23214 | MAT 1:1 | Littafin asalin Yesu Almasihu Dan Dauda, Dan Ibrahim. |
23216 | MAT 1:3 | Yahuza shine mahaifin Farisa da Zera, ta wurin Tamar. Farisa kuma shine mahaifin Hasruna, Hasruna kuma shine mahaifin Aram. |
23217 | MAT 1:4 | Aram shine mahaifin Amminadab, Amminadab shine mahaifin Nashon, Nashon shine mahaifin Salmon. |
23220 | MAT 1:7 | Sulaimanu shine mahaifin Rehobo'am, Rehobo'am shine mahaifin Abija, Abija shine mahaifin Asa. |
23221 | MAT 1:8 | Asa shine mahaifin Yehoshafat, Yehoshafat shine mahaifin Yoram, Yoram kuma shine mahaifin Uziya. |
23222 | MAT 1:9 | Uziya shine mahaifin Yotam, Yotam shine mahaifin Ahaz, Ahaz shine mahaifin Hezekiya. |
23223 | MAT 1:10 | Hezekiya shine mahaifin Manassa, Manassa shine mahaifin Amon, sannan Amon shine mahaifin Yosiya. |
23226 | MAT 1:13 | Zarubabel shine mahaifin Abihudu, Abihudu shine mahaifin Eliyakim, sannan Eliyakim shine mahaifin Azuru. |
23227 | MAT 1:14 | Azuru shine mahaifin Saduku. Saduku shine mahaifin Akimu, sannan Akimu shine mahaifin Aliyudu |
23228 | MAT 1:15 | Aliyudu shine mahaifin Ali'azara, Ali'azara shine mahaifin Matana, sannan Matana shine mahaifin Yakubu. |
23229 | MAT 1:16 | Yakubu shine mahaifin Yusufu maigidan Maryamu, wadda ta wurin ta ne aka haifi Yesu, wanda ake ce da shi Almasihu. |
23230 | MAT 1:17 | Tun daga Ibrahim zuwa Dauda, an yi tsara goma sha hudu ne, daga Dauda zuwa lokacin da aka kwashe su zuwa Babila, tsara goma sha hudu ne, sannan daga lokacin da aka kwashe su zuwa Babila zuwa Almasihu tsara goma sha hudu ne |
23231 | MAT 1:18 | Ga yadda haihuwar Yesu Almasihu ta kasance. Mahaifiyarsa, Maryamu, tana tashi da Yusufu, amma kafin su yi aure, sai aka same ta da juna biyu ta wurin Ruhu Mai Tsarki. |
23236 | MAT 1:23 | “Duba, budurwa za ta sami juna biyu sannan za ta haifi da, za su kira sunansa Immanuel”-ma'ana, “Allah tare da mu.” |
23238 | MAT 1:25 | Amma Yusufu bai sadu da ita ba sai bayan da ta haifi da. Ya kira sunansa Yesu. |
23242 | MAT 2:4 | Hirudus ya tara dukan manyan firistoci da marubuta na jama'a, ya tambaye su, “Ina za a haifi Almasihun?” |
23243 | MAT 2:5 | Suka ce masa, ''A Baitalami ne ta kasar Yahudiya, domin haka annabin ya rubuta, |
23250 | MAT 2:12 | Allah kuma ya gargade su a mafarki kada su koma wurin Hirudus, sai suka koma kasarsu ta wata hanya dabam. |
23252 | MAT 2:14 | A wannan dare fa Yusufu ya tashi ya dauki dan yaron da mahafiyarsa ya tafi Masar. |
23255 | MAT 2:17 | A lokacin ne aka cika fadar Annabi Irmiya, |
23256 | MAT 2:18 | ''An ji wata murya a Rama, tana kuka da bakin ciki mai zafi, Rahila ce take kuka saboda 'ya'yanta, kuma ta ki ta ta'azantu, domin ba su. |
23260 | MAT 2:22 | Amma da ya ji Arkilayus ya gaji mahaifinsa Hirudus, yana mulkin kasar Yahudiya, sai ya ji tsoron isa can. Bayan da Allah ya yi masa gargadi a mafarki, sai ya ratse zuwa kasar Galili |
23262 | MAT 3:1 | A kwanakin nan Yahaya Mai baftisma ya zo, yana wa'azi a jejin Yahudiya yana cewa, |
