2 | GEN 1:2 | To, ƙasa dai ba ta da siffa, babu kuma kome a cikinta, duhu ne kawai ya rufe ko’ina, Ruhun Allah kuwa yana yawo a kan ruwan. |
76 | GEN 3:20 | Mutumin ya sa wa matarsa suna, Hawwa’u, gama za tă zama mahaifiyar masu rai duka. |
77 | GEN 3:21 | Ubangiji Allah ya yi tufafin fata domin Adamu da Hawwa’u, ya kuma yi musu sutura. |
81 | GEN 4:1 | Adamu ya kwana da matarsa Hawwa’u, ta kuwa yi ciki ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Da taimakon Ubangiji na sami ɗa namiji.” |
82 | GEN 4:2 | Daga baya ta haifi ɗan’uwansa, ta kuma ba shi suna Habila. Sa’ad da suka yi girma sai Habila ya zama makiyayin tumaki, Kayinu kuwa ya zama manomi. |
140 | GEN 6:2 | sai ’ya’yan Allah maza suka ga cewa ’ya’yan mutane mata suna da bansha’awa, sai suka zaɓi waɗanda suke so, suka aura. |
164 | GEN 7:4 | Kwana bakwai daga yanzu zan aiko da ruwa a duniya yini arba’in da dare arba’in, zan kuma kawar da kowace halitta mai rai da na yi daga doron ƙasa.” |
190 | GEN 8:6 | Bayan kwana arba’in, sai Nuhu ya buɗe tagar jirgin da ya yi, |
240 | GEN 10:5 | (Daga waɗannan mutane ne masu zama a bakin teku suka bazu zuwa cikin ƙasashensu da kuma cikin al’ummansu, kowanne da yarensa.) |
304 | GEN 12:5 | Abram ya ɗauki matarsa Saira da Lot ɗan ɗan’uwansa, da dukan mallakar da suka tattara, da kuma mutanen da suka samu a Haran, suka kama hanya zuwa ƙasar Kan’ana. |
314 | GEN 12:15 | Sa’ad da fadawan Fir’auna suka gan ta kuwa, sai suka yabe ta wajen Fir’auna, aka kuwa kawo ta cikin fadarsa. |
331 | GEN 13:12 | Abram ya zauna a ƙasar Kan’ana, yayinda Lot ya zauna cikin biranen kwari, ya kafa tentunansa kusa da Sodom. |
382 | GEN 15:21 | Amoriyawa, Kan’aniyawa, Girgashiyawa da kuma Yebusiyawa.” |
503 | GEN 20:7 | Yanzu ka komar da matar mutumin, gama shi annabi ne, zai kuma yi maka addu’a, za ka kuwa rayu. In ba ka komar da ita ba fa, ka sani tabbatacce kai da dukan abin da yake naka za ku mutu.” |
568 | GEN 22:20 | Bayan wani ɗan lokaci, sai aka faɗa wa Ibrahim cewa, “Ga shi, Milka ita ma ta haifa wa Nahor ɗan’uwanka, ’ya’ya maza; |
574 | GEN 23:2 | Ta rasu a Kiriyat Arba (wato, Hebron) a ƙasar Kan’ana, Ibrahim kuwa ya tafi ya yi makokin Saratu, yana kuka saboda ita. |
595 | GEN 24:3 | Ina so ka rantse da sunan Ubangiji Allah na sama da ƙasa, cewa ba za ka samo wa ɗana mata daga ’yan matan Kan’aniyawa, waɗanda nake zama cikinsu ba. |
607 | GEN 24:15 | Kafin ya gama addu’a, sai Rebeka ta fito da tulu a kafaɗarta. Ita ’yar Betuwel ɗan Milka, matar Nahor, ɗan’uwan Ibrahim. |
629 | GEN 24:37 | Maigidana ya sa na yi rantsuwa, ya kuma ce, ‘Kada ka ɗauko wa ɗana mata daga ’ya’ya matan Kan’aniyawa, waɗanda nake zama a ƙasarsu, |
637 | GEN 24:45 | “Kafin in gama addu’ar, a zuciyata, sai ga Rebeka ta fito da tulunta a kafaɗarta. Ta gangara zuwa rijiyar ta ɗebo ruwa, na kuma ce mata, ‘Ina roƙonki ki ba ni ɗan ruwa daga tulunki.’ |
680 | GEN 25:21 | Ishaku ya yi addu’a ga Ubangiji a madadin matarsa, saboda ba ta haihuwa. Ubangiji ya amsa addu’arsa, matarsa Rebeka kuwa ta yi ciki. |
792 | GEN 28:18 | Kashegari da sassafe, sai Yaƙub ya ɗauki dutsen da ya yi matashin kai da shi, ya kafa shi al’amudi, ya kuma zuba mai a kansa. |
