| 23215 | MAT 1:2 | Ibrahim shine mahaifin Ishaku, Ishaku shine mahaifin Yakubu, Yakubu shine mahaifin Yahuza da 'yan'uwansa. |
| 23218 | MAT 1:5 | Salmon shine mahaifin Bo'aza ta wurin Rahab, Bo'aza shine mahaifin Obida ta wurin Rut. Obida shine mahaifin Yesse, |
| 23220 | MAT 1:7 | Sulaimanu shine mahaifin Rehobo'am, Rehobo'am shine mahaifin Abija, Abija shine mahaifin Asa. |
| 23224 | MAT 1:11 | Yosiya shine mahaifin Yekoniya da 'yan'uwansa, dai dai locacin da aka kwashe su zuwa kasar Babila. |
| 23228 | MAT 1:15 | Aliyudu shine mahaifin Ali'azara, Ali'azara shine mahaifin Matana, sannan Matana shine mahaifin Yakubu. |
| 23233 | MAT 1:20 | Yana cikin tunanin wadannan al'amura, sai mala'ikan Ubangiji ya bayyana gareshi a mafarki, ya ce masa, “Yusufu, dan Dauda, kada ka ji tsoron daukar Maryamu a matsayin matarka. Gama abinda ke cikinta, ta wurin Ruhu Mai Tsarki aka same shi. |
| 23236 | MAT 1:23 | “Duba, budurwa za ta sami juna biyu sannan za ta haifi da, za su kira sunansa Immanuel”-ma'ana, “Allah tare da mu.” |
| 23237 | MAT 1:24 | Yusufu ya farka daga barci, ya yi kamar yadda mala'ikan Ubangiji ya umarce shi, sai ya dauke ta a matsayin matarsa. |
| 23240 | MAT 2:2 | ''Ina wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Mun ga tauraronsa a gabas mun kuma zo mu yi masa sujada.'' |
| 23242 | MAT 2:4 | Hirudus ya tara dukan manyan firistoci da marubuta na jama'a, ya tambaye su, “Ina za a haifi Almasihun?” |
| 23243 | MAT 2:5 | Suka ce masa, ''A Baitalami ne ta kasar Yahudiya, domin haka annabin ya rubuta, |
| 23244 | MAT 2:6 | 'Ke kuma, Baitalami, ta kasar Yahudiya, ba ke ce mafi kankanta ba a cikin shugabanin Yahudiya, domin daga cikin ki mai mulki zai fito wanda zai zama makiyayin jama'a ta Isra'ila.''' |
| 23246 | MAT 2:8 | Ya aike su Baitalami, ya ce, ''Ku je ku binciko mani dan yaron da kyau. Idan kun same shi, ku kawo mani labari, don ni ma in je in yi masa sujada.” |
| 23249 | MAT 2:11 | Sai suka shiga gidan, suka ga dan yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka rusuna gabansa suka yi masa sujada. Sa'an nan suka kwance kayansu, suka mika masa kyautar su ta zinariya da lubban, da mur. |
| 23251 | MAT 2:13 | Bayan sun tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, ''Tashi, ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu zuwa kasar Masar, ka zauna a can sai na fada maka, don Hirudus yana shirin binciko dan yaron ya hallaka shi.” |
| 23253 | MAT 2:15 | Ya zauna a can har mutuwar Hirudus. Wannan kuwa domin a cika abin da Ubangiji ya fada ne ta bakin annabin, ''Daga Masar na kirawo Da na.'' |
| 23254 | MAT 2:16 | Da Hirudus ya ga masanan nan sun shashantar da shi, sai ya hasala kwarai, ya aika a karkashe dukan 'yan yara maza da suke Baitalami da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa kasa, gwargwadon lokacin da ya tabbatar a gun masanan. |
| 23256 | MAT 2:18 | ''An ji wata murya a Rama, tana kuka da bakin ciki mai zafi, Rahila ce take kuka saboda 'ya'yanta, kuma ta ki ta ta'azantu, domin ba su. |
