989 | GEN 34:8 | Amma Hamor ya ce musu, “Ɗana Shekem ya sa zuciyarsa a kan ’yarku. Ina roƙonku ku ba shi ita yă aura. |
2082 | EXO 21:4 | In maigidansa ya yi masa aure, ta kuwa haifa masa ’ya’ya maza ko mata, matan da ’ya’yan, za su zama na maigidan, sai mutumin kaɗai zai tafi ’yantacce. |
2109 | EXO 21:31 | Wannan doka ta shafi batun bijimin da ya kashe ɗa ko ’ya. |
3269 | LEV 18:17 | “ ‘Kada ka yi jima’i da mace da kuma ’yarta. Kada ka yi jima’i da ’yar ɗanta ko ’yar ’yarta; su danginta ne na kusa. Wannan mugun abu ne. |
4564 | NUM 27:8 | “Ka faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘In wani ya mutu ba shi da ɗa, a ba da gādonsa ga ’yarsa. |
5796 | DEU 32:36 | Ubangiji zai shari’anta mutanensa yă kuma ji tausayin bayinsa sa’ad da ya ga ƙarfinsu ya ƙare babu kowa kuma da ya rage, bawa ko ’yantacce. |
6865 | JDG 11:34 | Sa’ad da Yefta ya komo gida a Mizfa, wa ya fito yă tarye shi, ’yarsa tilo, tana rawa kiɗin ganguna! Ita ce kaɗai ’yarsa. Ban da ita ba shi da ɗa ko ’ya. |
7184 | RUT 3:10 | Sai ya amsa ya ce, “Ubangiji yă albarkace ki ’yata. Wannan alheri ya fi wannan da kika nuna da farko. Ba ki gudu kin bi saurayi, mai arziki ko matalauci ba. |
8820 | 1KI 3:1 | Solomon ya haɗa kai da Fir’auna sarkin Masar, ya kuwa auri ’yarsa. Ya kawo ta cikin Birnin Dawuda kafin yă gama ginin fadarsa, da haikalin Ubangiji, da kuma katanga kewaye da Urushalima. |
9231 | 1KI 14:10 | “ ‘Saboda wannan, zan kawo masifa a gidan Yerobowam. Zan yanke kowane ɗa na ƙarshe a Isra’ila, bawa ko ’yantacce. Zan ƙone gidan Yerobowam kamar yadda mutum yakan ƙone juji, sai duk ya ƙone ƙurmus. |
9475 | 1KI 21:21 | ‘Zan kawo masifa a kanka. Zan kawar da zuriyarka, in kuma yanke daga Ahab kowane ɗa namiji na ƙarshe cikin Isra’ila, bawa ko ’yantacce. |
9768 | 2KI 9:8 | Dukan gidan Ahab zai hallaka. Zan kashe dukan ’ya’yan Ahab maza a Isra’ila, bayi ko ’yantattu. |
22742 | MIC 7:9 | Domin na yi masa zunubi, zan fuskanci fushin Ubangiji, har sai ya dubi batuna ya kuma tabbatar da ’yancina. Zai kawo ni zuwa wurin haske; zan ga adalcinsa. |
29242 | GAL 5:13 | Ku ’yan’uwana, an kira ku ga zama ’yantattu. Amma kada ku yi amfani da ’yancinku don aikata ayyukan mutuntaka a maimakon haka, ku yi hidimar juna da ƙauna. |
29412 | EPH 6:8 | Gama kun san cewa Ubangiji zai ba da lada ga kowa gwargwadon kowane aiki nagarin da ya yi, ko shi bawa ne, ko ’yantacce. |