796 | GEN 28:22 | kuma wannan dutsen da na kafa al’amudi, zai zama gidan Allah, kuma dukan abin da ka ba ni zan ba ka kashi ɗaya bisa goma.” |
938 | GEN 32:10 | Sa’an nan Yaƙub ya yi addu’a, “Ya Allah na mahaifina Ibrahim, Allah na mahaifina Ishaku. Ya Ubangiji kai da ka ce mini, ‘Koma ƙasarka zuwa wurin danginka, zan kuma sa ka yi albarka.’ |
957 | GEN 32:29 | Sai mutumin ya ce, “Sunanka ba zai ƙara zama Yaƙub ba, amma Isra’ila, gama ka yi kokawa da Allah da mutane, ka kuwa yi rinjaye.” |
979 | GEN 33:18 | Bayan Yaƙub ya zo daga Faddan Aram, ya iso lafiya a birnin Shekem a Kan’ana, ya kuma kafa sansani a ƙofar birni. |
991 | GEN 34:10 | Za ku iya zauna a cikinmu, ƙasar tana nan a buɗe dominku. Ku yi zama a cikinta, ku yi sana’a, ku kuma sami dukiya.” |
1043 | GEN 36:2 | Isuwa ya ɗauko matansa daga cikin matan Kan’ana, ya ɗauko Ada ’yar Elon mutumin Hitti, da Oholibama ’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon Bahiwiye |
1122 | GEN 38:2 | A can Yahuda ya sadu da ’yar wani Bakan’ane, mai suna Shuwa. Ya aure ta, ya kuma kwana da ita; |
1129 | GEN 38:9 | Amma Onan ya san cewa ’ya’yan ba za su zama nasa ba; saboda haka a duk sa’ad da ya kwana da matar ɗan’uwansa, sai yă zub da maniyyinsa a ƙasa don kada yă samar wa ɗan’uwansa ’ya’ya. |
1151 | GEN 39:1 | To, aka kai Yusuf Masar, Fotifar wani mutumin Masar wanda yake ɗaya daga cikin hafsoshin Fir’auna, shugaban masu tsaro, ya saye shi daga mutanen Ishmayel waɗanda suka kai shi can. |
1180 | GEN 40:7 | Saboda haka ya tambayi hafsoshin Fir’auna, waɗanda suke a kurkuku tare da shi, a gidan maigidansa ya ce, “Me ya sa fuskokinku suke a ɓace haka?” |
1184 | GEN 40:11 | Kwaf Fir’auna kuwa yana a hannuna, na kuma ɗiba inabin na matse su cikin kwaf Fir’auna, na kuma sa kwaf ɗin a hannunsa.” |
1187 | GEN 40:14 | Amma fa, sa’ad da kome ya zama maka da kyau, ka tuna da ni, ka kuma yi mini alheri, ka ambace ni wa Fir’auna, ka fid da ni daga wannan kurkuku. |
1190 | GEN 40:17 | A kwandon na bisa, akwai kayan iri-iri da aka toya, masu kyau domin Fir’auna, amma tsuntsaye suka ci su a kwandon da yake kaina.” |
1193 | GEN 40:20 | To, a rana ta uku ne, ranar tunawa da haihuwar Fir’auna, ya kuwa yi biki wa dukan hafsoshinsa. Ya fid da shugaban masu shayarwa da kuma shugaban masu tuya a gaban hafsoshinsa. |
1194 | GEN 40:21 | Ya mai da shugaban masu shayarwa a matsayinsa, saboda haka shugaban masu shayarwa ya sāke sa kwaf a hannun Fir’auna, |
1205 | GEN 41:9 | Sai shugaban masu shayarwa ya ce wa Fir’auna, “Yau an tuna mini da kāsawata. |
1221 | GEN 41:25 | Sai Yusuf ya ce wa Fir’auna, “Mafarkan Fir’auna, ɗaya ne. Allah ya bayyana wa Fir’auna abin da yake shirin yi. |
1231 | GEN 41:35 | Ya kamata su tara dukan abincin waɗannan shekaru masu kyau da suke zuwa, su yi ajiyar hatsin a ƙarƙashin ikon Fir’auna, don a ajiye a birane don abinci. |
1240 | GEN 41:44 | Sa’an nan Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Ni ne Fir’auna, amma in ba tare da umarninka ba, ba wanda zai ɗaga hannu ko ƙafa a cikin dukan Masar.” |
1242 | GEN 41:46 | Yusuf yana zuwa shekara talatin sa’ad da ya shiga hidimar Fir’auna sarkin Masar. Yusuf kuwa ya fita daga gaban Fir’auna, ya zaga ko’ina a Masar. |