| 23257 | MAT 2:19 | Sa'adda Hirudus ya mutu, sai ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki a Masar ya ce, |
| 23258 | MAT 2:20 | ''Tashi ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka tafi kasar Isra'ila, domin masu neman ran dan yaron sun mutu.'' |
| 23259 | MAT 2:21 | Yusufu ya tashi, ya dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ya zo kasar Isra'ila. |
| 23262 | MAT 3:1 | A kwanakin nan Yahaya Mai baftisma ya zo, yana wa'azi a jejin Yahudiya yana cewa, |
| 23264 | MAT 3:3 | Wannan shine wanda annabi Ishaya ya yi maganarsa, ya ce, “Muryar wani mai kira a jeji yana cewa, 'Ku shirya wa Ubangiji hanyarsa, ku daidaita tafarkunsa.'' |
| 23268 | MAT 3:7 | Amma da ya ga Farisawa da Sadukiyawa da yawa, suna fitowa domin a yi masu baftisma, sai ya ce masu, “Ku 'ya'yan macizai masu dafi, wa ya gargade ku ku guje wa fushi mai zuwa? |
| 23269 | MAT 3:8 | Ku ba da 'ya'ya da za su nuna tubanku. |
| 23270 | MAT 3:9 | Kada kuwa ku dauka a ranku cewa, 'Ibrahim ne ubanmu.' Domin ina gaya maku, Allah yana da iko ya ta da wa Ibrahim 'ya'ya daga cikin duwatsun nan. |
| 23271 | MAT 3:10 | Ko yanzu ma an sa gatari a gindin bishiyoyin. Saboda haka duk bishiyar da ba ta ba da 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare ta a jefa a wuta. |
| 23278 | MAT 3:17 | Duba, wata murya daga sammai tana cewa, ''Wannan shi ne kaunataccen Da na. Wanda ya gamshe ni sosai.'' |
| 23279 | MAT 4:1 | Sa'an nan Ruhu ya bi da Yesu zuwa cikin jeji, domin Ibilis ya gwada shi. |
| 23280 | MAT 4:2 | Da ya yi azumi kwana arba'in dare da rana, daga baya yunwa ta kama shi. |
| 23282 | MAT 4:4 | Amma Yesu ya amsa ya ce masa, “A rubuce yake cewa, 'Ba da gurasa kadai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace magana da ta ke fitowa daga wurin Allah.''' |
| 23283 | MAT 4:5 | Sa'an nan Ibilis ya kai shi tsattsarkan birni ya dora shi can kan kololuwar ginin haikali, |
| 23284 | MAT 4:6 | ya ce masa, “In kai Dan Allah ne, to dira kasa. Domin a rubuce yake cewa, 'Zai ba mala'ikunsa umarni game da kai,' kuma, 'Za su daga ka da hannuwansu, domin kada ka yi tuntube da dutse.''' |
| 23285 | MAT 4:7 | Yesu ya ce masa, “kuma a rubuce yake, 'Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.''' |
| 23287 | MAT 4:9 | Ya ce masa, “Dukan wadannan zan baka idan ka rusuna ka yi mani sujada.'' |
| 23288 | MAT 4:10 | Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, Shaidan! Domin a rubuce yake, 'Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kadai za ka bauta wa.''' |
| 23289 | MAT 4:11 | Sa'an nan Ibilis ya rabu da shi, sai kuma mala'iku suka zo suka yi masa hidima. |
| 23293 | MAT 4:15 | “Kasar Zabaluna da kasar Naftali, ta bakin teku, da hayin Kogin Urdun, Galili ta al'ummai! |
| 23295 | MAT 4:17 | Daga lokacin nan, Yesu ya fara wa'azi, yana cewa, “Ku tuba domin mulkin sama ya kusa.” |
| 23296 | MAT 4:18 | Yana tafiya a bakin tekun Galili, sai ya ga wadansu 'yan'uwa biyu, Saminu da ake kira Bitrus, da dan'uwansa Andarawas, suna jefa taru a teku, domin su masunta ne. |
