23461 | MAT 9:13 | Amma ku je ku koyi abin da wannan yake nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba.’Gama ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi.” |
24665 | MRK 10:8 | su biyun kuma za su zama jiki ɗaya.’Saboda haka, su ba mutum biyu ba ne, amma mutum ɗaya. |
24773 | MRK 12:31 | Na biyun ita ce, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’Ba wata doka da ta fi waɗannan.” |
26371 | JHN 6:45 | A rubuce yake a cikin Annabawa cewa, ‘Allah zai koyar da dukansu.’Duk wanda ya saurari Uba, ya kuma koyi daga wurinsa, zai zo wurina. |