23214 | MAT 1:1 | Littafin asalin Yesu Almasihu Dan Dauda, Dan Ibrahim. |
23219 | MAT 1:6 | Yesse shine mahaifin sarki Dauda. Sarki Dauda shine mahaifin Sulaimanu ta wurin matar Uriya. |
23230 | MAT 1:17 | Tun daga Ibrahim zuwa Dauda, an yi tsara goma sha hudu ne, daga Dauda zuwa lokacin da aka kwashe su zuwa Babila, tsara goma sha hudu ne, sannan daga lokacin da aka kwashe su zuwa Babila zuwa Almasihu tsara goma sha hudu ne |
23233 | MAT 1:20 | Yana cikin tunanin wadannan al'amura, sai mala'ikan Ubangiji ya bayyana gareshi a mafarki, ya ce masa, “Yusufu, dan Dauda, kada ka ji tsoron daukar Maryamu a matsayin matarka. Gama abinda ke cikinta, ta wurin Ruhu Mai Tsarki aka same shi. |
23234 | MAT 1:21 | Za ta haifi Da, za ka kira sunansa Yesu, domin za ya ceci mutanensa daga zunubansu.” |
23235 | MAT 1:22 | Duk wannan ya faru ne domin a cika abinda aka fada ta bakin annabin, cewa, |
23236 | MAT 1:23 | “Duba, budurwa za ta sami juna biyu sannan za ta haifi da, za su kira sunansa Immanuel”-ma'ana, “Allah tare da mu.” |
23241 | MAT 2:3 | Da sarki Hirudus ya ji haka, sai ya damu kwarai, haka kuma dukan mutanen Urushalima. |
23248 | MAT 2:10 | Da suka ga tauraron, sai suka yi matukar farin ciki. |
23253 | MAT 2:15 | Ya zauna a can har mutuwar Hirudus. Wannan kuwa domin a cika abin da Ubangiji ya fada ne ta bakin annabin, ''Daga Masar na kirawo Da na.'' |
23254 | MAT 2:16 | Da Hirudus ya ga masanan nan sun shashantar da shi, sai ya hasala kwarai, ya aika a karkashe dukan 'yan yara maza da suke Baitalami da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa kasa, gwargwadon lokacin da ya tabbatar a gun masanan. |
23270 | MAT 3:9 | Kada kuwa ku dauka a ranku cewa, 'Ibrahim ne ubanmu.' Domin ina gaya maku, Allah yana da iko ya ta da wa Ibrahim 'ya'ya daga cikin duwatsun nan. |
23278 | MAT 3:17 | Duba, wata murya daga sammai tana cewa, ''Wannan shi ne kaunataccen Da na. Wanda ya gamshe ni sosai.'' |
23280 | MAT 4:2 | Da ya yi azumi kwana arba'in dare da rana, daga baya yunwa ta kama shi. |
23281 | MAT 4:3 | Sai mai jarabtar nan ya zo, ya ce masa, “Idan kai Dan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama gurasa.” |
23284 | MAT 4:6 | ya ce masa, “In kai Dan Allah ne, to dira kasa. Domin a rubuce yake cewa, 'Zai ba mala'ikunsa umarni game da kai,' kuma, 'Za su daga ka da hannuwansu, domin kada ka yi tuntube da dutse.''' |
23287 | MAT 4:9 | Ya ce masa, “Dukan wadannan zan baka idan ka rusuna ka yi mani sujada.'' |
23288 | MAT 4:10 | Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, Shaidan! Domin a rubuce yake, 'Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kadai za ka bauta wa.''' |
23295 | MAT 4:17 | Daga lokacin nan, Yesu ya fara wa'azi, yana cewa, “Ku tuba domin mulkin sama ya kusa.” |
23299 | MAT 4:21 | Da Yesu ya ci gaba da tafiya, sai ya ga wadansu mutum biyu, su kuma 'yan'uwa ne, Yakubu dan Zabadi, da dan'uwansa Yahaya, suna cikin jirgi tare da mahaifinsu Zabadi, suna gyaran tarunsu. Sai ya kira su. |
23303 | MAT 4:25 | Taro masu yawa suka bi shi daga kasar Galili, da Dikafolis, da Urushalima, da kasar Yahudiya, har ma daga hayin Urdun. |
23304 | MAT 5:1 | Da Yesu ya ga taron jama'ar, sai ya hau saman dutse. Sa'adda ya zauna, almajiransa suka zo wurinsa. |
23321 | MAT 5:18 | Domin gaskiya ina gaya maku, har sama da kasa su shude, amma digo ko wasali daya ba za ya shude ba a cikin shari'ar, sai an cika dukan al'amura. |
23324 | MAT 5:21 | Kun ji dai an ce wa mutanen da, 'Kada ka yi kisan kai,' kuma 'Duk wanda ya yi kisan kai yana cikin hatsarin hukunci.' |
23327 | MAT 5:24 | ka bar baikon ka a gaban bagadin, ka yi tafiyarka. Da farko dai, ka sasanta da dan'uwanka kafin ka zo ka mika baikon. |
23332 | MAT 5:29 | Idan idonka na dama zai sa ka tuntube, kwakule shi ka jefar daga gareka. Don gara daya daga cikin gabobinka ya halaka, da a jefa dukan jikin ka a jahannama. |