| 23299 | MAT 4:21 | Da Yesu ya ci gaba da tafiya, sai ya ga wadansu mutum biyu, su kuma 'yan'uwa ne, Yakubu dan Zabadi, da dan'uwansa Yahaya, suna cikin jirgi tare da mahaifinsu Zabadi, suna gyaran tarunsu. Sai ya kira su. |
| 23301 | MAT 4:23 | Yesu ya zazzaga dukan kasar Galili, yana koyarwa a majami'unsu, yana shelar bisharar mulkin, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya a cikin mutane. |
| 23304 | MAT 5:1 | Da Yesu ya ga taron jama'ar, sai ya hau saman dutse. Sa'adda ya zauna, almajiransa suka zo wurinsa. |
| 23307 | MAT 5:4 | Albarka ta tabbata ga masu makoki, domin za a ta'azantar da su. |
| 23308 | MAT 5:5 | Albarka ta tabbata ga masu tawali'u, domin za su gaji duniya. |
| 23312 | MAT 5:9 | Albarka ta tabbata ga masu kawo salama, domin za a ce da su 'ya'yan Allah. |
| 23314 | MAT 5:11 | Masu albarka ne ku sa'adda mutane suka zage ku, suka kuma tsananta maku, ko kuwa suka zarge ku da dukan miyagun abubuwa iri iri na karya, saboda ni. |
| 23320 | MAT 5:17 | Kada ku yi tsammanin na zo ne domin in rushe shari'a ko annabawa. Ban zo domin in rushe su ba, amma domin in cika su. |
| 23321 | MAT 5:18 | Domin gaskiya ina gaya maku, har sama da kasa su shude, amma digo ko wasali daya ba za ya shude ba a cikin shari'ar, sai an cika dukan al'amura. |
| 23324 | MAT 5:21 | Kun ji dai an ce wa mutanen da, 'Kada ka yi kisan kai,' kuma 'Duk wanda ya yi kisan kai yana cikin hatsarin hukunci.' |
| 23325 | MAT 5:22 | Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da dan'uwansa, yana cikin hatsarin hukunci. Kuma duk wanda ya ce da dan'uwansa, 'Kai mutumin banza!' yana cikin hatsarin tsayawa gaban majalisa, kowa kuma ya ce da dan'uwan sa 'Kai wawa!' yana cikin hatsarin shiga wutar jahannama. |
| 23326 | MAT 5:23 | Saboda haka idan za ka yi baiko a bagadi sai ka tuna cewa dan'uwanka yana da damuwa da kai, |
| 23327 | MAT 5:24 | ka bar baikon ka a gaban bagadin, ka yi tafiyarka. Da farko dai, ka sasanta da dan'uwanka kafin ka zo ka mika baikon. |
| 23328 | MAT 5:25 | Ka yi sulhu da mai karar ka tun kana hanyar zuwa gaban shari'a, domin kada mai karar ka ya mika ka ga alkali, alkali kuwa ya mika ka ga dogarai, za a kuwa jefa ka a kurkuku. |
| 23330 | MAT 5:27 | Kun dai ji an ce, 'Kada ka yi zina'. |
| 23331 | MAT 5:28 | Amma ina gaya maku, duk wanda ya dubi mace, da muguwar sha'awa, ya riga ya yi zina da ita a zuciyarsa. |
| 23334 | MAT 5:31 | An sake fada, 'Duk wanda ya kori matarsa, sai ya ba ta takaddar saki.' |
| 23336 | MAT 5:33 | Kun sake ji an ce wa wadan da suke a zamanin da, 'Kada ku yi rantsuwar karya, amma ku yi rantsuwar ku ga Ubangiji.' |
| 23340 | MAT 5:37 | Amma bari maganarku ta zama 'I, I', ko kuwa 'A'a, a'a.' Duk abin da ya wuce wannan, daga mugun yake. |
| 23341 | MAT 5:38 | Kun dai ji an ce, “Ido a maimakon ido, hakori kuma a maimakon hakori.' |
| 23343 | MAT 5:40 | Idan wani yana da niyyar kai kararku gaban shari'a saboda ya karbi rigarku, ku ba wannan mutumin mayafinku ma. |
