Wildebeest analysis examples for:   hau-hauulb   B    February 11, 2023 at 18:42    Script wb_pprint_html.py   by Ulf Hermjakob

23218  MAT 1:5  Salmon shine mahaifin Bo'aza ta wurin Rahab, Bo'aza shine mahaifin Obida ta wurin Rut. Obida shine mahaifin Yesse,
23224  MAT 1:11  Yosiya shine mahaifin Yekoniya da 'yan'uwansa, dai dai locacin da aka kwashe su zuwa kasar Babila.
23225  MAT 1:12  Bayan kwasar su zuwa kasar Babila, Yekoniya shine mahaifin Sheyaltiyel, Sheyaltiyel shine mahaifin Zarubabel.
23230  MAT 1:17  Tun daga Ibrahim zuwa Dauda, an yi tsara goma sha hudu ne, daga Dauda zuwa lokacin da aka kwashe su zuwa Babila, tsara goma sha hudu ne, sannan daga lokacin da aka kwashe su zuwa Babila zuwa Almasihu tsara goma sha hudu ne
23239  MAT 2:1  Bayanda aka haifi Yesu a Baitalami ta kasar Yahudiya, a zamanin sarki Hirudus, sai ga wadansu masana daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa,
23243  MAT 2:5  Suka ce masa, ''A Baitalami ne ta kasar Yahudiya, domin haka annabin ya rubuta,
23244  MAT 2:6  'Ke kuma, Baitalami, ta kasar Yahudiya, ba ke ce mafi kankanta ba a cikin shugabanin Yahudiya, domin daga cikin ki mai mulki zai fito wanda zai zama makiyayin jama'a ta Isra'ila.'''
23246  MAT 2:8  Ya aike su Baitalami, ya ce, ''Ku je ku binciko mani dan yaron da kyau. Idan kun same shi, ku kawo mani labari, don ni ma in je in yi masa sujada.”
23247  MAT 2:9  Bayan sun ji maganar sarkin, sai suka yi tafiyar su, ga shi kuwa, tauraron da suka gani a gabas yana tafe a gaban su, har ya zo ya tsaya bisa inda dan yaron nan yake.
23251  MAT 2:13  Bayan sun tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, ''Tashi, ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu zuwa kasar Masar, ka zauna a can sai na fada maka, don Hirudus yana shirin binciko dan yaron ya hallaka shi.”
23254  MAT 2:16  Da Hirudus ya ga masanan nan sun shashantar da shi, sai ya hasala kwarai, ya aika a karkashe dukan 'yan yara maza da suke Baitalami da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa kasa, gwargwadon lokacin da ya tabbatar a gun masanan.
23260  MAT 2:22  Amma da ya ji Arkilayus ya gaji mahaifinsa Hirudus, yana mulkin kasar Yahudiya, sai ya ji tsoron isa can. Bayan da Allah ya yi masa gargadi a mafarki, sai ya ratse zuwa kasar Galili
23261  MAT 2:23  sai ya je ya zauna a wani gari da ake kira Nazarat. Wannan ya cika abin da aka fada ta bakin annabawa, cewa, za a kira shi Banazare.
23276  MAT 3:15  Yesu ya amsa masa ya ce,Bari ya zama haka a yanzu, domin a cika dukan adalci.” Sai Yahaya ya yarje masa.
23277  MAT 3:16  Bayan da aka yi masa baftisma, Yesu ya fito nan da nan daga cikin ruwan, sai kuma sammai suka bude masa. Ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya, ya sauko a kansa.
23282  MAT 4:4  Amma Yesu ya amsa ya ce masa, “A rubuce yake cewa, 'Ba da gurasa kadai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace magana da ta ke fitowa daga wurin Allah.'''
23296  MAT 4:18  Yana tafiya a bakin tekun Galili, sai ya ga wadansu 'yan'uwa biyu, Saminu da ake kira Bitrus, da dan'uwansa Andarawas, suna jefa taru a teku, domin su masunta ne.
23316  MAT 5:13  Ku ne gishirin duniya, amma idan gishiri ya sane yaya za a mai da dandanonsa? Ba zai kara anfani ga komai ba, sai ko a zubar da shi, a tattake a karkashin kafafun mutane.
23319  MAT 5:16  Bari hasken ku ya haskaka gaban mutane yadda za su ga kyawawan ayyukanku su kuma yabi Ubanku da ke cikin sama.
23320  MAT 5:17  Kada ku yi tsammanin na zo ne domin in rushe shari'a ko annabawa. Ban zo domin in rushe su ba, amma domin in cika su.
