1357 | GEN 44:32 | Gama ni baranka na ɗauki lamunin saurayin a wurin mahaifinsa da cewa, ‘In ban komo maka da shi ba, sai alhakinsa yă zauna a kaina a gaban mahaifina, dukan raina!’ |
1649 | EXO 5:16 | Ba a ba wa bayinka tattaka, duk da haka ana ce mana, ‘Ku yi tubula!’ Ana wa bayinka dūka, amma fa laifin na mutanenka ne.” |
3098 | LEV 13:45 | “Mutum mai wannan cuta mai yaɗuwa dole yă sa yagaggun riguna, yă kuma bar gashin kansa ba gyara, yă rufe sashe ƙasa na fuskarsa, sa’an nan yă riga cewa, ‘Marar tsarki! Marar tsarki!’ |
4038 | NUM 11:13 | Ina ne zan sami nama in waɗannan mutane? Sun dinga yin mini kuka suna cewa ‘Ka ba mu nama mu ci!’ |
4046 | NUM 11:21 | Amma Musa ya ce, “Ga ni a cikin mutane dubu ɗari shida tafe tare da ni, kana kuma cewa, ‘Zan ba su nama su ci har wata guda cur!’ |
4440 | NUM 23:23 | Ba wata maitar da za tă ci Yaƙub, ba sihiri da zai cuci Isra’ila. Yanzu za a ce game da Yaƙub da Isra’ila, ‘Duba abin da Allah ya yi!’ |
5839 | DEU 33:27 | Allah madawwami shi ne mafakarka, a ƙarƙashina kuma madawwamin hannuwa ne. Zai kore abokin gābanka a gabanka, yana cewa, ‘Ka hallaka shi!’ |
6771 | JDG 9:15 | “Itacen ƙaya ya ce wa itatuwan, ‘In da gaske ne kuke so ku naɗa ni sarkinku, ku zo ku sha inuwana; in ba haka ba, bari wuta ta fito daga itacen ƙaya ta cinye itacen al’ul na Lebanon!’ |
6785 | JDG 9:29 | Da a ce waɗannan mutane suna a ƙarƙashina mana! Da zan hamɓarar da shi. In ce wa Abimelek, ‘Ka tara dukan mayaƙanka!’ ” |
7538 | 1SA 14:28 | Sai wani soja ya gaya masa cewa, “Mahaifinka ya sa kowa ya yi rantsuwa cewa, ‘La’ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin fāɗuwar rana!’ Shi ya sa duk sojojin ba su da ƙarfi.” |
8745 | 1KI 1:25 | Yau ya gangara, ya kuma miƙa hadayun shanu, da shanun da ake kiwo a gida, da tumaki masu yawa. Ya gayyaci dukan ’ya’yan sarki maza, da shugaban mayaƙa, da kuma Abiyatar firist. A yanzu haka suna ci, suna sha, tare da shi, suna cewa, ‘Ran Sarki Adoniya yă daɗe!’ |
8754 | 1KI 1:34 | A can ku sa Zadok firist, da annabi Natan su shafe shi sarki a bisa Isra’ila. Ku busa ƙaho, ku kuma yi ihu, kuna cewa, ‘Ran Sarki Solomon yă daɗe!’ |
8767 | 1KI 1:47 | Yanzu haka, fadawa sun zo suna wa ranka yă daɗe, Sarki Dawuda, sam barka, suna cewa, ‘Bari Allahnka yă sa sunan Solomon yă zama sananne fiye da naka, bari kuma sarautarsa tă fi taka girma!’ Sarki kuwa ya rusuna, ya yi sujada a kan gadonsa |
8803 | 1KI 2:30 | Sai Benahiya ya shiga tentin Ubangiji ya ce wa Yowab, “Sarki ya ce, ‘Ka fita!’ ” Amma Yowab ya amsa ya ce, “A’a, a nan zan mutu.” Sai Benahiya ya ce wa sarki, “Ga yadda Yowab ya amsa mini.” |
9232 | 1KI 14:11 | Karnuka za su ci waɗanda suka mutu na Yerobowam a cikin birni, kuma tsuntsayen sararin sama za su cinye waɗanda suka mutu a jeji. Ni Ubangiji na faɗa!’ |
9473 | 1KI 21:19 | Ka ce masa, Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ba ka kashe mutum ka kuma ƙwace kayansa ba?’ Sa’an nan ka ce masa ga abin da Ubangiji ya ce, ‘A inda karnuka suka lashe jinin Nabot, karnuka za su lashe jininka, I, naka!’ ” |
9541 | 2KI 1:4 | Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ba za ka tashi daga inda kake kwance ba, ba shakka za ka mutu!’ ” Iliya ya yi kamar yadda Ubangiji ya umarce shi, sai ya tafi. |
