555 | GEN 22:7 | sai Ishaku ya yi tambaya, ya ce wa mahaifinsa Ibrahim, “Baba?” Ibrahim ya ce masa, “Na’am ɗana!” Ishaku ya ce, “Ga dai wuta, ga kuma itace, amma ina ɗan ragon hadaya ta ƙonawa?” |
8786 | 1KI 2:13 | To, sai Adoniya, ɗan Haggit ya tafi wurin Batsheba mahaifiyar Solomon. Ita kuwa ta tambaye shi ta ce, “Lafiya?” Ya amsa ya ce, “I, lafiya.” |
9672 | 2KI 5:21 | Saboda haka Gehazi ya bi Na’aman a guje. Da Na’aman ya hango shi yana zuwa a guje, sai ya sauka daga keken yaƙinsa ya tarye shi ya ce, “Lafiya?” |
23849 | MAT 19:18 | Mutumin ya yi tambaya ya ce, “Waɗanne?” Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar ƙarya, |