23349  MAT 5:46  Domin idan kuna kaunar wadanda suke kaunarku, wanne lada kuka samu? Ba haka masu karban haraji ma suke yi ba?
23350  MAT 5:47  Kuma in kun gaida 'yan'uwanku kadai, me kuke yi fiye da sauran? Ba hakanan al'ummai ma suke yi ba?
23361  MAT 6:10  Bari mulkinka shi zo. Bari nufinka ya yiwu a duniya kamar yadda ake yi a sama.
23375  MAT 6:24  Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu, ko dai ya ki daya, ya so daya, ko kuma ya amince wa dayan ya raina dayan. Ba dama ku bauta wa Allah da kuma dukiya.
23379  MAT 6:28  To, don me kuke damuwa a kan tufafi? Ku dubi furannin jeji, yadda suke girma. Ba su aiki, kuma ba su sakar kaya.
23389  MAT 7:4  Ko kuwa yaya za ka iya ce wa dan'uwanka, 'Bari in cire maka dan hakin da ke idon ka,' alhali ga gungume a cikin naka idon?
23406  MAT 7:21  Ba duk mai ce mani, 'Ubangiji, Ubangiji,' ne, zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda ya yi nufin Ubana da yake cikin sama.
23427  MAT 8:13  Yesu ya ce wa hafsan, “Je ka! Bari ya zamar maka gwargwadon bangaskiyar da ka yi,” A daidai wannan sa'a bawansa ya warke.
23428  MAT 8:14  Da Yesu ya shiga gidan Btrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance da zazzabi.
23436  MAT 8:22  Amma Yesu ya ce masa,Bari matattu su binne matattunsu.”
23461  MAT 9:13  Sai ku fahimci ma'anar wannan tukuna, 'Ni kam, ina bukatar jinkai ba hadaya ba.' Ba domin in kira masu adalci su tuba na zo ba, sai dai masu zunubi.
23464  MAT 9:16  Babu mutumin da zai sa sabon kyalle a kan tsohuwar tufa, domin kyallen zai yage daga tufar, har ma yagewar ta fi ta da.
23470  MAT 9:22  Sai Yesu ya juya, ya gan ta ya ce, '''Yata, ki karfafa. Bangaskiyarki ta warkar da ke.'' Nan take matar ta warke.
23481  MAT 9:33  Bayan da an fitar da aljanin, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki, su ka ce, ''Kai, ba a taba ganin irin wannan a cikin Isra'ila ba!''
23488  MAT 10:2  To yanzu ga sunayen manzanin nan goma sha biyu. Na farkon shine, Saminu, wanda ake kira Bitrus, da dan'uwansa Andarawas, da Yakubu dan Zabadi, da dan'uwansa Yahaya;
23489  MAT 10:3  Filibus, da Bartalamawus, da Toma da Matiyu mai karbar haraji da Yakubu dan Halfa, da Taddawus;
23490  MAT 10:4  Saminu Bakairawane, da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bashe shi.
23511  MAT 10:25  Dai dai ne almajiri ya zama kamar malaminsa, bawa kuma kamar ubangijinsa. In har sun kira mai gida Ba'alzabuba, za su kuma bata mutanen gidansa!
23515  MAT 10:29  Ba 'yan tsuntsaye biyu ake sayarwa akan kobo ba? Ba ko daya a cikin su da zai fadi kasa ba tare da yardar Ubanku ba.
23520  MAT 10:34  ''Kada ku zaci na zo ne in kawo salama a duniya. Ban zo domin in kawo salama ba, sai dai takobi.
23529  MAT 11:1  Bayan Yesu ya gama yi wa almajiransa gargadi, sai ya bar wannan wuri, ya tafi biranensu domin yayi koyorwa, da wa'azi.
23535  MAT 11:7  Bayan wadannan sun tafi, sai Yesu ya fara wa jama'a jawabi game da Yahaya mai baftisma, yana cewa, “Me ake zuwa gani a jeji - ciyawa ce da iska ke busawa?
23549  MAT 11:21  “Kaiton ki Korasinu, kaiton ki Batsaida! In da an yi irin ayuka masu ban mamaki a Taya da Sidon! Yadda aka yi a cikinku, da tuni sun tuba suna sanye da tsumma da yafa toka.
23561  MAT 12:3  Amma Yesu ya ce masu,Baku karanta abin da Dauda ya yi ba, lokacin da ya ke jin yunwa, tare da mazan da ke tare da shi?
23577  MAT 12:19  Ba za ya yi jayayya ko tada murya ba, babu wanda za ya ji muryar sa a karabku.
23578  MAT 12:20  Ba zai karya kara da ya tankwashe ba; ba zai kashe fitilar da ta kusa mutuwa ba; sai ya kawo hukunci ga nasara.