9546 | 2KI 1:9 | Sai sarki ya aiki kaftin da sojojin hamsin wurin Iliya. Kaftin ya haura wajen Iliya, wanda yake zaune a kan tudu, ya ce masa, “Mutumin Allah, sarki ya ce, ‘Ka sauko, ka zo!’ ” |
9548 | 2KI 1:11 | Da jin haka sai sarki ya sāke aiken wani kaftin tare da waɗansu sojojinsa hamsin wurin Iliya. Kaftin ya ce wa Iliya, “Mutumin Allah, ga abin da sarki ya ce, ‘Ka sauko, nan take ka zo!’ ” |
10892 | 1CH 17:24 | saboda zai kahu kuma sunanka zai zama mai girma har abada. Sa’an nan mutane za su ce, ‘Ubangiji Maɗaukaki, Allah a bisa Isra’ila, Allahn Isra’ila ne!’ Kuma gidan bawanka Dawuda zai kahu a gabanka. |
12413 | NEH 6:7 | har ma ka naɗa annabawa su yi wannan shela game da kai a Urushalima, su ce, ‘Akwai sarki a Yahuda!’ To, wannan rahoto zai koma wurin sarki; saboda haka ka zo, mu tattauna wannan batu.” |
12806 | EST 6:9 | Sa’an nan, bari a ba da rigar da kuma dokin wa ɗaya daga cikin manyan sarakuna mafi kirki na sarki. Bari shi kuma yă sa wannan riga wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama, a kuma bi da shi a bisan doki ko’ina a titunan birni, ana shela a gabansa ana cewa, ‘Wannan shi ne abin da ake yin wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama!’ ” |
12911 | JOB 3:3 | “A hallaka ranar da aka haife ni, da kuma daren da aka ce, ‘An haifi jariri namiji!’ |
13308 | JOB 19:7 | “Ko da yake na yi kuka cewa, ‘An yi mini ba daidai ba!’ Ba a amsa mini ba; ko da yake na nemi taimako, ba a yi adalci ba. |
13422 | JOB 22:29 | Sa’ad da aka ƙasƙantar da mutane ka kuma ce, ‘A ɗaga su!’ Sa’an nan zai ceci masu tawali’u. |
17336 | PRO 30:15 | “Matsattsaku tana da ’ya’ya mata biyu. Suna kuka suna cewa, ‘Ba ni! Ba ni!’ “Akwai abubuwa uku da ba sa taɓa ƙoshi, guda huɗu ba sa taɓa cewa, ‘Ya isa!’ |
17337 | PRO 30:16 | Kabari, mahaifar da ba ta haihuwa, ƙasa, wadda ba ta taɓa ƙoshi da ruwa, da kuma wuta, wadda ba ta taɓa cewa ‘Ya isa!’ |
18114 | ISA 21:9 | Duba, ga wani mutum tafe a keken yaƙin tare da ƙungiyar dawakai. Ya kuma mayar da amsa, ‘Babilon ta fāɗi, ta fāɗi! Dukan siffofin allolinta kwance a ragargaje a ƙasa!’ ” |
18548 | ISA 41:27 | Ni ne na farkon da ya ce wa Sihiyona, ‘Duba, ga su nan!’ Na ba wa Urushalima saƙon labari mai daɗi. |
18581 | ISA 43:6 | Zan ce wa arewa, ‘Ku miƙa su!’ Ga kudu kuma, ‘Kada ku riƙe su.’ Kawo ’ya’yana maza daga nesa ’ya’yana mata kuma daga iyakar duniya, |
18676 | ISA 47:7 | Kika ce, ‘Zan ci gaba har abada, madawwamiyar sarauniya!’ Amma ba ki lura da waɗannan abubuwa ko ki yi la’akari a kan abin da zai faru ba. |
18971 | ISA 65:5 | suna cewa, ‘Ku tsaya a can; kada ku yi kusa da ni, gama na fi ku tsarki!’ Irin mutanen nan hayaƙi ne a hancina, wuta kuma da take cin gaba da ci dukan yini. |
18996 | ISA 66:5 | Ku ji maganar Ubangiji, ku da kuke rawar jiki ga maganarsa, “’Yan’uwanku da suke ƙinku, suna kuma ware ku saboda sunana, sun ce, ‘Bari a ɗaukaka Ubangiji, don mu ga farin cikinku!’ Duk da haka za su sha kunya. |
19054 | JER 2:20 | “Tun da daɗewa ka karya karkiyarka ka kuma tsintsinke sarƙoƙinka; sai ka ce, ‘Ba zan bauta maka ba!’ Tabbatacce, a kan kowane tudu mai tsayi da kuma a ƙarƙashin kowane ɗanyen itace ka kwanta kamar karuwa. |
19061 | JER 2:27 | Kuna ce wa itace, ‘Kai ne mahaifina,’ ga dutse kuma, ‘Kai ne ka haife ni.’ Sun juye mini bayansu ba fuskokinsu ba; duk da haka sa’ad da suna cikin wahala, sukan ce, ‘Zo ka cece mu!’ |
