47 | GEN 2:16 | Ubangiji Allah ya umarci mutumin ya ce, “Kana da ’yanci ka ci daga kowane itace a cikin lambun, |
296 | GEN 11:29 | Abram da Nahor suka yi aure. Sunan matar Abram, Saira ne, sunan matar Nahor kuwa Milka; ita ’yar Haran ce, mahaifin Milka da Iska. |
489 | GEN 19:31 | Wata rana ’yarsa babba ta ce wa ƙanuwarta, “Mahaifinmu ya tsufa, kuma babu wani mutum kusa a nan da zai yi mana ciki mu haifi ’ya’ya; yadda al’ada take a ko’ina a duniya. |
491 | GEN 19:33 | A wannan dare, suka sa mahaifinsu ya sha ruwan inabi, ’yar farin ta shiga ta kwana da shi. Shi kuwa bai san sa’ad da ta kwanta ko sa’ad da ta tashi ba. |
492 | GEN 19:34 | Kashegari, ’yar farin ta ce wa ƙanuwar, “Jiya da dare na kwana da mahaifina. Bari mu sa yă sha ruwan inabi kuma yau da dare, ke ma ki shiga ki kwana da shi, domin kada zuriyar mahaifinmu ta ƙare.” |
495 | GEN 19:37 | ’Yar farin ta haifi ɗa, ta kuma ba shi suna Mowab, shi ne mahaifin Mowabawa a yau. |
496 | GEN 19:38 | ’Yar ƙaramar ma ta haifi ɗa, ta kuwa ba shi suna Ben-Ammi, shi ne mahaifin Ammonawa a yau. |
508 | GEN 20:12 | Ban da haka, tabbatacce ita ’yar’uwata ce, ’yar mahaifina, ko da yake ba daga uwata ba, ta kuma zama matata. |
542 | GEN 21:28 | Ibrahim ya ware ’yan raguna bakwai daga cikin garke, |
543 | GEN 21:29 | sai Abimelek ya ce wa Ibrahim, “Mene ne ma’anar ’yan raguna bakwai da ka keɓe?” |
544 | GEN 21:30 | Ibrahim ya amsa ya ce, “Ka karɓi waɗannan ’yan tumaki bakwai daga hannuna a matsayin shaida cewa ni ne na haƙa wannan rijiya.” |
588 | GEN 23:16 | Ibrahim ya yarda da sharuɗan Efron, sai ya auna masa farashin da ya faɗa a kunnuwan Hittiyawa, shekel ɗari huɗu na azurfa, bisa ga ma’aunin da ’yan kasuwa suke amfani da shi a lokacin. |
595 | GEN 24:3 | Ina so ka rantse da sunan Ubangiji Allah na sama da ƙasa, cewa ba za ka samo wa ɗana mata daga ’yan matan Kan’aniyawa, waɗanda nake zama cikinsu ba. |
607 | GEN 24:15 | Kafin ya gama addu’a, sai Rebeka ta fito da tulu a kafaɗarta. Ita ’yar Betuwel ɗan Milka, matar Nahor, ɗan’uwan Ibrahim. |
615 | GEN 24:23 | Sa’an nan ya tambaye ta ya ce, “Ke ’yar wace ce? Ina roƙonki ki faɗa mini, akwai wuri a gidan mahaifinki da za mu kwana?” |
616 | GEN 24:24 | Sai ta ce masa, “Ni ’yar Betuwel ce ɗan da Milka ta haifa wa Nahor.” |
639 | GEN 24:47 | “Na tambaye ta, ‘Ke ’yar wane ne?’ “Ta ce, ‘’Yar Betuwel ɗan Nahor, wanda Milka ta haifa masa.’ “Sai na sa mata zobe a hancinta, woroworo kuma a hannuwata, |
679 | GEN 25:20 | Ishaku yana da shekara arba’in sa’ad da ya auri Rebeka ’yar Betuwel, mutumin Aram, daga Faddan Aram, ’yar’uwar Laban mutumin Aram. |
683 | GEN 25:24 | Da lokaci ya yi da za tă haihu, sai ga ’yan biyu maza a mahaifarta. |
727 | GEN 26:34 | Sa’ad da Yaƙub ya kai shekaru arba’in da haihuwa, sai ya auri Yudit ’yar Beyeri mutumin Hitti, da kuma Basemat ’yar Elon mutumin Hitti. |
783 | GEN 28:9 | saboda haka sai ya tafi wurin Ishmayel ya auri Mahalat, ’yar’uwar Nebayiwot da kuma ’yar Ishmayel ɗan Ibrahim, ban da matan da yake da su. |