23582  MAT 12:24  Amma da Farisawa su ka ji wannan al'ajibi, sai su ka ce, “Mutumin nan yana fitar da aljannu ta wurin Bahalzabuba sarkin aljannu ne.”
23585  MAT 12:27  Idan Ina fitar da aljannu da ikon Ba'alzabuba, ta wurin wa masu bin ku su ke fitar da su? Saboda haka, su za su shari'anta ku.
23602  MAT 12:44  Sai ya ce, 'zan koma gidana inda na fito'. Bayan ya dawo, sai ya tarar da gidan nan an share shi ya zama da tsabta.
23635  MAT 13:27  Bayin mai gonar kuwa suka zo suka ce masa, maigida, ashe ba iri mai kyau ka shuka a gonarka ba? ya ya aka yi ta kasance da ciyayi?
23638  MAT 13:30  Bari dukan su su girma tare har lokacin girbi, a lokacin girbin zan gaya wa masu girbin, “Ku tuge ciyayin da farko a daura su dami dami sai a kona su, amma a tara alkamar a kai rumbunana.'”
23642  MAT 13:34  Duk wadannan abubuwa Yesu ya fada wa taron cikin misalai. Babu abinda ya fada masu da ba a cikin misali ba.
23651  MAT 13:43  Sa'an nan ne mutane masu adalci za su haskaka kamar rana a mulkin Ubansu. Bari mai kunnen ji, ya ji.
23663  MAT 13:55  Wannan mutumin ba dan masassakin nan ba ne? Ba kuma sunan mahaifiyarsa Maryamu ba? Ba Kuma 'yan'uwansa sune, Yakubu da Yusufu da Saminu da kuma Yahuza ba?
23664  MAT 13:56  Ba 'yan'uwansa mata na tare da mu ba? To daga ina wannan mutumin ya sami dukan wadannnan abubuwa?
23670  MAT 14:4  Ya ce masa,Bai kamata ka dauke ta a matsayin matarka ba.”
23674  MAT 14:8  Bayan ta amshi umurni daga wurin mahaifiyarta, ta ce, “Ka bani kan Yahaya mai baptisma a kan tire.
23678  MAT 14:12  Sai almajiransa suka zo, su ka dauki gawar su ka je su ka yi jana'iza. Bayan haka, su ka je su ka fada wa Yesu.
23682  MAT 14:16  Amma Yesu ya ce masu,Babu amfanin tafiyar su, ku basu abin da za su ci.”
23689  MAT 14:23  Bayan ya sallami taron sun tafi, sai ya haura kan dutse domin yayi addu'a. Da dare yayi, yana can shi kadai.
23694  MAT 14:28  Bitrus ya amsa masa cewa, “Ubangiji, idan kai ne, ka umarce ni in zo wurin ka bisa ruwan.”
23695  MAT 14:29  Yesu yace, “Zo” Sai Bitrus ya fita daga jirgin yana tafiya akan ruwan zuwa wurin Yesu.
23696  MAT 14:30  Amma da Bitrus ya ga iska, sai ya tsorata. Yayin da ya fara nutsewa, sai ya tada murya ya ce, “Ubangiji, ka cece ni!”
23697  MAT 14:31  Nan take Yesu ya mika hannunsa, ya kama Bitrus ya ce masa, “Kai mai karancin bangaskiya, meyasa ka yi shakka?”
23698  MAT 14:32  Bayan da Yesu da Bitrus suka shiga cikin kwale-kwalen, sai iska ta daina kadawa.
23717  MAT 15:15  Bitrus ya amsa ya ce wa Yesu, “Ka bayyana wannan misali a garemu,”
23724  MAT 15:22  Sai wata mace Bakan'aniya ta zo daga wannan yanki. Ta daga murya ta ce,” Ka yi mani jinkai, Ubangiji, Dan Dauda; 'yata tana cikin bakar azaba da aljani.”
23726  MAT 15:24  Amma Yesu ya amsa ya ce,Ba a aike ni gun kowa ba sai dai ga batattun tumakin gidan Isra'ila.”
23728  MAT 15:26  Ya amsa ya ce,Ba daidai bane a dauki gurasar yara a jefa wa kananan karnuka.
23730  MAT 15:28  Sai Yesu ya amsa ya ce mata, “Mace, bangaskiyarki tana da girma. Bari ya zamar maki yadda ki ke so.”'Yarta ta warke a lokacin.
23734  MAT 15:32  Yesu ya kira almajiransa zuwa gun sa sai ya ce, “Ina jin tausayin taron, sun kasance tare da ni kwana uku ke nan kuma ba su da abin da za su ci. Bana so in sallame su ba tare da sun ci abinci ba, domin kada su suma a hanya.”