19101 | JER 4:5 | “Ku yi shela a Yahuda ku kuma furta a Urushalima ku ce, ‘Ku busa ƙaho a ko’ina a ƙasar!’ Ku tā da murya da ƙarfi ku ce, ‘Ku tattaru! Bari mu gudu zuwa birane masu katanga!’ |
19175 | JER 6:17 | Na naɗa muku masu tsaro a kanku na kuma ce, ‘Ku saurari karan ƙaho!’ Amma kuka ce, ‘Ba za mu saurara ba.’ |
19541 | JER 22:18 | Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, “Ba za su yi kuka dominsa ba, ‘Kaito, ɗan’uwana! Kaito, ’yar’uwata!’ Ba za su yi kuka dominsa ba, ‘Kaito, maigidana! Kaito, darajarsa!’ |
19544 | JER 22:21 | Na ja maka kunne sa’ad da kake zama lafiya, amma sai ka ce, ‘Ba zan saurara ba!’ Wannan halinka ne tun kana matashi; ba ka yi mini biyayya ba. |
19578 | JER 23:25 | “Na ji abin da annabawa suna cewa su da suke annabcin ƙarya a sunana. Suna cewa, ‘Na yi mafarki! Na yi mafarki!’ |
20083 | JER 44:4 | Sau da sau na aiki bayina annabawa, waɗanda suka ce, ‘Kada ku yi wannan abin ƙyama da na ƙi!’ |
20166 | JER 48:17 | Yi kuka saboda ita, dukanku mazaunan kewayenta, duk waɗanda suka san shahararta; ku ce, ‘Dubi yadda sandan sarauta mai iko ya karye, dubi yadda sanda mai daraja ya karye!’ |
22007 | DAN 7:5 | “A gabana kuma ga dabba ta biyu, wadda ta yi kamar beyar. Aka ɗaga ta a gefenta guda, tana kuwa da haƙarƙarai uku a bakinta a tsakanin haƙoranta. Aka faɗa mata, ‘Tashi ki cika cikinki da ɗanyen nama!’ |
22217 | HOS 4:15 | “Ko da yake kun yi zina, ya Isra’ila, kada Yahuda ya yi laifi. “Kada ku tafi Gilgal; kada ku haura zuwa Bet-Awen. Kuma kada ku rantse cewa, ‘Muddin Ubangiji yana a raye!’ |
22265 | HOS 8:2 | Isra’ila ta yi mini kuka, ‘Ya Allahnmu, mun yarda da kai!’ |
22896 | ZEP 3:7 | Na ce wa birnin, ‘Tabbatacce za ki ji tsorona ki kuma yarda da gyara!’ Ta haka ba za a datse wurin zamanki ba, ba kuwa dukan hukuncena za su hau bisa kansu ba. Amma har yanzu suna marmari su yi rashin gaskiya a duk abin da suke yi. |
22998 | ZEC 4:7 | “Kai mene ne, ya babban dutse? A gaban Zerubbabel za a rushe ka ka zama fili. Sa’an nan Zerubbabel yă kawo dutsen da ya fi kyau, a kuma yi ta sowa ana cewa, ‘Allah yă yi masa albarka! Allah yă yi masa albarka!’ ” |
23102 | ZEC 11:5 | Masu sayensu sun yanyanka su, suka kuwa tafi ba hukunci. Masu sayar da su sun ce, ‘Yabi Ubangiji, na yi arziki!’ Makiyayansu ma ba su ji tausayinsu ba. |
23163 | MAL 1:5 | Za ku ga wannan da idanunku ku kuma ce, ‘Ubangiji da girma yake, har gaba da iyakokin Isra’ila ma!’ |
23171 | MAL 1:13 | Kun kuma ce, ‘Mun gaji da irin wannan wahala!’ Kuna hura mini hancin reni,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Sa’ad da kuka kawo raunannu, gurguntattun dabbobi, ko kuma dabbobi masu fama da cuta, kuka kuma miƙa su hadaya, kuna gani zan karɓi wannan daga gare ku?” In ji Ubangiji. |
23325 | MAT 5:22 | Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da ɗan’uwansa, za a hukunta shi. Kuma duk wanda ya ce wa ɗan’uwansa ‘Raka,’za a kai shi gaban Majalisa. Amma duk wanda ya ce, ‘Kai wawa!’ Zai kasance a hatsarin shiga jahannama ta wuta. |
23408 | MAT 7:23 | Sa’an nan zan ce musu a fili, ‘Ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!’ |
23824 | MAT 18:28 | “Amma da wannan bawa ya fita, sai ya gamu da wani abokin bautarsa wanda yake binsa bashin dinari ɗari. Sai ya cafke shi, ya shaƙe shi a wuya yana cewa, ‘Biya ni abin da nake binka!’ |
24049 | MAT 24:23 | A lokacin in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko, ‘Ga shi can!’ Kada ku gaskata. |
