11 | GEN 1:11 | Sa’an nan Allah ya ce, “Bari ƙasa tă fid da tsire-tsire, da shuke-shuke, da itatuwa a bisa ƙasa masu ba da amfani da ’ya’ya a cikinsu, bisa ga irinsu.” Haka kuwa ya kasance. |
26 | GEN 1:26 | Sa’an nan Allah ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, cikin kamanninmu, bari kuma su yi mulki a bisa kifin teku, tsuntsayen sama, da kuma dabbobi, su yi mulki a bisa dukan duniya, da kuma a bisa dukan halittu, da masu rarrafe a ƙasa.” |
29 | GEN 1:29 | Sa’an nan Allah ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da ’ya’ya masu kwaya da suke a fāɗin duniya, da dukan itatuwa masu ba da ’ya’ya, don su zama abinci a gare ku. |
35 | GEN 2:4 | Wannan shi ne asalin tarihin sammai da duniya sa’ad da aka halicce su. Sa’ad da Ubangiji Allah ya yi duniya da sammai, |
37 | GEN 2:6 | amma dai rafuffuka suna ɓullo da ruwa daga ƙasa suna jiƙe ko’ina a fāɗin ƙasa. |
38 | GEN 2:7 | Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mutum daga turɓayar ƙasa, ya kuma hura numfashin rai cikin hancinsa, mutumin kuwa ya zama rayayyen taliki. |
53 | GEN 2:22 | Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙarƙarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin. |
61 | GEN 3:5 | Gama Allah ya san cewa sa’ad da kuka ci daga itacen idanunku za su buɗe, za ku kuma zama kamar Allah, ku san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu.” |
62 | GEN 3:6 | Sa’ad da macen ta ga ’ya’yan itacen suna da kyau don abinci, abin sha’awa ga ido, abin marmari kuma don samun hikima, sai ta tsinka ta ci, ta kuma ba da waɗansu wa mijinta wanda yake tare da ita, shi ma ya ci. |
63 | GEN 3:7 | Sa’an nan idanun dukansu biyu suka buɗe, suka kuma gane tsirara suke; saboda haka suka ɗinɗinka ganyayen ɓaure suka yi wa kansu sutura. |
70 | GEN 3:14 | Saboda haka Ubangiji Allah ya ce wa macijin, “Saboda ka yi haka, “Na la’anta ka cikin dukan dabbobi da kuma cikin dukan namun jeji! Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya turɓaya kuma za ka ci dukan kwanakin rayuwarka. |
72 | GEN 3:16 | Sa’an nan ya ce wa macen, “Zan tsananta naƙudarki ainun, da azaba kuma za ki haifi ’ya’ya. Za ki riƙa yin marmarin mijinki zai kuwa yi mulki a kanki.” |
73 | GEN 3:17 | Ga Adamu kuwa ya ce, “Saboda ka saurari matarka, ka kuma ci daga itacen da na ce, ‘Kada ka ci,’ “Za a la’anta ƙasa saboda kai. Da wahala za ka ci daga cikinta dukan kwanakin rayuwarka. |
82 | GEN 4:2 | Daga baya ta haifi ɗan’uwansa, ta kuma ba shi suna Habila. Sa’ad da suka yi girma sai Habila ya zama makiyayin tumaki, Kayinu kuwa ya zama manomi. |
88 | GEN 4:8 | To, Kayinu ya ce wa ɗan’uwansa Habila, “Mu tafi gona.” Yayinda suke a gona, sai Kayinu ya tasar wa Habila ya buge shi ya kashe. |
89 | GEN 4:9 | Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina ɗan’uwanka Habila?” Sai Kayinu ya ce, “Ban sani ba, ni mai gadin ɗan’uwana ne?” |
90 | GEN 4:10 | Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Saurara! Ga jinin ɗan’uwanka yana mini kuka daga ƙasa. |
91 | GEN 4:11 | Yanzu, kai la’ananne ne, an kuma kore ka daga ƙasa wadda ta buɗe bakinta ta shanye jinin ɗan’uwanka daga hannunka. |
95 | GEN 4:15 | Amma Ubangiji ya ce masa, “Ba haka ba ne! Duk wanda ya kashe Kayinu, za a ninƙa hukuncinsa har sau bakwai.” Sa’an nan Ubangiji ya sa wa Kayinu alama don duk wanda ya same shi kada yă kashe shi. |