1260 | GEN 42:7 | Nan da nan da Yusuf ya ga ’yan’uwansa, sai ya gane su, amma ya yi kamar baƙo, ya kuma yi musu magana da tsawa. Ya tambaya, “Daga ina kuka fito?” Suka amsa, “Daga ƙasar Kan’ana, don mu saya abinci.” |
1269 | GEN 42:16 | Ku aiki ɗaya daga cikinku yă kawo ɗan’uwanku; za a sa sauranku a kurkuku, saboda a gwada maganarku a ga ko gaskiya ce kuke faɗi. In ba haka ba, to, da ran Fir’auna, ku ’yan leƙen asiri ne!” |
1282 | GEN 42:29 | Sa’ad da suka zo wurin mahaifinsu Yaƙub a ƙasar Kan’ana, suka faɗa masa dukan abin da ya faru da su. Suka ce, |
1287 | GEN 42:34 | Amma ku kawo mini ƙaramin ɗan’uwanku domin in san cewa ku ba ’yan leƙen asiri ba ne, amma mutane ne masu gaskiya. Sa’an nan zan mayar muku da ɗan’uwanku, ku kuma iya yin sana’a a ƙasar.’ ” |
1320 | GEN 43:29 | Da ya ɗaga idanu, sai ya ga ɗan’uwansa Benyamin, ɗan mahaifiyarsa, sai ya yi tambaya, “Wannan ne ƙaramin ɗan’uwanku, wanda kuka faɗa mini a kai?” Ya kuma ce, “Allah yă yi maka albarka, ɗana.” |
1321 | GEN 43:30 | Saboda motsi mai zurfi da zuciyarsa ta yi da ganin ɗan’uwansa, sai Yusuf ya gaggauta ya fita, ya nemi wuri yă yi kuka. Ya shiga ɗakinsa ya yi kuka a can. |
1367 | GEN 45:8 | “Saboda haka fa, ba ku ba ne kuka aiko ni nan, Allah ne. Ya mai da ni mahaifi ga Fir’auna, shugaban dukan gidansa da kuma mai mulkin dukan Masar. |
1376 | GEN 45:17 | Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Faɗa wa ’yan’uwanka, ‘Yi wannan; ku jibge dabbobinku ku koma zuwa ƙasar Kan’ana, |
1393 | GEN 46:6 | Suka kuma ɗauki dabbobinsu da mallakarsu, da suka samu a Kan’ana, Yaƙub kuwa da dukan zuriyarsa suka tafi Masar. |
1408 | GEN 46:21 | ’Ya’yan Benyamin maza su ne, Bela, Beker, Ashbel, Gera, Na’aman, Ehi, Rosh, Muffim, Huffim da Ard. |
1418 | GEN 46:31 | Sa’an nan Yusuf ya ce wa ’yan’uwansa da gidan mahaifinsa, “Zan haura in yi magana da Fir’auna, zan kuwa ce masa, ‘’Yan’uwana da gidan mahaifina, waɗanda suke zaune a ƙasar Kan’ana, sun zo wurina. |
1422 | GEN 47:1 | Yusuf ya tafi yă faɗa wa Fir’auna, “Mahaifina da ’yan’uwana, tare da garkunansu da shanunsu da kome da suke da shi, sun zo daga ƙasar Kan’ana, suna kuwa a Goshen yanzu.” |
1425 | GEN 47:4 | Suka kuma ce masa, “Mun zo, mu zauna a nan na ɗan lokaci, gama yunwa ta yi tsanani a Kan’ana, dabbobin bayinka kuma ba su da wurin kiwo. Saboda haka yanzu, muna roƙonka, bari bayinka su zauna a Goshen.” |
1428 | GEN 47:7 | Sa’an nan Yusuf ya shigar da Yaƙub mahaifinsa, ya gabatar da shi a gaban Fir’auna. Bayan Yaƙub ya albarkaci Fir’auna, |
1430 | GEN 47:9 | Yaƙub kuwa ya ce wa Fir’auna, “Shekarun hijirata, shekaru ɗari da talatin ne. Shekaruna kaɗan ne cike da wahala, ba za a kuwa daidaita su da shekarun hijirar kakannina ba.” |
1431 | GEN 47:10 | Sai Yaƙub ya albarkaci Fir’auna, ya yi masa bankwana, sa’an nan ya fita. |
1444 | GEN 47:23 | Yusuf ya ce wa mutane, “Yanzu da na saye ku da kuma gonakinku a yau wa Fir’auna, ga iri don ku shuka a gonaki. |
1455 | GEN 48:3 | Yaƙub ya ce wa Yusuf, “Allah Maɗaukaki ya bayyana gare ni a Luz a ƙasar Kan’ana, a can ya albarkace ni |
1465 | GEN 48:13 | Yusuf ya ɗauke su biyu, Efraim a damansa zuwa hagun Isra’ila, Manasse kuma a hagunsa zuwa hannun daman Isra’ila, ya kuma kawo su kusa da shi. |