802 | GEN 29:6 | Sa’an nan Yaƙub ya tambaye su, “Yana nan lafiya?” Suka ce, “I, yana lafiya, ga ma ’yarsa Rahila tafe da tumaki.” |
806 | GEN 29:10 | Sa’ad da Yaƙub ya ga Rahila ’yar Laban, ɗan’uwan mahaifiyarsa, da tumakin Laban, sai ya tafi ya gungurar da dutsen daga bakin rijiyar, ya kuma shayar da tumakin kawunsa. |
814 | GEN 29:18 | Yaƙub ya ƙaunaci Rahila, sai ya ce, “Zan yi maka aiki na shekaru bakwai domin ƙaramar ’yarka Rahila.” |
816 | GEN 29:20 | Saboda haka Yaƙub ya yi bauta shekaru bakwai domin a ba shi Rahila, amma shekarun suka zama kamar ’yan kwanaki ne kawai gare shi saboda ƙaunar da yake mata. |
819 | GEN 29:23 | Amma da yamma ta yi, sai ya ɗauki ’yarsa Liyatu ya ba da ita ga Yaƙub, sai Yaƙub ya kwana da ita. |
820 | GEN 29:24 | Laban kuma ya ba da baranyarsa Zilfa wa ’yarsa tă zama mai hidimarta. |
822 | GEN 29:26 | Laban ya amsa, “Ba al’adarmu ba ce a nan a ba da ’ya ƙarama aure kafin ’yar fari. |
823 | GEN 29:27 | Ka gama makon amaryanci na ’yar nan; sa’an nan za mu ba ka ƙaramar ita ma, don ƙarin waɗansu shekaru bakwai na aiki.” |
824 | GEN 29:28 | Haka kuwa Yaƙub ya yi. Ya gama mako guda da Liyatu, sa’an nan Laban ya ba shi ’yarsa Rahila tă zama matarsa. |
825 | GEN 29:29 | Laban ya ba da baranyarsa Bilha wa ’yarsa Rahila ta zama mai hidimarta. |
852 | GEN 30:21 | Daga baya ta haifi ’ya ta kuwa ba ta suna Dina. |
982 | GEN 34:1 | To, Dina, ’yar da Liyatu ta haifa wa Yaƙub, ta je ta ziyarci matan ƙasar. |
984 | GEN 34:3 | Zuciyarsa kuwa ta damu da son Dina ’yar Yaƙub, ya kuwa ƙaunaci yarinyar, ya yi mata magana a hankali. |
986 | GEN 34:5 | Sa’ad da Yaƙub ya ji cewa an ɓata ’yarsa Dina, sai ya yi shiru game da batun sai ’ya’yansa maza sun dawo gida, gama ’ya’yansa suna a jeji tare da dabbobinsa suna kiwo. |
988 | GEN 34:7 | Da ’ya’yan Yaƙub maza suka dawo daga jeji sai suka ji labarin. Abin kuwa ya zafe su ƙwarai, don Shekem ya jawo abin kunya wa jama’ar Isra’ila ta wurin kwana da ’yar Yaƙub, don bai kamata wannan abu yă faru ba. |
1000 | GEN 34:19 | Saurayin wanda aka fi girmamawa a cikin dukan gidan mahaifinsa, bai ɓata lokaci a yin abin da suka ce ba, domin ya ji daɗin ’yar Yaƙub. |
1043 | GEN 36:2 | Isuwa ya ɗauko matansa daga cikin matan Kan’ana, ya ɗauko Ada ’yar Elon mutumin Hitti, da Oholibama ’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon Bahiwiye |
1044 | GEN 36:3 | ya kuma auri Basemat ’yar Ishmayel wadda take ’yar’uwar Nebayiwot. |
1055 | GEN 36:14 | ’Ya’yan Oholibama maza ’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon, matar Isuwa, waɗanda ta haifa wa Isuwa su ne, Yewush, Yalam da Kora. |
1059 | GEN 36:18 | ’Ya’yan Oholibama maza matar Isuwa, Shugabannin su ne; Yewush, Yalam da Kora. Waɗannan su ne manya da suka fito daga dangin Oholibama ’yar Ana matar Isuwa. |
1066 | GEN 36:25 | ’Ya’yan Ana su ne, Dishon da Oholibama ’yar Ana. |
1080 | GEN 36:39 | Sa’ad da Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya rasu, Hadad ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Fau, kuma sunan matarsa Mehetabel ce ’yar Matired, jikanyar Me-Zahab. |