23268 | MAT 3:7 | Amma da ya ga Farisawa da Sadukiyawa da yawa, suna fitowa domin a yi masu baftisma, sai ya ce masu, “Ku 'ya'yan macizai masu dafi, wa ya gargade ku ku guje wa fushi mai zuwa? |
23270 | MAT 3:9 | Kada kuwa ku dauka a ranku cewa, 'Ibrahim ne ubanmu.' Domin ina gaya maku, Allah yana da iko ya ta da wa Ibrahim 'ya'ya daga cikin duwatsun nan. |
23272 | MAT 3:11 | Na yi maku baftisma da ruwa, zuwa tuba. Amma mai zuwa baya na, ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in dauka ba. Shi ne zai yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta. |
23275 | MAT 3:14 | Amma Yahaya ya yi ta kokarin ya hana shi, yana cewa, “Ni da nake bukatar ka yi mani baftisma, ka zo gare ni?” |
23277 | MAT 3:16 | Bayan da aka yi masa baftisma, Yesu ya fito nan da nan daga cikin ruwan, sai kuma sammai suka bude masa. Ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya, ya sauko a kansa. |
23281 | MAT 4:3 | Sai mai jarabtar nan ya zo, ya ce masa, “Idan kai Dan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama gurasa.” |
23282 | MAT 4:4 | Amma Yesu ya amsa ya ce masa, “A rubuce yake cewa, 'Ba da gurasa kadai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace magana da ta ke fitowa daga wurin Allah.''' |
23284 | MAT 4:6 | ya ce masa, “In kai Dan Allah ne, to dira kasa. Domin a rubuce yake cewa, 'Zai ba mala'ikunsa umarni game da kai,' kuma, 'Za su daga ka da hannuwansu, domin kada ka yi tuntube da dutse.''' |
23285 | MAT 4:7 | Yesu ya ce masa, “kuma a rubuce yake, 'Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.''' |
23288 | MAT 4:10 | Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, Shaidan! Domin a rubuce yake, 'Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kadai za ka bauta wa.''' |
23296 | MAT 4:18 | Yana tafiya a bakin tekun Galili, sai ya ga wadansu 'yan'uwa biyu, Saminu da ake kira Bitrus, da dan'uwansa Andarawas, suna jefa taru a teku, domin su masunta ne. |
23306 | MAT 5:3 | “Albarka ta tabbata ga masu talauci a ruhu, domin mulkin sama nasu ne. |
23307 | MAT 5:4 | Albarka ta tabbata ga masu makoki, domin za a ta'azantar da su. |
23308 | MAT 5:5 | Albarka ta tabbata ga masu tawali'u, domin za su gaji duniya. |
23309 | MAT 5:6 | Albarka ta tabbata ga masu yunwa da kishin adalci, domin za a kosar da su. |
23310 | MAT 5:7 | Albarka ta tabbata ga masu jinkai, domin za su samu jinkai. |
23311 | MAT 5:8 | Albarka ta tabbata ga masu tsabtar zuciya, domin za su ga Allah. |
23312 | MAT 5:9 | Albarka ta tabbata ga masu kawo salama, domin za a ce da su 'ya'yan Allah. |
23313 | MAT 5:10 | Albarka ta tabbata ga wadanda ake tsananta masu saboda adalci, domin mulkin sama nasu ne. |
23322 | MAT 5:19 | Saboda haka duk wanda ya karya mafi kankanta daga cikin dokokin nan ko kuwa ya koya wa wasu su yi haka, za a kira shi mafi kankanta a cikin mulkin sama. Amma dukan wanda ya kiyaye su ko kuwa ya koyar da su, za a kira shi mafi girma a cikin mulkin sama. |
