842 | GEN 30:11 | Sai Liyatu ta ce, “Na yi sa’a!” Saboda haka ta ba shi suna Gad. |
4456 | NUM 24:9 | Kamar zaki sun laɓe sun kwanta, kamar zakanya, wa zai yi ƙarfin hali yă tashe su? “Bari waɗanda suka albarkace ka, su sami albarka waɗanda kuma suka la’anta ka, su la’antu!” |
7069 | JDG 20:13 | Yanzu fa sai ku fitar da waɗannan ’yan iskan da suka aikata wannan abu na Gibeya don mu kashe su mu kawar da mugunta daga Isra’ila!” Amma mutanen Benyamin ba su saurari ’yan’uwansu Isra’ilawa ba. |
7288 | 1SA 3:10 | Ubangiji kuma ya zo ya tsaya a wurin, yana kira ya ce, “Sama’ila, Sama’ila!” Kamar yadda ya kira a lokutan baya. Sai Sama’ila ya ce, “Yi magana gama bawanka yana saurara.” |
8558 | 2SA 20:1 | Akwai wani mai tā-da-na-zaune-tsaye, sunansa Sheba, ɗan Bikri, daga kabilar Benyamin, a wurin. Sai ya busa ƙaho, ya yi ihu ya ce, “Ba mu da rabo a wurin Dawuda, ba mu da sashe a wurin ɗan Yesse! Kowa yă nufi tentinsa, ya Isra’ila!” |
9567 | 2KI 2:12 | Da Elisha ya ga haka sai ya yi ihu yana cewa, “Babana! Babana! Kekunan yaƙin da mahayan dawakan Isra’ila!” Elisha kuwa bai sāke ganinsa ba. Sai ya kama tufafinsa ya yayyage. |
18298 | ISA 30:11 | Ku bar wannan hanya, ku tashi daga wannan hanya, ku kuma daina kalubalantarmu da Mai Tsarkin nan na Isra’ila!” |
26662 | JHN 12:13 | Sai suka ɗaɗɗauko rassan dabino suka fiffita taryensa, suna ɗaga murya suna cewa, “Hosanna!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” “Mai albarka ne Sarkin Isra’ila!” |