1120 | GEN 37:36 | Ana cikin haka, Midiyawa suka sayar da Yusuf a Masar wa Fotifar, ɗaya daga cikin shugabannin ’yan gadin fadar Fir’auna. |
1122 | GEN 38:2 | A can Yahuda ya sadu da ’yar wani Bakan’ane, mai suna Shuwa. Ya aure ta, ya kuma kwana da ita; |
1132 | GEN 38:12 | Bayan an daɗe sai matar Yahuda, ’yar Shuwa ta rasu. Sa’ad da Yahuda ya gama makoki, sai ya haura zuwa Timna, zuwa wurin mutanen da suke askin tumakinsa, abokinsa Hira mutumin Adullam kuwa ya tafi tare da shi. |
1147 | GEN 38:27 | Sa’ad da lokaci ya yi da za tă haihu, ashe, tagwaye ’yan maza ne suke cikinta. |
1170 | GEN 39:20 | Maigidan Yusuf ya ɗauke shi ya sa a kurkuku, wurin da ake tsare ’yan kurkukun sarki. Amma yayinda Yusuf yake can a cikin kurkuku, |
1241 | GEN 41:45 | Fir’auna ya ba wa Yusuf suna Zafenat-Faneya, ya kuma ba shi Asenat ’yar Fotifera firist na On, ta zama matarsa. Yusuf kuwa ya zaga dukan ƙasar Masar. |
1246 | GEN 41:50 | Kafin shekarun yunwa su zo, Asenat ’yar Fotifera, firist na On, ta haifa wa Yusuf ’ya’ya maza biyu. |
1262 | GEN 42:9 | Sa’an nan ya tuna da mafarkansa game da su, ya kuma ce musu, “Ku ’yan leƙen asiri ne! Kun zo don ku leƙi asirin ƙasar ku ga inda ba ta da tsaro.” |
1264 | GEN 42:11 | Mu duka ’ya’yan mutum ɗaya maza ne. Bayinka mutane ne masu gaskiya, ba ’yan leƙen asiri ba ne.” |
1267 | GEN 42:14 | Yusuf ya ce musu, “Daidai ne yadda na faɗa muku. Ku ’yan leƙen asiri ne! |
1269 | GEN 42:16 | Ku aiki ɗaya daga cikinku yă kawo ɗan’uwanku; za a sa sauranku a kurkuku, saboda a gwada maganarku a ga ko gaskiya ce kuke faɗi. In ba haka ba, to, da ran Fir’auna, ku ’yan leƙen asiri ne!” |
1283 | GEN 42:30 | “Mutumin da yake shugaba a ƙasar ya yi mana matsananciyar magana, ya kuma ɗauke mu tamƙar ’yan leƙen asirin ƙasa. |
1284 | GEN 42:31 | Amma muka ce masa, ‘Mu masu gaskiya ne; mu ba ’yan leƙen asiri ba ne. |
1287 | GEN 42:34 | Amma ku kawo mini ƙaramin ɗan’uwanku domin in san cewa ku ba ’yan leƙen asiri ba ne, amma mutane ne masu gaskiya. Sa’an nan zan mayar muku da ɗan’uwanku, ku kuma iya yin sana’a a ƙasar.’ ” |
1302 | GEN 43:11 | Sa’an nan mahaifinsu Isra’ila ya ce musu, “In dole ne a yi haka, to, sai ku yi. Ku sa waɗansu amfani mafi kyau na ƙasar a buhunanku, ku ɗauka zuwa wurin mutumin a matsayin kyauta, da ɗan man ƙanshi na shafawa, da kuma ’yar zuma, da kayan yaji, da ƙaro, da tsabar citta da kuma almon. |
1335 | GEN 44:10 | Sai ya ce, “To, shi ke nan, bari yă zama yadda kuka faɗa. Duk wanda aka same shi da kwaf na azurfan zai zama bawana, sauran kuwa za su ’yantu daga zargin.” |
1402 | GEN 46:15 | Waɗannan su ne ’ya’yan Liyatu maza da ta haifa wa Yaƙub a Faddan Aram, ban da ’yarsa Dina. ’Ya’yansa maza da mata duka, mutum talatin da uku ne. |
1405 | GEN 46:18 | Waɗannan su ne ’ya’yan da Zilfa ta haifa wa Yaƙub, ita ce Laban ya ba wa ’yarsa Liyatu. ’Ya’yan duka, su sha shida ne. |
1407 | GEN 46:20 | A Masar, Asenat ’yar Fotifera, firist na On ta haifi Manasse da Efraim wa Yusuf. |
