1285 | GEN 42:32 | Dā mu ’yan’uwa ne goma sha biyu, ’ya’yan mahaifi guda maza. Ɗayanmu ya rasu, kuma ƙaramin yanzu yana tare da mahaifinmu a Kan’ana.’ |
2914 | LEV 7:34 | Daga hadaya ta salama ta Isra’ilawa, na ɗauki ƙirjin da aka kaɗa da kuma cinyar da aka miƙa, na ba da su ga Haruna firist da kuma ’ya’yansa maza a matsayin rabonsu na kullum daga Isra’ilawa.’ ” |
4282 | NUM 18:24 | A maimako haka, na ba wa Lawiyawa zakka da Isra’ilawa suka kawo domin hadaya ga Ubangiji, a matsayin gādonsu. Shi ya sa na ce game da su, ‘Ba su da gādo a cikin Isra’ilawa.’ ” |
4424 | NUM 23:7 | Sai Bala’am ya furta abin da Allah ya faɗa masa ya ce, “Balak ya kawo ni daga Aram, sarkin Mowab ya kawo ni daga gabashin duwatsu. Ya ce, ‘Zo, ka la’anta mini Yaƙub; zo, ka tsine Isra’ila.’ |
4881 | NUM 35:34 | Kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zama, wadda ni kuma nake zama a ciki, gama Ni Ubangiji, ina zama a cikin Isra’ilawa.’ ” |
8301 | 2SA 12:12 | Ka aikata wannan a ɓoye, amma zan aikata wannan da rana tsaka, a gaban dukan Isra’ila.’ ” |
9004 | 1KI 8:16 | ‘Tun ran da na fitar da mutanena Isra’ila daga Masar, ban zaɓi wani birni a cikin wata kabilar Isra’ila a gina haikali domin Sunana yă kasance a can ba, amma na zaɓi Dawuda yă yi mulkin mutanena Isra’ila.’ |
9763 | 2KI 9:3 | Sa’an nan ka ɗauki kwalabar man ka zuba a kansa, ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, na naɗa ka sarkin Isra’ila.’ Sa’an nan ka buɗe ƙofa ka ruga a guje; kada ka ɓata lokaci!” |
9772 | 2KI 9:12 | Suka ce masa, “Ba gaskiya ba ne, ka dai faɗa mana.” Yehu ya ce, “Ga abin da ya ce mini, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce, na naɗa ka sarki a bisa Isra’ila.’ ” |
10951 | 1CH 21:12 | shekara uku na yunwa, wata uku na shan ɗibga a gaban abokan gābanka, sa’ad da za su bi suna kakkashe ku, ko kuwa kwana uku na takobin Ubangiji, ranakun annoba a cikin ƙasar, mala’ikan Ubangiji zai hallaka kowane sashe na Isra’ila.’ Yanzu sai ka yanke shawara yadda zan amsa wa wanda ya aiko ni.” |
11293 | 2CH 6:6 | Amma yanzu na zaɓi Urushalima domin Sunana yă kasance a can, na kuma zaɓi Dawuda yă yi mulkin mutanena Isra’ila.’ |
19090 | JER 3:19 | “Ni kaina na faɗa, “ ‘Da farin ciki zan ɗauke ki kamar ’ya’yana maza in ba ki ƙasa mai daɗi, gādo mafi kyau da wata al’umma.’ Na zaci za ki kira ni ‘Mahaifi’ ba za ki ƙara rabuwa da bina ba. |
19767 | JER 31:7 | Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ku rera don farin ciki wa Yaƙub; ku yi sowa don al’ummai da suke nesa. Ka sa a ji yabanku, ku kuma ce, ‘Ya Ubangiji ka ceci mutanenka, raguwar Isra’ila.’ |
20151 | JER 48:2 | Ba za a ƙara yabi Mowab ba; a Heshbon mutane za su shirya mata maƙarƙashiya. ‘Zo, mu tafi mu kawo ƙarshe ga wannan al’umma.’ Ke kuma, ya Madmen za ki yi shiru; takobi zai fafare ki. |
20741 | EZK 11:17 | “Saboda haka, ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan tattaro ku daga al’ummai in kuma dawo da ku daga ƙasashen da aka warwatsa ku, zan kuwa sāke mayar muku da ƙasar Isra’ila.’ |
27743 | ACT 21:11 | Da ya zo wurinmu, sai ya ɗauki ɗamarar Bulus, ya ɗaura hannuwansa da ƙafafunsa da ita sa’an nan ya ce, “Ruhu Mai Tsarki ya ce, ‘Haka Yahudawan Urushalima za su daure mai wannan ɗamara su kuma ba da shi ga Al’ummai.’ ” |
27793 | ACT 22:21 | “Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, ‘Je ka; zan aike ka can nesa a wurin Al’ummai.’ ” |