489 | GEN 19:31 | Wata rana ’yarsa babba ta ce wa ƙanuwarta, “Mahaifinmu ya tsufa, kuma babu wani mutum kusa a nan da zai yi mana ciki mu haifi ’ya’ya; yadda al’ada take a ko’ina a duniya. |
2766 | LEV 2:3 | Sauran hadaya ta garin zai zama na Haruna da ’ya’yansa; sashe mafi tsarki ne na hadayar da aka yi ga Ubangiji ta wuta. |
2773 | LEV 2:10 | Sauran hadaya ta garin za tă zama ta Haruna da ’ya’yansa; sashe mafi tsarki ne na hadayun da aka yi ga Ubangiji ta wuta. |
3697 | NUM 3:4 | Amma Nadab da Abihu suka fāɗi suka mutu a gaban Ubangiji a Hamadar Sinai a sa’ad da suka ƙona turare da haramtacciyar wuta a gabansa. Ba su kuwa da ’ya’ya; saboda haka Eleyazar da Itamar kaɗai suka yi aiki firist a zamanin mahaifinsu Haruna. |
3702 | NUM 3:9 | Ka ba da Lawiyawa ga Haruna da ’ya’yansa; su ne za su zama Isra’ilawan da za a ba da su ɗungum gare shi. |
5197 | DEU 10:9 | Shi ya sa Lawiyawa ba su da rabo, ko gādo a cikin ’yan’uwansu; Ubangiji ne gādonsu yadda Ubangiji Allahnku ya faɗa musu.) |
5404 | DEU 18:18 | Zan tayar musu da wani annabi kamar ka daga cikin ’yan’uwansu; zan sa kalmomina a cikin bakinsa, zai kuma faɗa musu kome da na umarce shi. |
8340 | 2SA 13:20 | Absalom ɗan’uwanta ya ce mata, “Amnon, ɗan’uwanki ya ɓata ki ko? To, ki yi shiru ’yar’uwata; ai, ɗan’uwanki ne. Kada wannan abu yă dame ki.” Tamar kuwa ta zauna a gidan ɗan’uwanta Absalom, zaman kaɗaici. |
12609 | NEH 11:17 | Sai kuma Mattaniya ɗan Mika, ɗan Zabdi, ɗan Asaf, shugaban da yake bi da hidimar godiya da kuma addu’a. Sai Bakbukiya, na biyu a cikin ’yan’uwansa; da Abda ɗan Shammuwa, ɗan Galal, ɗan Yedutun. |
13841 | JOB 39:3 | Suna kwanciya su haifi ’ya’yansu; naƙudarsu ta ƙare bayan sun haihu. |
14243 | PSA 22:23 | Zan furta sunanka ga ’yan’uwana; cikin taron masu sujada zan yabe ka. |
18049 | ISA 16:10 | An ɗauke farin ciki da murna daga gonakin itatuwa masu ’ya’ya; babu wanda yake rerawa ko yake sowa a cikin gonakin inabi; babu wanda yake matsin ruwan inabi a wuraren matsi, gama na kawo ƙarshen yin sowa. |
18151 | ISA 23:4 | Ki ji kunya, ya ke Sidon, da ke kuma, kagarar teku, gama teku ya yi magana ya ce, “Ban taɓa naƙuda ba balle in haifi ’ya’ya; ban taɓa goyon ’ya’ya maza ba balle in reno ’ya’ya mata.” |
19314 | JER 11:19 | Na kasance kamar ɗan rago marar faɗa wanda aka kai mayanka; ban gane cewa sun ƙulla mini maƙarƙashiya, suna cewa, “Bari mu lalatar da itacen duk da ’ya’yansa; bari mu datse shi daga ƙasar masu rai, har da ba za a ƙara tunawa da sunansa ba.” |
20876 | EZK 16:45 | Ke ’yar mahaifiyarki ce da gaske, wadda ta ƙi mijinta da ’ya’yanta; ke kuma ’yar’uwar ’yar’uwanki mata ce da gaske, waɗanda suka ƙi mazansu da ’ya’yansu. Mahaifiyarki mutuniyar Hitti ce, mahaifinki kuma mutumin Amoriyawa ne. |
20962 | EZK 19:12 | Amma aka tumɓuke ta cikin fushi aka jefar da ita a ƙasa. Iskar gabas ta sa ta yanƙwane, aka kakkaɓe ’ya’yanta; rassanta masu ƙarfi suka bushe wuta kuma ta cinye su. |
21107 | EZK 23:31 | Kin bi hanyar ’yar’uwarki; saboda haka zan sa kwaf nata a hannunki. |
22402 | JOL 2:22 | Kada ku ji tsoro, ya ku namun jeji, gama wuraren kiwo sun yi kore shar. Itatuwa suna ba da ’ya’yansu; itacen ɓaure da na inabi suna ba da amfaninsu. |
30056 | HEB 2:12 | Ya ce, “Zan sanar da sunanka ga ’yan’uwana; a gaban jama’a zan rera yabonka.” |
30553 | 2PE 1:7 | ga tsoron Allah kuma ku ƙara da nuna alheri ga ’yan’uwa; ga nuna alheri ga ’yan’uwa kuma ku ƙara da ƙauna. |