8720 | 2SA 24:25 | Dawuda ya gina wa Ubangiji bagade a wurin, ya kuma miƙa masa hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta salama. Sa’an nan Ubangiji ya amsa addu’o’in a madadin ƙasar, aka kuma kawar wa Isra’ila annoban. |
9042 | 1KI 8:54 | Da Solomon ya gama dukan waɗannan addu’o’i da roƙe-roƙe ga Ubangiji, sai ya tashi daga gaban bagaden Ubangiji, inda ya durƙusa da hannuwansa a buɗe waje sama. |
11327 | 2CH 6:40 | “Yanzu, Allahna, bari idanunka su buɗu kunnuwanka kuma su saurara ga addu’o’in da ake miƙa a wannan wuri. |
11344 | 2CH 7:15 | Yanzu, idanuna za su buɗu, kunnuwata kuma za su saurara ga addu’o’in da aka miƙa a wannan wuri. |
12974 | JOB 5:19 | Zai cece ka daga bala’o’i guda shida; har bakwai ma ba abin da zai same ka. |
14443 | PSA 35:13 | Duk da haka sa’ad da suke ciwo, na sanya rigar makoki na ƙasƙantar da kaina da azumi. Sa’ad da aka mayar mini da addu’o’i babu amsa, |
15075 | PSA 72:20 | Wannan ya kammala addu’o’in Dawuda ɗan Yesse. |
15261 | PSA 80:5 | Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, har yaushe fushinka zai yi ta ƙuna a kan addu’o’in mutanenka? |
15830 | PSA 109:7 | Sa’ad da aka yi masa shari’a, bari a same shi da laifi, bari kuma addu’o’insa su hukunta shi. |
16540 | PRO 3:15 | Ta fi lu’ulu’u daraja; ba a kwatanta abin da ka fi sha’awa da ita. |
16683 | PRO 8:11 | gama hikima ta fi lu’ulu’ai daraja, kuma ba abin da kake sha’awa da za a kwatanta da ita. |
17039 | PRO 20:15 | Zinariya akwai ta, lu’ulu’u kuma ga shi a yalwace, amma leɓunan da suke magana da sani suna da wuyan samu kamar duwatsu masu daraja. |
17739 | ISA 1:15 | Sa’ad da kuka ɗaga hannuwanku wajen yin addu’a, zan ɓoye fuskata daga gare ku; ko da kun miƙa addu’o’i masu yawa, ba zan kasa kunne ba. Hannuwanku sun cika da jini! |
22074 | DAN 9:17 | “Yanzu, ya Allahnmu, ka ji addu’o’i da koke-koken bayinka. Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka duba da rahama wurinka mai tsarki da ya zama kango. |
22090 | DAN 10:6 | Jikinsa kamar lu’ulu’u yake, fuskarsa kuma kamar walƙiya, idanunsa kamar harshen wuta, hannuwansa da ƙafafunsa kamar gogaggiyar tagulla, muryarsa kuma kamar amon babban taron jama’a. |
23084 | ZEC 9:16 | Ubangiji Allahnsu zai cece su a wannan rana gama su mutanensa ne da kuma garkensa. Za su haska a cikin ƙasarsa kamar lu’ulu’u a rawani. |
23653 | MAT 13:45 | “Har wa yau dai, mulkin sama yana kama da ɗan kasuwa mai neman lu’ulu’ai masu kyau. |
28008 | ROM 1:10 | cikin addu’o’ina a kowane lokaci; ina kuma addu’a cewa a ƙarshe in Allah ya yarda hanya za tă buɗe mini in zo wurinku. |
28879 | 2CO 1:11 | yayinda kuke taimakonmu ta wurin addu’o’inku. Mutane da yawa kuwa za su yi godiya ta dalilinmu, saboda albarkar da aka yi mana, ta amsa addu’o’i masu yawa. |
29162 | GAL 2:14 | Da na ga cewa ba sa yin daidai da gaskiyar bishara, sai na ce wa Bitrus a gabansu duka, “Kai mutumin Yahuda ne, duk da haka kana rayuwa kamar Ba’al’umme ba kamar mutumin Yahuda ba. To, yaya aka yi, kana tilasta Al’ummai su bi al’adun Yahudawa? |
29432 | PHP 1:4 | A cikin dukan addu’o’ina dominku duka, nakan yi addu’a da farin ciki kullum |
29447 | PHP 1:19 | gama na san cewa ta wurin addu’o’inku da kuma taimako daga Ruhun Yesu Kiristi, abin da ya same ni zai zama sanadin kuɓutata. |
29792 | 1TI 2:9 | Ina kuma so mata su lura su yi wa kansu adon da ya cancanta, da rigunan da suka dace, ba da adon kitso ko sa kayan zinariya ko lu’ulu’u ko kuma tufafi masu tsada ba, |
29835 | 1TI 5:5 | Gwauruwa wadda ba ta da kowa da zai taimake ta, za tă sa zuciyarta ga Allah, tana roƙo da addu’o’i dare da rana gare shi don taimako. |
30104 | HEB 5:7 | A lokacin da Yesu ya yi rayuwa a duniya, ya yi addu’o’i da roƙe-roƙe tare da kuka mai zafi da kuma hawaye ga wannan wanda yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa ji shi saboda tsananin bangirman da ya yi. |
30855 | REV 5:8 | Bayan ya karɓa, sai halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi ƙasa a gaban Ɗan Ragon. Kowannensu yana da garaya kuma suna riƙe da kaskon zinariya cike da turare, waɗanda suke addu’o’in tsarkaka. |
30898 | REV 8:3 | Wani mala’ika, da yake da kaskon zinariyar da ake zuba turare, ya zo ya tsaya kusa da bagaden. Aka ba shi turare da yawa don yă miƙa tare da addu’o’in dukan tsarkaka a bisa bagaden zinariya a gaban kursiyin. |
30899 | REV 8:4 | Hayaƙin turaren tare da addu’o’in tsarkaka, suka hau zuwa gaban Allah daga hannun mala’ikan. |
31133 | REV 21:11 | Ya haskaka da ɗaukakar Allah, haskensa kuwa ya yi kamar lu’ulu’u mai daraja sosai, kamar yasfa, yana ƙyalƙyali kamar madubi. |
31143 | REV 21:21 | Ƙofofi goma sha biyun nan lu’ulu’ai goma sha biyu ne, kowace ƙofa an yi ta da lu’ulu’u guda. Babban titin birnin kuwa an yi shi da zinariya zalla, yana kuma ƙyalli kamar madubi. |