101 | GEN 4:21 | Sunan ɗan’uwansa Yubal, shi ne mahaifin dukan makaɗan garaya da masu hura sarewa. |
104 | GEN 4:24 | Idan za a rama wa Kayinu har sau bakwai, lalle za a rama wa Lamek sau saba’in da bakwai ke nan.” |
107 | GEN 5:1 | Wannan shi ne rubutaccen tarihin zuriyar Adamu. Sa’ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin kamannin Allah. |
108 | GEN 5:2 | Ya halicce su namiji da ta mace, ya kuma albarkace su. Sa’ad da kuma aka halicce su, ya kira su “Mutum.” |
109 | GEN 5:3 | Sa’ad da Adamu ya yi shekaru 130, sai ya haifi ɗa wanda ya yi kama da shi, ya kuma kira shi Set. |
111 | GEN 5:5 | Gaba ɗaya dai, Adamu ya yi shekaru 930, sa’an nan ya mutu. |
112 | GEN 5:6 | Sa’ad da Set ya yi shekara 105, sai ya haifi Enosh. |
114 | GEN 5:8 | Gaba ɗaya dai, Set ya yi shekaru 912, sa’an nan ya mutu. |
115 | GEN 5:9 | Sa’ad da Enosh ya yi shekara 90, sai ya haifi Kenan. |
117 | GEN 5:11 | Gaba ɗaya dai, Enosh ya yi shekaru 905, sa’an nan ya mutu. |
118 | GEN 5:12 | Sa’ad da Kenan ya yi shekara 70, sai ya haifi Mahalalel. |
120 | GEN 5:14 | Gaba ɗaya dai, Kenan ya yi shekara 910, sa’an nan ya mutu. |
121 | GEN 5:15 | Sa’ad da Mahalalel ya yi shekara 65, sai ya haifi Yared. |
123 | GEN 5:17 | Gaba ɗaya dai, Mahalalel ya yi shekara 895, sa’an nan ya mutu. |
124 | GEN 5:18 | Sa’ad da Yared ya yi shekara 162, sai ya haifi Enok. |
126 | GEN 5:20 | Gaba ɗaya dai, Yared ya yi shekara 962, sa’an nan ya mutu. |
127 | GEN 5:21 | Sa’ad da Enok ya yi shekara 65, sai ya haifi Metusela. |
130 | GEN 5:24 | Enok ya kasance cikin zumunci da Allah, sa’an nan ba a ƙara ganinsa ba. Saboda Allah ya ɗauke shi. |
131 | GEN 5:25 | Sa’ad da Metusela ya yi shekara 187, sai ya haifi Lamek. |
133 | GEN 5:27 | Gaba ɗaya dai, Metusela ya yi shekaru 969, sa’an nan ya mutu. |
134 | GEN 5:28 | Sa’ad da Lamek ya yi shekara 182, sai ya haifi ɗa. |
135 | GEN 5:29 | Ya ba shi suna Nuhu ya kuma ce, “Zai yi mana ta’aziyya a cikin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la’anta.” |
137 | GEN 5:31 | Gaba ɗaya dai, Lamek ya yi shekaru 777, sa’an nan ya mutu. |
139 | GEN 6:1 | Sa’ad da mutane suka fara ƙaruwa a duniya, aka kuma hahhaifi musu ’ya’ya mata, |
141 | GEN 6:3 | Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Ruhuna ba zai zauna a cikin mutum har abada ba, saboda shi mai mutuwa ne, kwanakinsa za su zama shekaru ɗari da arba’in ne.” |
142 | GEN 6:4 | Nefilimawa suna nan a duniya a waɗancan kwanaki, da kuma kwanakin da suka bi baya, a sa’ad da ’ya’yan Allah suka kwana da ’ya’yan mutane mata, suka kuma hahhaifi musu ’ya’ya. Ai, su ne jarumawan dā, mutanen da suka shahara. |
161 | GEN 7:1 | Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Nuhu. “Shiga jirgin, kai da dukan iyalinka, gama na ga kai mai adalci ne a wannan zamani. |
164 | GEN 7:4 | Kwana bakwai daga yanzu zan aiko da ruwa a duniya yini arba’in da dare arba’in, zan kuma kawar da kowace halitta mai rai da na yi daga doron ƙasa.” |
166 | GEN 7:6 | Nuhu yana da shekaru 106 ne sa’ad da aka yi ambaliya ruwa a duniya. |
172 | GEN 7:12 | Ruwa yana ta kwararowa bisa duniya, yini arba’in da dare arba’in. |
176 | GEN 7:16 | Dabbobi da kowane abu mai rai da suka shiga ciki, namiji ne da ta mace, yadda Allah ya umarci Nuhu. Sa’an nan Ubangiji ya kulle jirgin daga baya. |
