabci. |
21713 | EZK 45:14 | Sashe na man da aka ƙayyade, da aka auna da garwa, kashi ɗaya bisa goma ne na garwa daga ganga (wanda yakan ci garwa goma, gama garwa goma suna daidai da ganga guda). |
21749 | EZK 47:1 | Mutumin ya komo da ni zuwa mashigin haikalin, sai na kuwa ga ruwa yana malalowa daga ƙarƙashin madogarar ƙofar haikalin wajen gabas (gama haikalin yana fuskantar gabas). Ruwan yana malalowa daga ƙarƙashin gefen kudun haikalin, kudu da bagaden. |
22501 | AMO 5:9 | yakan kawo hallaka a mafaka mai ƙarfi yakan kuma mai da birnin mai katanga ya zama kufai). |
24231 | MAT 27:33 | Sai suka iso wani wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai). |
24475 | MRK 5:42 | Nan da nan, sai yarinyar ta tashi ta yi tafiya (shekarunta goma sha biyu ne). Saboda wannan, suka yi mamaki ƙwarai. |
24917 | MRK 15:22 | Suka kawo Yesu a wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai). |
24937 | MRK 15:42 | Ranar kuwa ita ce ranar Shirye-shirye (wato, ana kashegari Asabbaci). Saboda haka, da yamma ta yi, sai |
26154 | JHN 1:41 | Abu na fari da Andarawus ya yi shi ne ya sami ɗan’uwansa Siman ya gaya masa cewa, “Mun sami Almasihu” (wato, Kiristi). |
26155 | JHN 1:42 | Ya kuma kawo shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi ya ce, “Kai ne Siman ɗan Yohanna. Za a ce da kai Kefas” (in an fassara, Bitrus ke nan). |
26907 | JHN 19:13 | Da Bilatus ya ji haka, sai ya fito da Yesu, ya kuma zauna a kujerar shari’ar da ake ce da shi Daɓen Dutse (wanda a harshen Arameyik ana ce da shi Gabbata). |
26911 | JHN 19:17 | Ɗauke da gicciyensa, ya kuwa fita zuwa wurin Ƙoƙon Kai (wanda a harshen Arameya ana ce da shi Golgota). |
28011 | ROM 1:13 | Ina so ku sani ’yan’uwa cewa na yi shirin zuwa wurinku sau da dama (amma aka hana ni yin haka sai yanzu). Na so in zo domin in sami mutane wa Kiristi a cikinku, kamar yadda na yi a cikin sauran Al’ummai. |
28263 | ROM 10:7 | “ko kuwa ‘Wa zai gangara can zurfin ƙasa?’ ” (wato, don yă hauro da Kiristi daga matattu). |
29307 | EPH 2:11 | Saboda haka, ku tuna dā ku Al’ummai ne bisa ga haihuwa, waɗanda kuma ake kira masu “kaciya” sukan kira ku “marasa kaciya” (ga shi kuwa, kaciyar nan ta jiki ce, wadda ake yi da hannu). |
30208 | HEB 10:8 | Da farko ya ce, “Hadayu da sadakoki, hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka so, ba ka kuwa jin daɗinsu” (ko da yake doka ta bukaci a yi su). |