606 | GEN 24:14 | Bari yă zama sa’ad da na ce wa wata yarinya, ‘Ina roƙonki ki saukar da tulunki domin in sha,’ in ta ce, ‘Ka sha, zan kuma ba wa raƙumanka ma’; bari tă zama ita ce ka zaɓa wa bawanka Ishaku. Ta haka zan san cewa ka nuna wa maigidana alheri.” |
9035 | 1KI 8:47 | in suka canja zuciyarsu a ƙasar da aka riƙe su kamammu, suka tuba, suka kuma roƙe ka a ƙasar waɗanda suka ci su da yaƙi, suka ce, ‘Mun yi zunubi, mun yi abin da ba daidai ba, mun yi mugunta’; |
9741 | 2KI 8:10 | Elisha ya amsa ya ce, “Je ka ce masa, ‘Ba shakka za ka warke’; ammaUbangiji ya nuna mini cewa ba shakka zai mutu.” |
11324 | 2CH 6:37 | Kuma in suka canja zuciya a cikin ƙasar da suke zaman bauta, suka tuba suka roƙe ka a ƙasar zaman bautarsu suka kuma ce, ‘Mun yi zunubi, mu yi abin da ba daidai ba, mu kuwa yi mugunta’; |
18530 | ISA 41:9 | na ɗauke ka daga iyakar duniya, daga kusurwoyi masu nesa na kira ka. Na ce, ‘Kai bawana ne’; na zaɓe ka ban kuwa ƙi ka ba. |
18608 | ISA 44:5 | Wani zai ce, ‘Ni na Ubangiji ne’; wani kuma zai kira kansa da sunan Yaƙub; har yanzu wani zai rubuta a hannunsa, ‘Na Ubangiji,’ ya kuma ɗauki sunan Isra’ila. |
19836 | JER 32:36 | “Kana cewa game da wannan birni, ‘Ta wurin takobi, yunwa da annoba za a ba da shi ga sarkin Babilon’; amma ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana cewa |
22197 | HOS 2:25 | Zan dasa ta wa kaina a ƙasar; zan shuka ƙaunata ga wanda na ce ‘Ba ƙaunatacciyata ba.’ Zan faɗa wa waɗanda a ce ‘Ba mutanena ba,’ ‘Ku mutanena ne’; za su kuwa ce, ‘Kai ne Allahna.’ ” |
24741 | MRK 11:32 | In kuma muka ce, ‘Daga wurin mutane ne’; suna jin tsoron mutane, don kowa ya ɗauka cewa, Yohanna, annabi ne na gaskiya.” |
25459 | LUK 10:27 | Sai ya amsa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka, da kuma dukan hankalinka’; kuma, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ ” |