780 | GEN 28:6 | Yanzu Isuwa ya san cewa Ishaku ya albarkaci Yaƙub ya kuma aike shi zuwa Faddan Aram don yă auri mata daga can, ya kuma san cewa sa’ad da ya albarkace shi, ya umarce shi cewa, “Kada ka auro wata mace daga cikin Kan’aniyawa,” |
18056 | ISA 17:3 | Birni mai katanga za tă ɓace daga Efraim, ikon sarauta kuma daga Damaskus; raguwar Aram za tă zama kamar darajar Isra’ila,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. |
19091 | JER 3:20 | Amma kamar mace marar aminci ga mijinta, haka kika kasance marar aminci gare ni, ya gidan Isra’ila,” in ji Ubangiji. |
19142 | JER 5:15 | Ya gidan Isra’ila,” in ji Ubangiji, “Ina kawo al’umma daga nesa a kanku al’umma ce ta tun dā mai ƙarfin hali, mutane ne da ba ku san harshensu ba, waɗanda ba za ku fahimci abin da suke faɗa ba. |
21160 | EZK 25:8 | “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin Mowab da Seyir sun ce, “Duba, gidan Yahuda ta zama sauran al’ummai,” |
22448 | AMO 1:15 | Sarkinta zai je bauta, shi da ma’aikatansa,” in ji Ubangiji. |
23110 | ZEC 11:13 | Sai Ubangiji ya ce mini, “Jefar da shi cikin ma’aji,” Lada mai kyau da aka yi cinikina ne! Saboda haka sai na ɗauki azurfa talatin ɗin na jefa su cikin gidan Ubangiji don a sa cikin ma’aji. |
23172 | MAL 1:14 | “La’ananne ne macucin da yake da lafiyayyiyar dabba namiji a garkensa wadda ya yi alkawari zai bayar, amma sai ya miƙa hadayar dabba mai aibi ga Ubangiji. Gama ni babban sarki ne, za a kuma ji tsoron sunana a cikin al’ummai,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. |