8733 | 1KI 1:13 | Ki shiga wurin Sarki Dawuda ki ce masa, ‘Ranka yă daɗe sarki, ba ka rantse mini ni baiwarka cewa, “Tabbatacce Solomon ɗanka ne zai zama sarki bayana, yă kuma zauna a kujerar sarautar ba”? To, me ya sa Adoniya ya zama sarki?’ |
10050 | 2KI 18:22 | Sai ya ci gaba da cewa, in kuma ka ce mini “Muna dogara ga Ubangiji Allahnmu ne,” ba masujadansa da bagadansa ne Hezekiya ya ciccire, yana ce wa Urushalima da Yahuda, “Dole ku yi sujada a gaban wannan bagade a Urushalima”? |
14065 | PSA 10:13 | Don me mugun mutum zai ƙi Allah? Don me yakan ce wa kansa, “Allah ba zai nemi hakki daga gare ni ba”? |
17033 | PRO 20:9 | Wa zai iya cewa, “Na kiyaye zuciyata da tsarki; ni mai tsabta ne marar zunubi kuma”? |
17395 | ECC 1:10 | Akwai wani abin da za a ce, “Duba! Ga wani abu sabo”? Abin yana nan, tun dā can, ya kasance kafin lokacinmu. |
18085 | ISA 19:11 | Shugabannin Zowan ba kome ba ne, wawaye ke kawai; mashawarta masu hikima na Fir’auna suna ba da shawarwari marasa amfani. Yaya za ka ce wa Fir’auna, “Ni ɗaya ne cikin masu hikima, almajirin sarakuna na dā can”? |
18279 | ISA 29:16 | Kuna birkitar abubuwa, sai ka ce an mayar da mai ginin tukwane ya zama yumɓu! Abin da aka yi zai ce wa wanda ya yi shi, “Ba shi ne ya yi ni ba”? Tukunya za tă iya ce wa mai ginin tukwane, “Ba ka san kome ba”? |
18407 | ISA 36:7 | Kuma in ka ce mini, “Mun dogara ga Ubangiji Allahnmu ne” ba shi ba ne Hezekiya ya rurrushe masujadan kan tudunsa da bagadansa, yana ce wa Yahuda da Urushalima, “Dole ku yi sujada wa gaban wannan bagade”? |
18517 | ISA 40:27 | Ya Yaƙub, ya Isra’ila, me ya sa kake ce kana kuma gunaguni cewa, “Hanyata tana a ɓoye daga Ubangiji; Allah bai kula da abin da yake damuna ba”? |
28067 | ROM 3:8 | In haka ne, “Ba sai mu yi ta yin mugunta don yă zama hanyar samun nagarta ba”? Kamar yadda masu baƙar magana game da mu suna cewa wai haka muke faɗa. Tabbatacce za a hukunta irin waɗannan da hukuncin da ya dace da su. |
28280 | ROM 11:3 | “Ya Ubangiji, sun karkashe annabawanka suka kuma rurrushe bagadanka; ni kaɗai na ragu, suna kuma neman raina”? |
29582 | COL 2:21 | “Kada ka kama! Kada ka ɗanɗana! Kada ka taɓa”? |
30035 | HEB 1:5 | Gama ga wane daga cikin mala’ikun Allah ya taɓa cewa, “Kai Ɗana ne; yau na zama Uba a gare ka”? Ko kuwa, “Zan zama Ubansa, shi kuma zai zama Ɗana”? |
30043 | HEB 1:13 | Ga wane daga cikin mala’iku Allah ya taɓa cewa, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka”? |