23736  MAT 15:34  Yesu ya ce masu, “Gurasa nawa ku ke da ita?” Suka ce,Bakwai da 'yan kifi marasa yawa.”
23750  MAT 16:9  Ba ku gane ko tuna da gurasa guda biyar da aka ciyar da mutum dubu biyar, kuma kwando nawa kuka tara ba?
23757  MAT 16:16  Sai Saminu Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Almasihu, Dan Allah mai rai.”
23759  MAT 16:18  Ina kuma gaya maka cewa kai ne Bitrus, a kan wannan dutse zan gina ikilisiya ta. Kofofin hades ba za su yi nasara da ita ba.
23763  MAT 16:22  Sai Bitrus ya kai shi a gefe ya tsauta masa, cewa, “Wannan ya yi nesa da kai, Ubangiji; wannan ba zai taba faruwa da kai ba.”
23764  MAT 16:23  Amma Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Ka koma bayana, Shaidan! Kai sanadin tuntube ne gare ni, domin ba ka damuwa da abubuwan da suke na Allah, amma sai abubuwan mutane.”
23770  MAT 17:1  Bayan kwana shida Yesu ya dauki Bitrus da Yakubu, da Yahaya dan'uwansa, ya kai su kan wani dutse mai tsawo su kadai.
23773  MAT 17:4  Bitrus ya amsa ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ya yi kyau da muke a wurin nan. In kana so, zan yi bukkoki uku daya dominka, daya domin Musa, daya domin Iliya.”
23782  MAT 17:13  Sa'annan almajiransa suka fahimci cewa yana yi masu magana a kan Yahaya mai Baftisma ne.
23793  MAT 17:24  Da suka iso Kafarnahum, mutane masu karbar haraji na rabin shekel suka zo wurin Bitrus suka ce, “Malaminku na ba da rabin shekel na haraji?”
23794  MAT 17:25  Sai ya ce, “I.” Amma da Bitrus ya shiga cikin gida, Yesu ya fara magana da shi yace, “Menene tunaninka Saminu? Sarakunan duniya, daga wurin wa suke karbar haraji ko kudin fito? Daga talakawansu ko daga wurin baki?”
23795  MAT 17:26  Sai Bitrus ya ce, “Daga wurin baki,” Yesu ya ce masa, “Wato an dauke wa talakawansu biya kenan.
23817  MAT 18:21  Bitrus ya zo ya ce wa Yesu, ''Ubangiji, sau nawa ne dan'uwana zai yi mani laifi in gafarta masa? Har sai ya kai sau bakwai?''
23818  MAT 18:22  Yesu ya amsa ya ce masa, ''Ban gaya maka sau bakwai ba, amma bakwai din ma har sau saba'in.
23835  MAT 19:4  Yesu ya amsa ya ce, ''Baku karanta ba, cewa shi wanda ya yi su tun farko ya yi su miji da mace?
23842  MAT 19:11  Amma Yesu yace masu, ''Ba kowa ne zai karbi wannan koyarwa ba, amma sai wadanda an yardar masu su karbe ta.
23858  MAT 19:27  Sai Bitrus ya amsa ya ce masa, ''Duba, mun bar kome da kome mun bi ka. To me za mu samu?''
23863  MAT 20:2  Bayan sun shirya kudin da zai biya ma'aikata kimanin dinari daya a kowanne yini, sai ya aike su gonarsa suyi aiki.
23883  MAT 20:22  Amma Yesu ya amsa, ya ce, ''Baku san abin da kuke roko ba. Ko zaku iya sha daga cikin kokon da zan sha bada dadewa ba?'' Sai suka ce masa, ''Zamu iya.''
23887  MAT 20:26  Ba zai kasance haka a tsakanin ku ba. A maimakon haka, duk wanda ke da marmari ya zama da girma a tsakanin ku, ya zama baran ku.
23896  MAT 21:1  Yayinda Yesu da almajiransa suka kusato Urushalima sai suka zo Betafaji wajen dutsen zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa guda biyu,
23912  MAT 21:17  Sai Yesu ya bar su, ya fice daga birnin zuwa Betaniya ya kwana a wurin.
23922  MAT 21:27  Sai suka amsa ma Yesu suka ce, ''Bamu sani ba.” Shi ma yace masu, “Nima bazan gaya maku ko da wane iko nake yin abubuwan nan ba.
23932  MAT 21:37  Bayan wannnan, sai mai gonar ya aika da dansa wurin su yana cewa, 'za su yi wa dana biyayya.'