1498 | GEN 49:24 | Amma bakansa yana nan daram hannuwansa masu ƙarfi ba sa jijjiguwa saboda hannun Maɗaukaki na Yaƙub, saboda Makiyayi, Dutsen Isra’ila, |
1502 | GEN 49:28 | Dukan waɗannan su ne kabilu goma sha biyu na Isra’ila, kuma abin da mahaifinsu ya faɗa musu ke nan sa’ad da ya albarkace su, yana ba kowane albarkar da ta dace da shi. |
1504 | GEN 49:30 | kogon da yake cikin filin Makfela, kusa da Mamre a Kan’ana, wanda Ibrahim ya saya tare da filin, yă zama makabarta daga Efron mutumin Hitti. |
1511 | GEN 50:4 | Sa’ad da kwanakin makoki suka wuce, sai Yusuf ya ce wa iyalin gidan Fir’auna, “In na sami tagomashi a idanunku, ku yi magana da Fir’auna domina. Ku faɗa masa, |
1514 | GEN 50:7 | Saboda haka Yusuf ya haura don yă binne mahaifinsa. Dukan hafsoshin Fir’auna suka yi masa rakiya tare da manyan mutanen gidan Fir’auna, da kuma dukan manyan mutanen Masar |
1562 | EXO 2:7 | Sai ’yar’uwarsa ta tambayi ’yar Fir’auna, ta ce, “In tafi in samo ɗaya daga cikin matan Ibraniyawa tă yi miki renon yaron?” |
1565 | EXO 2:10 | Sa’ad da ya yi girma, sai ta kawo shi wajen ’yar Fir’auna, ya kuwa zama ɗanta, ta kuma ba shi suna Musa, tana cewa, “Na tsamo shi daga ruwa.” |
1568 | EXO 2:13 | Kashegari ya fita, sai ya ga Ibraniyawa biyu suna faɗa. Ya tambayi mai laifin ya ce, “Don me kake bugun ɗan’uwanka, mutumin Ibraniyawa?” |
1570 | EXO 2:15 | Da Fir’auna ya ji wannan, sai ya yi ƙoƙari yă kashe Musa, amma Musa ya gudu daga wajen Fir’auna, ya tafi ƙasar Midiyan inda ya zauna kusa da wata rijiya. |
1580 | EXO 2:25 | Sai Allah ya dubi Isra’ilawa, ya kuma damu da su. |
1588 | EXO 3:8 | Saboda haka na sauko domin in cece su daga hannun Masarawa, in kuma fitar da su daga ƙasar Masar, in kai su ƙasa mai kyau mai fāɗi, ƙasa mai zub da madara da zuma, inda Kan’aniyawa, Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa suke. |
1591 | EXO 3:11 | Amma Musa ya ce wa Allah, “Wane ni in tafi wurin Fir’auna, in kuma fitar da Isra’ilawa daga Masar?” |
1595 | EXO 3:15 | Allah ya kuma ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Ubangiji, Allah na kakanninka, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub, ya aiko ni wurinku.’ Wannan shi ne sunana har abada, sunan da za a tuna da ni daga tsara zuwa tsara ke nan. |
1596 | EXO 3:16 | “Tafi ka tattara dattawan Isra’ila, ka ce musu, ‘Ubangiji, Allah na kakanninku, Allah na Ibrahim, Ishaku da Yaƙub, ya bayyana a gare ni ya ce, Na lura da ku, na kuma ga abubuwan da ake yi muku a Masar. |
1597 | EXO 3:17 | Na kuma yi alkawari, zan fitar da ku daga azabarku a Masar zuwa ƙasar Kan’aniyawa, Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa, ƙasa mai zub da madara da zuma.’ |
1598 | EXO 3:18 | “Dattawan Isra’ila za su saurare ka. Sa’an nan da kai da dattawan Isra’ila, za ku tafi wurin sarkin Masar, ku ce masa, ‘Ubangiji, Allah na Ibraniyawa, ya sadu da mu. Bari mu yi tafiyar kwana uku zuwa cikin hamada domin mu yi hadaya wa Ubangiji Allahnmu.’ |
1624 | EXO 4:22 | Sa’an nan ka gaya wa Fir’auna, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce; Isra’ila shi ne ɗan farina, |
1631 | EXO 4:29 | Musa da Haruna suka tattara dukan dattawan Isra’ilawa, |
1643 | EXO 5:10 | Sai shugabannin masu aikin gandu suka fita suka gaya wa mutanen Isra’ila, “Ga abin da Fir’auna ya ce, ‘Ba zan ƙara ba ku tattaka ba. |
