8078 | 2SA 2:26 | Sai Abner ya kira Yowab ya ce, har abada ne māshi zai yi ta hallakarwa? Ba ka sani cewa ƙarshen zai zama da ɗaci ba. Sai yaushe za ka umarci mutanenka su daina fafaran ’yan’uwansu? |
13828 | JOB 38:31 | “Za ka iya daure kyakkyawar kaza da ’ya’yanta? Ko za ka iya kunce igiyoyin mafarauci da kare da zomo? |
17813 | ISA 5:4 | Me kuma ya rage da za a yi wa gonar inabina fiye da abin da na yi mata? Da na nemi inabi masu kyau, me ya sa ta ba da munana ’ya’ya? |
19742 | JER 30:6 | Ku tambaya ku ji. Namiji zai iya haifi ’ya’ya? To, me ya sa kuke ganin kowane mai ƙarfi da hannuwansa a kwankwaso kamar mace mai naƙuda, kowace fuska ta koma fari? |
28772 | 1CO 14:26 | Me za mu ce ke nan ’yan’uwa? Sa’ad da kuka taru, wani yakan yi waƙa, wani koyarwa, wani wahayi, wani yin magana da wani harshe, wani kuma fassara. Dole ne a yi duka don gina ikkilisiya. |