23282 | MAT 4:4 | Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa, ‘Ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah.’” |
23284 | MAT 4:6 | Ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, yi tsalle ka sauka ƙasa. Gama a rubuce yake, “ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai, za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’” |
23285 | MAT 4:7 | Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’” |
23288 | MAT 4:10 | Sai Yesu ya ce masa, “Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake, ‘Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa.’” |
23850 | MAT 19:19 | ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ka kuma ‘ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’” |
24676 | MRK 10:19 | Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, kada ka cuci wani, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’” |
24726 | MRK 11:17 | Da yake koya musu, sai ya ce, “Ashe, ba a rubuce yake ba cewa, ‘Za a kira gidana, gidan addu’a na dukan al’ummai ba’?Amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’” |
25136 | LUK 4:4 | Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba.’” |
25140 | LUK 4:8 | Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta wa.’” |
25143 | LUK 4:11 | za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’” |
25144 | LUK 4:12 | Yesu ya amsa ya ce, “An ce, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’” |
26357 | JHN 6:31 | Kakannin-kakanninmu sun ci Manna a hamada; kamar yadda yake a rubuce, ‘Ya ba su burodi daga sama su ci.’” |
27472 | ACT 13:41 | “ ‘Ku duba, ku masu ba’a, ku yi mamaki, ku hallaka, gama zan yi wani abu a zamaninku da ba za ku taɓa gaskatawa ba ko da wani ya gaya muku.’” |
27478 | ACT 13:47 | Gama abin da Allah ya umarce mu ke nan cewa, “ ‘Na sa ka zama haske ga Al’ummai, don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya.’” |
27807 | ACT 23:5 | Bulus ya amsa ya ce, “’Yan’uwa, ai, ban san cewa shi ne babban firist ba; gama yana a rubuce cewa, ‘Kada ka yi mugun magana game da mai mulkin mutanenka.’” |