1412 | GEN 46:25 | Waɗannan su ne ’ya’ya mazan da Bilha ta haifa wa Yaƙub, ita ce Laban ya ba wa ’yarsa Rahila. ’Ya’yan suka su bakwai ne. |
1459 | GEN 48:7 | Yayinda nake dawowa daga Faddan Aram, cikin baƙin cikina Rahila ta rasu a ƙasar Kan’ana yayinda muke kan hanya, ’yar rata daga Efrata. Saboda haka na binne ta a can kusa da hanya zuwa Efrata” (wato, Betlehem). |
1560 | EXO 2:5 | Sai ’yar Fir’auna ta gangara zuwa kogi domin tă yi wanka, bayinta kuwa suna tafiya a bakin kogi. Sai ta ga kwandon a ciyawa, ta aiki ɗaya daga cikin masu hidimarta tă ɗauko mata. |
1562 | EXO 2:7 | Sai ’yar’uwarsa ta tambayi ’yar Fir’auna, ta ce, “In tafi in samo ɗaya daga cikin matan Ibraniyawa tă yi miki renon yaron?” |
1565 | EXO 2:10 | Sa’ad da ya yi girma, sai ta kawo shi wajen ’yar Fir’auna, ya kuwa zama ɗanta, ta kuma ba shi suna Musa, tana cewa, “Na tsamo shi daga ruwa.” |
1573 | EXO 2:18 | Da ’yan matan suka komo wurin Reyuwel mahaifinsu, sai ya tambaye su ya ce, “Yaya kuka dawo da wuri yau?” |
1575 | EXO 2:20 | Ya tambayi ’yan matansa, “To ina yake? Don me kuka bar shi a can? A gayyace shi, yă zo, yă ci wani abu.” |
1576 | EXO 2:21 | Musa ya yarda yă zauna da mutumin wanda ya ba da ’yarsa Ziffora aure da Musa. |
1662 | EXO 6:6 | “Saboda haka, ka ce wa Isra’ilawa, ‘Ni ne Ubangiji, zan kuma fitar da ku daga bauta ta Masarawa. Zan ’yantar da ku daga zama bayinsu, da ƙarfina zan fanshe ku, in kawo hukunci mai zafi a kansu, don in cece ku. |
1679 | EXO 6:23 | Haruna ya auri Elisheba, ’yar Amminadab, ’yar’uwar Nashon, sai ta haifa masa Nadab da Abihu, Eleyazar da Itamar. |
1681 | EXO 6:25 | Eleyazar ɗan Haruna, ya auri ɗaya daga cikin ’yan matan Futiyel, sai ta haifa masa Finehas. Waɗannan su ne shugabannin iyalan Lawi, dangi, dangi. |
1812 | EXO 11:5 | Kowane ɗan fari, namiji, a Masar zai mutu, daga kan ɗan fari na Fir’auna wanda zai ci gadon sarauta, har zuwa kan ɗan fari na baiwa, wadda take niƙa, da kuma dukan ’yan farin shanu. |
2080 | EXO 21:2 | “In ka sayi mutumin Ibraniyawa a matsayin bawa, zai bauta maka shekara shida. Amma a shekara ta bakwai, za ka ’yantar da shi, yă tafi ’yantacce, ba tare da ya biya kome ba. |
2081 | EXO 21:3 | In ya zo shi kaɗai, zai tafi ’yantacce shi kaɗai; amma in yana da mata a lokacin da ya zo, za tă tafi tare da shi. |
2085 | EXO 21:7 | “In mutum ya sayar da ’yarsa a matsayin baiwa, ba za a ’yantar da ita kamar bawa ba. |
2087 | EXO 21:9 | In ya zaɓe ta domin ɗansa, dole yă ba ta duk damar da ’ya ta mace take da shi. |
2104 | EXO 21:26 | “In mutum ya bugi bawa ko baiwa a ido, har idon ya lalace, dole yă ’yantar da shi ko ita, maimakon ido. |
2105 | EXO 21:27 | In kuma ya fangare haƙorin bawa ko baiwa, dole yă ’yantar da bawan ko baiwar, a maimakon haƙorin. |
2336 | EXO 28:42 | “Ka yi ’yan wandunan ciki na lilin don su rufe tsiraicinsu, tsayinsu zai kama daga kwankwaso zuwa cinya. |
2375 | EXO 29:38 | “Ga abin da za ka miƙa a bisa bagaden kowace rana. ’Yan raguna biyu masu shekara ɗaya-ɗaya. |
2442 | EXO 32:3 | Saboda haka dukan mutane suka tuttuɓe ’yan kunnensu suka kawo wa Haruna. |