| 23346 | MAT 5:43 | Kun ji abin da aka fada, 'Za ka kaunaci makwabcin ka ka ki magabcin ka.' |
| 23347 | MAT 5:44 | Amma ina gaya maku, ku kaunaci magabtan ku, ku yi addu'a domin masu tsananta maku, ku albarkaci wadanda suka la'ance ku, ku yi alheri ga wadanda suke kin ku, |
| 23348 | MAT 5:45 | domin ku zama 'ya'yan Ubanku da ke cikin sama. Domin yakan sa rana ta haskaka wa mugu da mutumin kirki, kuma yakan aiko da ruwan sama ga adali da azzalumi. |
| 23350 | MAT 5:47 | Kuma in kun gaida 'yan'uwanku kadai, me kuke yi fiye da sauran? Ba hakanan al'ummai ma suke yi ba? |
| 23353 | MAT 6:2 | Saboda haka, in za ku yi sadaka, kada ku busa kaho yadda munafukai suke yi a majami'u da kuma akan tituna domin mutane su yabesu. Gaskiya ina gaya maku, sun samu ladansu. |
| 23356 | MAT 6:5 | Sa'adda za ku yi addu'a kuma, kada ku zama kamar munafukai, domin sun cika son yin addu'a a tsaye a majami'unsu da kuma a gefen tituna, domin mutane su gansu. Gaskiya ina gaya maku, sun sami ladarsu kenan. |
| 23357 | MAT 6:6 | Amma ku, idan za ku yi addu'a, sai ku shiga cikin daki. Ku rufe kofa, ku yi addu'a ga Ubanku wanda yake a asirce, Ubanku kuwa da ke ganin abin da ake yi a asirce, zai saka maku. |
| 23358 | MAT 6:7 | Idan za ku yi addu'a, kada ku yi ta maimaici marar anfani, kamar yadda al'ummai suke yi, domin a tunanin su za a saurare su saboda yawan maganganunsu. |
| 23360 | MAT 6:9 | Saboda haka sai ku yi addu'a kamar haka: 'Ubanmu da ke sama, bari a tsarkake sunanka. |
| 23364 | MAT 6:13 | Kuma kada ka kawo mu cikin jaraba, amma ka kubutar da mu daga Mugun.' [Gama mulki da iko da daukaka naka ne har abada. Amin] |
| 23382 | MAT 6:31 | Don haka kada ku damu, kuna cewa, 'Me za mu ci? ko, Me za mu sha?' ko kuwa, 'Wadanne tufafi za mu sa?' |
| 23383 | MAT 6:32 | Ai, al'ummai ma suna neman dukan irin wadannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu. |
| 23388 | MAT 7:3 | Don me kake duban dan hakin da ke idon dan'uwanka, amma ba ka kula da gungumen da ke naka idon ba? |
| 23389 | MAT 7:4 | Ko kuwa yaya za ka iya ce wa dan'uwanka, 'Bari in cire maka dan hakin da ke idon ka,' alhali ga gungume a cikin naka idon? |
| 23390 | MAT 7:5 | Kai munafiki! Ka fara cire gungumen da ke idonka, sa'annan za ka iya gani sosai yadda za ka cire dan hakin da ke idon dan'uwanka. |
| 23391 | MAT 7:6 | Kada ku ba karnuka abin da ke tsattsarka. Kada kuma ku jefa wa aladu, lu'u lu'anku. Idan ba haka ba za su tattake su a karkashin sawunsu, su kuma juyo su kekketa ku. |
| 23396 | MAT 7:11 | Saboda haka, idan ku da ku ke miyagu, kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga 'ya'yanku, ina kimanin yadda Ubanku na sama zai ba da abubuwa masu kyau ga duk wadanda suke rokon sa? |
| 23397 | MAT 7:12 | Saboda haka, duk abinda ku ke so mutane su yi maku, ku ma sai ku yi masu, domin wannan shi ne dukan shari'a da koyarwar annabawa. |
| 23401 | MAT 7:16 | Za ku gane su ta irin ''ya'yansu. Mutane na cirar inabi a jikin kaya, ko kuwa baure a jikin sarkakkiya? |