177 | GEN 7:17 | Kwana arba’in ambaliya ta yi ta saukowa a duniya, sa’ad da ruwa ya yi ta ƙaruwa sai ya yi ta ɗaga jirgin sama, ya kuwa tashi can bisa duniya. |
195 | GEN 8:11 | Sa’ad da kurciya ta komo wurinsa da yamma, sai ga ɗanyen ganyen zaitun da ta tsinko a bakinta! Sa’an nan Nuhu ya san cewa ruwa ya janye daga duniya. |
199 | GEN 8:15 | Sa’an nan Allah ya ce wa Nuhu, |
205 | GEN 8:21 | Da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce a zuciyarsa, “Ba zan ƙara la’anta ƙasa saboda mutum ba, ko da yake dukan tunanin zuciyar mutum mugu ne tun yana ƙarami. Ba kuwa zan ƙara hallaka dukan halittu masu rai, kamar yadda na yi ba. |
207 | GEN 9:1 | Sa’an nan Allah ya sa wa Nuhu da ’ya’yansa maza albarka, yana ce musu, “Ku haifi ’ya’ya, ku ƙaru, ku kuma cika duniya. |
220 | GEN 9:14 | Duk sa’ad da na kawo gizagizai a bisa duniya, bakan gizo kuma ya bayyana a ciki gizagizan, |
222 | GEN 9:16 | Duk sa’ad da bakan gizo ya bayyana cikin gizagizan, zan gan shi in kuma tuna da madawwamin alkawari tsakanin Allah da dukan halittu masu rai, na kowane iri a duniya.” |
227 | GEN 9:21 | Sa’ad da ya sha ruwan inabin ya kuwa bugu, sai ya kwanta tsirara cikin tentinsa. |
228 | GEN 9:22 | Ham, mahaifin Kan’ana ya ga tsiraici mahaifinsa, ya kuma faɗa wa ’yan’uwansa biyu a waje. |
229 | GEN 9:23 | Amma Shem da Yafet suka ɗauki mayafi, suka shimfiɗa a kafaɗarsu, sa’an nan suka shiga suna tafiya da baya har zuwa inda mahaifinsu yake kwance, suka rufe tsiraicinsa. Suka kau da fuskokinsu domin kada su ga tsiraicin mahaifinsu. |
230 | GEN 9:24 | Sa’ad da Nuhu ya farka daga buguwarsa ya kuma gane abin da ƙarami ɗansa ya yi, |
231 | GEN 9:25 | sai ya ce, “Kan’ana la’ananne ne, zai zama bawa mafi ƙanƙanta ga ’yan’uwansa.” |
232 | GEN 9:26 | Ya kuma ce, “Albarka ta tabbata ga Ubangiji Allah na Shem! Bari Kan’ana yă zama bawan Shem. |
233 | GEN 9:27 | Allah yă ƙara fāɗin ƙasar Yafet; bari Yafet yă zauna a tentunan Shem, bari kuma Kan’ana yă zama bawansa.” |
235 | GEN 9:29 | Gaba ɗaya dai, Nuhu ya yi shekara 950, sa’an nan ya mutu. |
242 | GEN 10:7 | ’Ya’yan Kush maza su ne, Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka. ’Ya’yan Ra’ama maza kuwa su ne, Sheba da Dedan. |
250 | GEN 10:15 | Kan’ana shi ne mahaifin, Sidon ɗan farinsa, da na Hittiyawa, |
253 | GEN 10:18 | Arbadiyawa, Zemarawa, da Hamawa. Daga baya zuriyar Kan’aniyawa suka yaɗu |
254 | GEN 10:19 | har iyakar Kan’ana ta kai Sidon ta wajen Gerar har zuwa Gaza, sa’an nan ta milla zuwa Sodom, Gomorra, Adma da Zeboyim, har zuwa Lasha. |
260 | GEN 10:25 | Aka haifa wa Eber ’ya’ya maza biyu. Aka ba wa ɗaya suna Feleg, gama a zamaninsa ne aka raba duniya; aka kuma sa wa ɗan’uwansa suna Yoktan. |
267 | GEN 10:32 | Waɗannan su ne zuriyar ’ya’yan Nuhu maza bisa ga jerin zuriyarsu cikin al’ummominsu. Daga waɗannan ne al’ummomi suka bazu ko’ina a duniya bayan ambaliya. |
271 | GEN 11:4 | Sa’an nan suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni da hasumiyar da za tă kai har sammai, domin mu yi wa kanmu suna, don kada mu warwatsu ko’ina a doron ƙasa.” |
273 | GEN 11:6 | Ubangiji ya ce, “Ga su, su jama’a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne. Wannan kuwa masomi ne kawai na abin da za su iya yi, babu kuma abin da suka yi shirya yi da ba za su iya yi ba. |