23325 | MAT 5:22 | Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da dan'uwansa, yana cikin hatsarin hukunci. Kuma duk wanda ya ce da dan'uwansa, 'Kai mutumin banza!' yana cikin hatsarin tsayawa gaban majalisa, kowa kuma ya ce da dan'uwan sa 'Kai wawa!' yana cikin hatsarin shiga wutar jahannama. |
23331 | MAT 5:28 | Amma ina gaya maku, duk wanda ya dubi mace, da muguwar sha'awa, ya riga ya yi zina da ita a zuciyarsa. |
23334 | MAT 5:31 | An sake fada, 'Duk wanda ya kori matarsa, sai ya ba ta takaddar saki.' |
23335 | MAT 5:32 | Amma ina gaya maku ko wa ya saki matarsa, idan ba a kan laifin lalata ba, ya mai da ita mazinaciya kenan. Kuma duk wanda ya aure ta bayan sakin, ya yi zina kenan. |
23337 | MAT 5:34 | Amma ina gaya maku, kada ku yi rantsuwa sam, ko da sama domin kursuyin Allah ne; |
23340 | MAT 5:37 | Amma bari maganarku ta zama 'I, I', ko kuwa 'A'a, a'a.' Duk abin da ya wuce wannan, daga mugun yake. |
23342 | MAT 5:39 | Amma ina gaya maku, kada ku yi jayayya da wanda ke mugu, a maimakon haka, ko wa ya mare ku a kuncin dama, ku juya masa dayan ma. |
23347 | MAT 5:44 | Amma ina gaya maku, ku kaunaci magabtan ku, ku yi addu'a domin masu tsananta maku, ku albarkaci wadanda suka la'ance ku, ku yi alheri ga wadanda suke kin ku, |
23354 | MAT 6:3 | Amma in za ku yi sadaka, kada hannunku na hagu ya san abin da hannunku na dama yake yi, |
23357 | MAT 6:6 | Amma ku, idan za ku yi addu'a, sai ku shiga cikin daki. Ku rufe kofa, ku yi addu'a ga Ubanku wanda yake a asirce, Ubanku kuwa da ke ganin abin da ake yi a asirce, zai saka maku. |
23364 | MAT 6:13 | Kuma kada ka kawo mu cikin jaraba, amma ka kubutar da mu daga Mugun.' [Gama mulki da iko da daukaka naka ne har abada. Amin] |
23368 | MAT 6:17 | Amma in kuna azumi, ku shafa mai a ka, ku kuma wanke fuska, |
23374 | MAT 6:23 | Amma in idonka na da lahani, dukan jiki na cike da duhu. Saboda haka, in hasken da yake cikinka duhu ne, ina misalin yawan duhun! |
23375 | MAT 6:24 | Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu, ko dai ya ki daya, ya so daya, ko kuma ya amince wa dayan ya raina dayan. Ba dama ku bauta wa Allah da kuma dukiya. |
23376 | MAT 6:25 | Saboda haka ina gaya maku, kada ku damu a kan rayuwarku, game da abin da za ku ci, da abin da za ku sha- ko kuwa jikinku, abin da za ku yi tufafi da shi. Ashe rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba? |
23377 | MAT 6:26 | Ku dubi tsuntsayen da ke sararin sama. Ai, ba su shuka, balle girbi, ba su kuma tarawa a cikin rumbuna, amma Ubanku na Sama na ciyar da su. Ashe, ba ku fi su martaba ba? |
23381 | MAT 6:30 | Idan Allah yayi wa ciyawar jeji ado, wadda yau tana wanzuwa, gobe kuwa a jefa ta cikin murhu, ina misalin adon da za ya yi maku, ya ku masu karancin bangaskiya? |
23383 | MAT 6:32 | Ai, al'ummai ma suna neman dukan irin wadannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu. |