2513 | EXO 34:16 | Kada ku auro wa ’ya’yanku maza ’yan matansu, waɗanda suke yi wa alloli sujada, har su sa ’ya’yanku su bi allolinsu. |
2554 | EXO 35:22 | Duk waɗanda suke da niyya, maza da mata, gaba ɗaya, suka kawo kayan ado na zinariya na kowane iri. ’Yan kunne, da ƙawane, da mundaye, da kayayyakin zinariya iri-iri. Dukansu suka miƙa zinariyarsu a matsayin hadaya ga Ubangiji. |
2760 | LEV 1:14 | “ ‘In hadaya ga Ubangiji ɗin, hadaya ta ƙonawa ta tsuntsaye ce, zai miƙa kurciya ko ’yar tattabara. |
2780 | LEV 3:1 | “ ‘In hadayar wani mutum, hadaya ta salama ce, ya kuma miƙa ’yar dabba daga garke, ko namiji ko ta mace ce, sai yă miƙa dabbar da ba ta da lahani a gaban Ubangiji. |
2828 | LEV 4:32 | “ ‘Idan kuwa daga cikin ’yan tumaki zai ba da hadayarsa, sai ya kawo ’yar tunkiya marar lahani. |
2920 | LEV 8:2 | “Kawo Haruna da ’ya’yansa maza, ka ɗauki rigunansu, man keɓewa, bijimi domin hadaya don zunubi, ’yan raguna biyu da kuma kwandon da yake da burodi marar yisti, |
3050 | LEV 12:5 | In ta haifi ’ya ta mace ce, makoni biyu macen za tă ƙazantu kamar yadda takan kasance a lokacin al’adarta. Sa’an nan dole tă jira kwana sittin don a tsabtacce ta daga zub da jininta. |
3051 | LEV 12:6 | “ ‘Sa’ad da kwanakin tsabtaccewarta don ɗa namiji ko ’ya ta mace suka cika, sai ta kawo ɗan rago bana ɗaya wa firist a bakin ƙofar Tentin Sujada don hadaya ta ƙonawa da tattabara ko kurciya na hadaya don zunubi. |
3052 | LEV 12:7 | Firist zai miƙa su a gaban Ubangiji don yă yi kafara dominta, sa’an nan tă tsabtacce daga zub da jininta. “ ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi domin macen da ta haifi ɗa namiji ko ’ya ta mace. |
3122 | LEV 14:10 | “A rana ta takwas dole yă kawo ɗan rago da ’yar tunkiya bana ɗaya, kowane marar lahani, tare da rabin garwan gari mai laushi haɗe da mai domin hadaya ta gari, da kuma moɗa ɗaya na mai. |
3261 | LEV 18:9 | “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar’uwarka, ko ’yar mahaifinka ko ’yar mahaifiyarka, ko an haife ta a gida ɗaya da kai ko kuwa a wani wuri dabam. |
3262 | LEV 18:10 | “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar ɗanka ko ’yar ’yarka, wannan zai ƙasƙantar da kai. |
3263 | LEV 18:11 | “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar matar mahaifinka wadda aka haifa wa mahaifinka; ita ’yar’uwarka ce. |
3269 | LEV 18:17 | “ ‘Kada ka yi jima’i da mace da kuma ’yarta. Kada ka yi jima’i da ’yar ɗanta ko ’yar ’yarta; su danginta ne na kusa. Wannan mugun abu ne. |
3302 | LEV 19:20 | “ ‘In wani ya kwana da mace wadda take baiwa, wadda aka yi wa wani alkawari amma bai fanshe ta ba, ko kuwa ba a ’yantar da ita ba, dole a yi hukuncin da ya dace. Duk da haka ba za a kashe su ba, domin ba a ’yantar da ita ba. |
3311 | LEV 19:29 | “ ‘Kada ka ƙasƙantar da ’yarka ta wurin mai da ita karuwa, in ba haka ba ƙasar za tă juya ga karuwanci tă kuma cika da mugunta. |
3333 | LEV 20:14 | “ ‘In mutum ya auri ’ya da mahaifiyarta, mugun abu ne. Da shi da su, dole a ƙone su da wuta, saboda kada mugun abu yă kasance a cikinku. |