275 | GEN 11:8 | Saboda haka Ubangiji ya watsar da su daga wurin zuwa ko’ina a doron ƙasa, suka kuwa daina gina birnin. |
276 | GEN 11:9 | Shi ya sa aka kira birnin Babel, domin a can ne Ubangiji ya rikitar da harshen dukan duniya. Daga can Ubangiji ya watsar da su ko’ina a doron ƙasa. |
277 | GEN 11:10 | Wannan shi ne labarin Shem. Shekara biyu bayan ambaliya, sa’ad da Shem ya yi shekara 100, sai ya haifi Arfakshad. |
279 | GEN 11:12 | Sa’ad da Arfakshad ya yi shekara 35, sai ya haifi Shela. |
281 | GEN 11:14 | Sa’ad da Shela ya yi shekaru 30, sai ya haifi Eber. |
283 | GEN 11:16 | Sa’ad da Eber ya yi shekaru 34, sai ya haifi Feleg. |
285 | GEN 11:18 | Sa’ad da Feleg ya yi shekaru 30, sai ya haifi Reyu. |
287 | GEN 11:20 | Sa’ad da Reyu ya yi shekaru 32, sai ya haifi Serug. |
289 | GEN 11:22 | Sa’ad da Serug ya yi shekaru 30, sai ya haifi Nahor. |
291 | GEN 11:24 | Sa’ad da Nahor ya yi shekaru 29, sai ya haifi Tera. |
298 | GEN 11:31 | Tera ya ɗauki ɗansa Abraham, jikansa Lot ɗan Haran, da surukarsa Saira, matar Abram, tare kuwa suka bar Ur ta Kaldiyawa, don su tafi Kan’ana. Amma sa’ad da suka zo Haran sai suka zauna a can. |
301 | GEN 12:2 | “Zan mai da kai al’umma mai girma, zan kuma albarkace ka; zan sa sunanka yă zama mai girma, ka kuma zama sanadin albarka. |
302 | GEN 12:3 | Zan albarkaci duk wanda ya albarkace ka, in kuma la’anci duk wanda ya la’anta ka, dukan mutanen duniya za su sami albarka ta wurinka.” |
303 | GEN 12:4 | Saboda haka Abram ya tashi yadda Ubangiji ya faɗa masa; Lot ma ya tafi tare da shi. Abram yana da shekaru 75, sa’ad da ya tashi daga Haran. |
305 | GEN 12:6 | Abram ya ratsa ƙasar har zuwa wurin babban itace na More a Shekem. A lokacin Kan’aniyawa suna a ƙasar. |
308 | GEN 12:9 | Sa’an nan Abram ya tashi ya ci gaba da tafiya zuwa wajen Negeb. |
311 | GEN 12:12 | Sa’ad da Masarawa suka ganki, za su ce, ‘Wannan matarsa ce.’ Za su kuwa kashe ni, su bar ki da rai. |
313 | GEN 12:14 | Sa’ad da Abram ya isa Masar, Masarawa suka ga cewa Saira kyakkyawa mace ce ƙwarai. |
314 | GEN 12:15 | Sa’ad da fadawan Fir’auna suka gan ta kuwa, sai suka yabe ta wajen Fir’auna, aka kuwa kawo ta cikin fadarsa. |
316 | GEN 12:17 | Amma Ubangiji ya wahalar da Fir’auna da gidansa da cututtuka masu zafi saboda Saira, matar Abram. |
317 | GEN 12:18 | Saboda haka Fir’auna ya kira Abram ya ce, “Me ke nan ka yi mini? Me ya sa ba ka faɗa mini cewa ita matarka ce ba? |
319 | GEN 12:20 | Sa’an nan Fir’auna ya yi wa mutanensa umarni a kan Abram, suka kuwa sallame shi tare da matarsa da kuma dukan abin da yake da shi. |
326 | GEN 13:7 | Rikici kuma ya tashi tsakanin masu kiwon dabbobin Abram da na Lot. Mazaunan ƙasar, a lokacin kuwa Kan’aniyawa da Ferizziyawa ne. |
344 | GEN 14:7 | Sa’an nan suka juya suka tafi En Mishfat (wato, Kadesh), suka cinye dukan ƙasar Amalekawa, da kuma Amoriyawa waɗanda suke zaune a Hazazon Tamar. |
347 | GEN 14:10 | Kwarin Siddim kuwa ya cika da ramummukan kwalta, sa’ad da sarakunan Sodom da Gomorra suka gudu kuwa, waɗansu mutane suka fāɗa cikin ramummukan kwaltan, sauran kuwa suka gudu zuwa tuddai. |
348 | GEN 14:11 | Sarakunan nan huɗu suka washe dukan kayayyakin Sodom da Gomorra, da kuma dukan abincinsu, sa’an nan suka tafi. |
349 | GEN 14:12 | Suka kuma kama Lot ɗan ɗan’uwan Abram, wanda yake zaune a Sodom, da kayayyakinsa, suka yi tafiyarsu. |