| 23402 | MAT 7:17 | Haka kowanne itace mai kyau yakan haifi kyawawan 'ya'ya, amma mummunan itace kuwa yakan haifi munanan 'ya'ya. |
| 23403 | MAT 7:18 | Kyakkyawan itace ba zai taba haifar da munanan 'ya'ya ba, haka kuma mummunan itace ba zai taba haifar da kyawawan 'ya'ya ba. |
| 23404 | MAT 7:19 | Duk itacen da ba ya ba da 'ya'ya masu kyau, sai a sare shi a jefa a wuta. |
| 23405 | MAT 7:20 | Domin haka, ta irin 'ya'yansu za a gane su. |
| 23406 | MAT 7:21 | Ba duk mai ce mani, 'Ubangiji, Ubangiji,' ne, zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda ya yi nufin Ubana da yake cikin sama. |
| 23407 | MAT 7:22 | A ranar nan da yawa za su ce mani, 'Ubangiji, Ubangiji,' ashe ba mu yi annabci da sunanka ba, ba mu fitar da aljanu da sunanka ba, ba mu kuma yi manyan ayyuka masu yawa da sunanka ba?' |
| 23408 | MAT 7:23 | Sa'annan zan ce masu 'Ni ban taba saninku ba! Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!' |
| 23412 | MAT 7:27 | Ruwa ya sauko, ambaliyar ruwa ta zo, sai iska ta taso ta buga gidan. Sai kuma ya rushe, ya kuwa yi cikakkiyar ragargajewa.'' |
| 23413 | MAT 7:28 | Ya zama sa'adda Yesu ya gama fadin wadannan maganganu, sai taro suka yi mamakin koyarwarsa, |
| 23418 | MAT 8:4 | Yesu ya ce masa, 'Ka tabbata, ba ka gaya wa kowa komai ba. Sai dai ka je ka nuna kan ka ga firist, ka kuma bayar da baiko da Musa ya umarta domin shaida garesu? |
| 23423 | MAT 8:9 | Domin ni ma ina karkashin ikon wani ne, ina kuma da sojoji a karkashina, sai in ce wa wannan, 'je ka,' sai ya je, wani kuma in ce masa, 'zo,' sai ya zo, in ce wa bawa na, 'yi abu kaza,' sai ya yi,” |
| 23424 | MAT 8:10 | Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki, har ya ce wa mabiyansa, “Gaskiya, ina gaya maku, ko a cikin isra'ila ban taba samun bangaskiya mai karfi irin wannan ba. |
| 23426 | MAT 8:12 | Amma 'ya'yan mulkin kuwa sai a jefa su cikin matsanancin duhu. Can za su yi kuka da cizon hakora.” |
| 23427 | MAT 8:13 | Yesu ya ce wa hafsan, “Je ka! Bari ya zamar maka gwargwadon bangaskiyar da ka yi,” A daidai wannan sa'a bawansa ya warke. |
| 23432 | MAT 8:18 | Sa'adda Yesu ya ga taro masu yawa kewaye da shi, sai ya ba da umarni su tafi su koma wancan hayi na tekun Galili. |
| 23440 | MAT 8:26 | Yesu ya ce masu, “Don me kuka firgita haka, ya ku masu karancin bangaskiya?” Sa'annan ya tashi, ya tsauta wa iskar da tekun. Sai wurin gaba daya ya yi tsit. |
| 23441 | MAT 8:27 | Mutanen suka yi al'ajibi, suka ce, “Wanne irin mutum ne wannan, wanda har iska da teku ma suke masa biyayya?”. |
| 23442 | MAT 8:28 | Da Yesu ya zo daga wancan hayin a kasar Garasinawa, mutane biyu masu al'janu suka fito suka same shi. Suna fitowa daga makabarta kuma suna da fada sosai, har ma ba mai iya bin ta wannan hanya. |
| 23445 | MAT 8:31 | Sai al'janun suka roki Yesu suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan.” |
| 23447 | MAT 8:33 | Mutanen masu kiwon aladun suka gudu, suka shiga gari, suka yi ta ba da labarin komai da komai, musamman abin da ya faru da masu al'janun. |