24083 | MAT 25:6 | “Can tsakar dare, sai aka ji kira, ana cewa, ‘Ga ango nan! Ku fito, ku tarye shi!’ |
24088 | MAT 25:11 | “An jima can, sai ga sauran sun iso. Suka ce, ‘Ranka yă daɗe! Ranka yă daɗe! Ka buɗe mana ƙofa!’ |
24098 | MAT 25:21 | “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’ |
24100 | MAT 25:23 | “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’ |
24404 | MRK 4:12 | Saboda, “ ‘ko sun dinga duba, ba za su taɓa gane ba, kuma ko su dinga ji, ba za su taɓa fahimta ba, in ba haka ba, mai yiwuwa, su tuba, a gafarta musu!’ ” |
24807 | MRK 13:21 | A lokacin nan, in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko kuwa, ‘Duba, ga shi can!’ Kada ku gaskata. |
24823 | MRK 13:37 | Abin da na faɗa muku, na faɗa wa kowa. ‘Ku yi tsaro!’ ” |
25100 | LUK 3:6 | Dukan ’yan Adam kuwa za su ga ceton Allah!’ ” |
25445 | LUK 10:13 | “ ‘Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida!’ Ai, da a ce a Taya da Sidon ne aka yi ayyukan banmamaki da aka yi a cikinku, da tuni sun tuba, suna zama cikin rigar makoki da toka. |
25614 | LUK 13:27 | “Amma shi zai amma ya ce, ‘Ban san ku, ko inda kuka fito ba. Ku rabu da ni, dukan ku masu aikata mugunta!’ |
25620 | LUK 13:33 | Duk da haka, dole in ci gaba da aikin a yau, da kuma gobe, sa’an nan in ci gaba da yin haka kashegari kuma, gama tabbatacce, ba annabi da yakan mutu a bayan birnin Urushalima!’ |
25687 | LUK 15:30 | Amma da wannan ɗan naka, wanda ya ɓatar da dukiyarka a kan karuwai ya dawo, ka yanka masa ɗan saniya mai ƙiba!’ |
25743 | LUK 17:23 | Mutane za su ce muku, ‘Ga shi can!’ Ko kuma, ‘Ga shi nan!’ Kada ku yi hanzarin binsu. |
25825 | LUK 19:25 | “Suka ce, ‘Ranka yă daɗe, ai, yana da guda goma ko!’ |
25862 | LUK 20:14 | “Amma da ’yan hayan suka gan shi, sai suka tattauna zancen, suka ce, ‘Wannan shi ne magājin, mu kashe shi sa’an nan gādon zai zama namu!’ |
26033 | LUK 23:29 | Gama lokaci yana zuwa da za ku ce, ‘Masu albarka ne bakararru, wato, mata marasa haihuwa, da mahaihuwar da ba su taɓa haihuwa ba, da kuma mama da ba su taɓa shayar da nono ba!’ |
27225 | ACT 7:40 | Suka ce wa Haruna, ‘Ka yi mana allolin da za su yi mana jagora. Game da wannan Musa ɗin wanda ya fitar da mu daga Masar, ba mu san abin da ya faru da shi ba!’ |
27785 | ACT 22:13 | Ya tsaya kusa da ni ya ce, ‘Ɗan’uwa Shawulu, ka sami ganin garinka!’ A daidai lokacin kuwa na iya ganinsa. |
31072 | REV 18:10 | Don tsoron ganin azabarta za su tsaya daga nesa, su yi kuka suna cewa, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma. Ya ke Babilon, birni mai iko! Cikin sa’a guda hallakarki ta zo!’ |
31079 | REV 18:17 | Cikin sa’a guda irin wannan dukiya mai yawa ta hallaka!’ “Duk matuƙan jirgin ruwa, da dukan waɗanda suke tafiya a jirgin ruwa, ma’aikatanta, da duk masu samun abin zama gari daga teku za su tsaya daga nesa. |
31081 | REV 18:19 | Za su zuba ƙura a kawunansu, da kuka da makoki za su yi ta kururuwa, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma, inda dukan waɗanda suke da jiragen ruwa a teku suka arzuta da ɗumbun dukiyarsa! Cikin sa’a ɗaya ta hallaka!’ |
31095 | REV 19:9 | Sai mala’ikan ya ce mini, “Rubuta, ‘Masu albarka ne waɗanda aka gayyace su zuwa bikin auren Ɗan Ragon!’ ” Sai ya ƙara da cewa, “Waɗannan su ne kalmomin Allah da gaske.” |