1298 | GEN 43:7 | Suka amsa, “Mutumin ya yi mana tambaya sosai game da kanmu da iyalinmu. Ya tambaye mu, ‘Mahaifinku yana da rai har yanzu? Kuna da wani ɗan’uwa?’ Mu dai mun amsa tambayoyinsa ne. Ta yaya za mu sani zai ce, ‘Ku kawo ɗan’uwanku a nan’?” |
1344 | GEN 44:19 | Ranka yă daɗe ya tambayi bayinka ya ce, ‘Kuna da mahaifi ko ɗan’uwa?’ |
1420 | GEN 46:33 | Sa’ad da Fir’auna ya kira ku ciki, ya yi tambaya, ‘Mece ce sana’arku?’ |
21360 | EZK 33:11 | Ka faɗa musu, ‘Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba na jin daɗin mutuwar mugu, amma a maimako haka ya fi su juye daga hanyoyinsu su rayu. Ku juye! Ku juye daga mugayen hanyoyinku! Don me za ku mutu, ya gidan Isra’ila?’ |