15881 | PSA 112:10 | Mugun mutum zai gani yă kuma yi fushi, zai ciza haƙora yă kuma lalace; sha’awace-sha’awacen mugaye za su zo ga ƙarshe. |
17598 | ECC 12:5 | sa’ad da mutane suke jin tsoron tudu da kuma hatsarori a tituna; sa’ad da itacen almon ya toho, fāra kuma ya yi ta jan jikinsa da ƙyar, sha’awace-sha’awace sun kafe. Daga nan mutum ya tafi madawwamiyar gidansa ya bar masu makoki suna ta yi. |
20641 | EZK 6:9 | Sa’an nan a cikin al’ummai inda aka kai ku zaman bauta, waɗanda suka a tsere za su tuna da ni, yadda raina ya ɓaci ta wurin zukatansu marasa imani, waɗanda suka rabu da ni, da kuma ta wurin idanunsu, waɗanda suka yi sha’awace-sha’awacen gumakansu. Za su ji ƙyamar kansu saboda mugayen abubuwan da suka aikata. |
22785 | NAM 3:4 | duk saboda yawan sha’awace-sha’awacen karuwa, mai daɗin baki, uwargidan maita, wadda ta ɓad da al’ummai ta wurin karuwancinta ta kuma ɓad da mutane ta wurin maitancinta. |
27791 | ACT 22:19 | “Na amsa na ce, ‘Ubangiji, waɗannan mutane sun san cewa na bi majami’a-majami’a na jefa waɗanda suka gaskata da kai a cikin kurkuku, in kuma yin musu dūka. |
28022 | ROM 1:24 | Saboda haka Allah ya yashe su ga mugayen sha’awace-sha’awacen zukatansu ga fasikanci don a ƙasƙantar da jikunansu ga yin abin kunya. |
28024 | ROM 1:26 | Saboda wannan, Allah ya yashe su ga sha’awace-sha’awacensu masu banƙyama. Har matansu suka sauya daga haɗuwar mace da miji wadda ita ce daidai bisa ga halitta zuwa haɗuwa da ’yan’uwansu mata wadda ba daidai ba. |
28164 | ROM 7:5 | Gama sa’ad da halin mutuntaka yake mulkinmu, sha’awace-sha’awacen zunubi waɗanda dokar ta zuga sun yi ta aiki a jikunanmu, don mu ba da amfani wa mutuwa. |
28189 | ROM 8:5 | Waɗanda suke rayuwa bisa ga mutuntaka sun kafa hankulansu a kan sha’awace-shawa’acen jiki; amma waɗanda suke rayuwa bisa ga Ruhu sun kafa hankulansu a kan abubuwan da Ruhu yake so. |
28348 | ROM 13:14 | A maimakon haka, ku ɗauki halin Ubangiji Yesu Kiristi, kada kuma ku yi tunani game da yadda za ku gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka. |
29245 | GAL 5:16 | Saboda haka ina ce muku, ku yi rayuwa ta wurin Ruhu, ba za ku kuwa gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka ba. |
29299 | EPH 2:3 | Dukanmu a dā mun yi irin rayuwan nan a cikinsu, muna bin kwaɗayi da sha’awace-sha’awacen jikunanmu da tunaninmu. Kamar sauran mutane, mun cancanci fushin Allah. |
29361 | EPH 4:22 | sai ku tuɓe tsohon mutumin nan naku da kuma rayuwarku ta dā, wadda take lalacewa saboda sha’awace-sha’awacen da suke ruɗe ku. |
29864 | 1TI 6:9 | Mutanen da suke son yin arziki sukan fāɗi cikin jarraba, su fāɗa a tarko, suna mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka. |
29916 | 2TI 2:22 | Ka yi nesa da mugayen sha’awace-sha’awace na ƙuruciya, ka kuma bi adalci, bangaskiya, ƙauna da kuma salama, tare da waɗanda suke kira ga Ubangiji daga zuciya mai tsabta. |
29926 | 2TI 3:6 | Irin su ne suke saɗaɗawa su shiga gidaje suna rinjayar mata marasa ƙarfin hali, waɗanda zunubai suka sha kansu, mugayen sha’awace-sha’awace kuma sun ɗauke hankulansu, |
29987 | TIT 2:12 | Yana koya mana mu ce, “A’a” ga rashin tsoron Allah da kuma sha’awace-sha’awacen duniya, mu kuma yi rayuwa ta kamunkai, ta adalci da kuma ta tsoron Allah a cikin wannan zamani, |
29993 | TIT 3:3 | A wani lokaci can baya mu ma wawaye ne, marasa biyayya, aka ruɗe mu, sha’awace-sha’awace da kwaɗayi iri-iri suka daure mu, muka yi zaman ƙiyayya da kishi, aka ƙi mu, mu kuma muka ƙi juna. |
30264 | HEB 11:25 | Ya zaɓa yă sha wahala tare da mutanen Allah, maimakon yă ji daɗin sha’awace-sha’awacen zunubi na ɗan lokaci. |
30405 | JAS 4:1 | Me yake jawo faɗace-faɗace da gardandami a tsakaninku? Ashe, ba sha’awace-sha’awacenku da suke yaƙi a zukatanku ba ne? |
30455 | 1PE 1:14 | Kamar ’ya’ya masu biyayya, kada ku bi mugayen sha’awace-sha’awacen da dā kuke da su sa’ad da kuke rayuwa a cikin jahilci. |
30477 | 1PE 2:11 | Abokaina ƙaunatattu, ina roƙonku, a matsayin bare da kuma baƙi a duniya, ku rabu da sha’awace-sha’awacen zunubin da suke yaƙi da ranku. |
30515 | 1PE 4:2 | Ta haka, ba ya sauran rayuwarsa a kan mugayen sha’awace-sha’awacen jiki, sai dai nufin Allah. |
30550 | 2PE 1:4 | Ta wurin waɗannan ya ba mu alkawaransa masu girma da kuma masu daraja, domin ta wurinsu ku iya yin tarayya cikin Allahntakarsa, ku kuma kuɓuta daga lalatar da take cikin duniya wadda mugayen sha’awace-sha’awace suke jawowa. |
30577 | 2PE 2:10 | Wannan gaskiya ce musamman ga waɗanda suke bin sha’awace-sha’awacen lalaci na mutuntaka, suna kuma rena masu mulki. Da ƙarfin hali da kuma girman kai, waɗannan mutane ba sa tsoro kawo zargin ɓata sunan talikan sama; |
30580 | 2PE 2:13 | Za a yi musu sakamako da muguntar da suka yi. A ra’ayinsu jin daɗi shi ne a yi annashuwa da rana tsaka. Su ƙazamai ne marasa kunya, suna cike da jin daɗin sha’awace-sha’awacensu yayinda suke cin biki tare da ku. |
30633 | 1JN 2:16 | Gama duk abin da yake na duniya, kamar sha’awace-sha’awacen mutuntaka, sha’awar idanunsa, da kuma taƙama da abin da yake da shi, yake kuma yi, ba daga wurin Uba suke fitowa ba sai dai daga duniya. |
30634 | 1JN 2:17 | Duniya da sha’awace-sha’awacenta suna shuɗewa, amma mutumin da yake aikata nufin Allah, zai rayu har abada. |
30758 | JUD 1:18 | Sun ce muku, “A kwanakin ƙarshe za a kasance da masu ba’a waɗanda za su bi sha’awace-sha’awacensu na rashin tsoron Allah.” |