1653 | EXO 5:20 | Da suka bar Fir’auna, sai suka sadu da Musa da Haruna suna jira su sadu da su, |
1656 | EXO 5:23 | Gama tun da na tafi wurin Fir’auna, na yi masa magana da sunanka, sai ya fara gasa wa mutanen nan azaba, ba ka kuma ceci mutanenka.” |
1660 | EXO 6:4 | Na kuma kafa alkawari da su don in ba su ƙasar Kan’ana, inda suka yi zaman baƙunci. |
1661 | EXO 6:5 | Ban da haka ma, na ji nishe-nishen Isra’ilawa, waɗanda Masarawa suka bautar, na kuma tuna da alkawarina. |
1662 | EXO 6:6 | “Saboda haka, ka ce wa Isra’ilawa, ‘Ni ne Ubangiji, zan kuma fitar da ku daga bauta ta Masarawa. Zan ’yantar da ku daga zama bayinsu, da ƙarfina zan fanshe ku, in kawo hukunci mai zafi a kansu, don in cece ku. |
1687 | EXO 7:1 | Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Duba, na maishe ka kamar Allah ga Fir’auna, ɗan’uwanka Haruna kuma zai zama annabinka. |
1688 | EXO 7:2 | Za ka faɗi kome da na umarce ka, ɗan’uwanka Haruna kuwa zai faɗa wa Fir’auna, yă bar Isra’ilawa su fita daga ƙasarsa. |
1689 | EXO 7:3 | Amma zan taurare zuciyar Fir’auna, kuma ko da na ninka mu’ujizai da kuma alamu a Masar, |
1696 | EXO 7:10 | Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna, suka yi yadda Ubangiji ya umarce su. Haruna ya jefa sandansa ƙasa, a gaban Fir’auna da bayinsa, sai sandan ya zama maciji. |
1712 | EXO 7:26 | Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka je wurin Fir’auna, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka bar mutanena su tafi domin su yi mini sujada. |
1720 | EXO 8:5 | Musa ya ce wa Fir’auna, “Na ba ka dama ka ba da lokacin da zan yi addu’a dominka da kuma bayinka da mutanenka, gidajenku kuwa za su rabu da kwaɗi, amma ban da waɗanda suke cikin Nilu.” |
1723 | EXO 8:8 | Bayan Musa da Haruna sun bar Fir’auna, Sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji saboda kwaɗin da ya kawo a bisa Fir’auna. |
1730 | EXO 8:15 | Sai bokaye suka ce wa Fir’auna, “Wannan fa da hannun Allah a ciki.” Amma zuciyar Fir’auna ta taurare, bai kuwa saurara ba, kamar dai yadda Ubangiji ya riga ya faɗa. |
1741 | EXO 8:26 | Sa’an nan Musa ya rabu da Fir’auna, ya kuma yi addu’a ga Ubangiji, |
1753 | EXO 9:10 | Sai suka ɗibi tokar matoya, suka tsaya a gaban Fir’auna, Musa ya watsa ta a iska, sai marurai masu zafi suka fiffito bisa mutane da dabbobi. |
1755 | EXO 9:12 | Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna, bai kuwa saurare Musa da Haruna ba kamar yadda Ubangiji ya riga ya ce wa Musa. |
1756 | EXO 9:13 | Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe, ka sadu da Fir’auna, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Ibraniyawa ya ce, Ka bar mutanena su tafi don su yi mini sujada, |
1776 | EXO 9:33 | Sai Musa ya tashi daga gaban Fir’auna, ya fita daga birni. Da ya miƙa hannuwansa ta wajen Ubangiji, sai tsawa da ƙanƙara suka tsaya, kwararowar ruwa kuma ta ɗauke. |
1779 | EXO 10:1 | Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Je wurin Fir’auna, gama na riga na taurare zuciyarsa da kuma zukatan fadawansa domin in aikata waɗannan mu’ujizai nawa a tsakiyarsu, |
1798 | EXO 10:20 | Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna, bai kuwa bar Isra’ilawa suka tafi ba. |