|
19884 | ‘A kowace shekara ta bakwai dole kowannenku yă ’yantar da duk wani ɗan’uwa mutumin Ibraniyawa wanda aka sayar masa. Bayan ya yi muku hidima shekaru shida, dole ku bar shi yă tafi ’yantacce.’ Amma kakanninku ba su saurare ni ba, ba su ji ni ba. |