23384 | MAT 6:33 | Amma ku nemi mulkinsa da farko da adalcinsa, kuma dukan wadannan abubuwa za a baku. |
23393 | MAT 7:8 | Ai duk wanda ya roka, zai karba, kuma duk wanda ya nema zai samu, wanda ya kwankwasa kuma za a bude masa. |
23407 | MAT 7:22 | A ranar nan da yawa za su ce mani, 'Ubangiji, Ubangiji,' ashe ba mu yi annabci da sunanka ba, ba mu fitar da aljanu da sunanka ba, ba mu kuma yi manyan ayyuka masu yawa da sunanka ba?' |
23411 | MAT 7:26 | Amma duk wanda ya ji maganar nan tawa, bai aikata ta ba, za a misalta shi da wawan mutum da ya gina gidansa a kan rairayi. |
23426 | MAT 8:12 | Amma 'ya'yan mulkin kuwa sai a jefa su cikin matsanancin duhu. Can za su yi kuka da cizon hakora.” |
23427 | MAT 8:13 | Yesu ya ce wa hafsan, “Je ka! Bari ya zamar maka gwargwadon bangaskiyar da ka yi,” A daidai wannan sa'a bawansa ya warke. |
23436 | MAT 8:22 | Amma Yesu ya ce masa, “Bari matattu su binne matattunsu.” |
23438 | MAT 8:24 | Sai ga wata babbar iska ta taso a tekun, har rakuman ruwa suka fara shan kan jirgin. Amma Yesu yana barci. |
23443 | MAT 8:29 | Sai suka kwala ihu suka ce, “Ina ruwanka da mu, kai dan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?” |
23450 | MAT 9:2 | Sai gashi, sun kawo masa wani mutum shanyayye kwance a tabarma. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, ''Da, ka yi farin ciki. An gafarta maka zunuban ka.'' |
23453 | MAT 9:5 | Wanne ya fi sauki, a ce, 'An gafarta maka zunubanka,' ko kuwa a ce, 'Tashi ka yi tafiya'? |
23454 | MAT 9:6 | Amma domin ku sani Dan mutum yana da ikon gafarta zunubai a duniya...'' Sai ya ce wa shanyayyen, ''Tashi, ka dauki shimfidarka ka tafi gida.'' |
23456 | MAT 9:8 | Da taron suka ga haka sai suka yi mamaki, suka daukaka Allah, wanda ya ba mutane irin wannan iko. |
23460 | MAT 9:12 | Amma da Yesu ya ji haka ya ce, ''Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya. |
23463 | MAT 9:15 | Sai Yesu ya ce masu, ''Masu hidimar buki za su yi bakin ciki tun ango yana tare da su? Ai, lokaci yana zuwa da za a dauke masu angon. A sa'annan ne fa za su yi azumi.'' |
23465 | MAT 9:17 | Mutane kuma ba su dura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. Idan sun yi haka, sai salkunan kuma su fashe inabin ya tsiyaye, sai salkunan su lalace. A maimakon haka, ana sa sabon inabi cikin sababbin salkuna, ta haka an tsirar da duka biyun kenan.'' |
23478 | MAT 9:30 | Sai idanunsu suka bude. Amma Yesu ya umarce su kwarai, ya ce, ''Kada fa kowa ya ji labarin nan.'' |
23479 | MAT 9:31 | Amma suka tafi suka yi ta baza labarinsa a duk yankin. |
23482 | MAT 9:34 | Amma sai Farisawa suka ce, ''Ai, da ikon sarkin aljanu ya ke fitar da aljanu.'' |
23483 | MAT 9:35 | Sai Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da kauyuka, yana koyarwa a majami'unsu, yana yin bisharar mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya. |