23333 | MAT 5:30 | Ko kuwa idan hannunka na dama zai sa ka tuntube, ka yanke shi ka jefar daga gare ka. Domin gara daya daga cikin gabobin ka ya halaka, da a jefa dukan jikinka a jahannama. |
23334 | MAT 5:31 | An sake fada, 'Duk wanda ya kori matarsa, sai ya ba ta takaddar saki.' |
23340 | MAT 5:37 | Amma bari maganarku ta zama 'I, I', ko kuwa 'A'a, a'a.' Duk abin da ya wuce wannan, daga mugun yake. |
23344 | MAT 5:41 | Duk wanda ya tilasta ku ga tafiyar mil daya, ku je da shi biyu. |
23348 | MAT 5:45 | domin ku zama 'ya'yan Ubanku da ke cikin sama. Domin yakan sa rana ta haskaka wa mugu da mutumin kirki, kuma yakan aiko da ruwan sama ga adali da azzalumi. |
23349 | MAT 5:46 | Domin idan kuna kaunar wadanda suke kaunarku, wanne lada kuka samu? Ba haka masu karban haraji ma suke yi ba? |
23359 | MAT 6:8 | Domin haka, kada ku zama kamarsu, domin Ubanku ya san bukatar ku tun kafin ku roke shi. |
23365 | MAT 6:14 | Domin in kun yafe wa mutane laifuffukansu, Ubanku na Sama shima zai yafe maku. |
23372 | MAT 6:21 | Domin inda dukiyar ka take, a nan zuciyar ka ma take. |
23380 | MAT 6:29 | Duk da haka ina gaya maku, ko Sulaimanu ma, cikin dukan daukakar sa bai yi ado kamar daya daga cikin wadannan ba. |
23382 | MAT 6:31 | Don haka kada ku damu, kuna cewa, 'Me za mu ci? ko, Me za mu sha?' ko kuwa, 'Wadanne tufafi za mu sa?' |
23386 | MAT 7:1 | Kada ku yi hukunci, domin ku ma kada a hukunta ku. Domin da irin hukuncin da ku kan hukunta da shi za a hukunta ku. |
23388 | MAT 7:3 | Don me kake duban dan hakin da ke idon dan'uwanka, amma ba ka kula da gungumen da ke naka idon ba? |
23399 | MAT 7:14 | Domin kofar zuwa rai matsattsiya ce, hanyar ta mai wuyar bi ce, masu samun ta kuwa kadan ne. |
23404 | MAT 7:19 | Duk itacen da ba ya ba da 'ya'ya masu kyau, sai a sare shi a jefa a wuta. |
23405 | MAT 7:20 | Domin haka, ta irin 'ya'yansu za a gane su. |
23410 | MAT 7:25 | Da ruwa ya sauko, ambaliyar ruwa ta zo, iska ta taso ta buga gidan, amma bai fadi ba, domin an gina shi bisa dutse. |
23414 | MAT 7:29 | Domin yana koya masu da iko, ba kamar marubuta ba. |
23415 | MAT 8:1 | Da Yesu ya sauko daga dutsen, sai taro masu yawa suka bi shi. |
23419 | MAT 8:5 | Da Yesu ya shiga kafarnahum, sai wani hafsa ya zo gunsa ya roke shi, |
23423 | MAT 8:9 | Domin ni ma ina karkashin ikon wani ne, ina kuma da sojoji a karkashina, sai in ce wa wannan, 'je ka,' sai ya je, wani kuma in ce masa, 'zo,' sai ya zo, in ce wa bawa na, 'yi abu kaza,' sai ya yi,” |
23424 | MAT 8:10 | Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki, har ya ce wa mabiyansa, “Gaskiya, ina gaya maku, ko a cikin isra'ila ban taba samun bangaskiya mai karfi irin wannan ba. |
23428 | MAT 8:14 | Da Yesu ya shiga gidan Btrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance da zazzabi. |
23430 | MAT 8:16 | Da maraice ya yi, sai mutanen suka kakkawo wa Yesu masu aljanu da yawa. Da magana kawai ya fitar da aljanun, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya. |
23434 | MAT 8:20 | Yesu ya ce masa, “Yanyawa suna da ramukansu, tsuntsayen sama kuma da shekunan su, amma Dan mutum ba shi da wurin da zai kwanta.” |
23437 | MAT 8:23 | Da Yesu ya shiga jirgi, almajiransa suka bi shi. |
23440 | MAT 8:26 | Yesu ya ce masu, “Don me kuka firgita haka, ya ku masu karancin bangaskiya?” Sa'annan ya tashi, ya tsauta wa iskar da tekun. Sai wurin gaba daya ya yi tsit. |
23442 | MAT 8:28 | Da Yesu ya zo daga wancan hayin a kasar Garasinawa, mutane biyu masu al'janu suka fito suka same shi. Suna fitowa daga makabarta kuma suna da fada sosai, har ma ba mai iya bin ta wannan hanya. |
23448 | MAT 8:34 | Sai duk jama'ar gari suka fito su sami Yesu. Da suka gan shi, suka roke shi ya bar kasarsu. |
23450 | MAT 9:2 | Sai gashi, sun kawo masa wani mutum shanyayye kwance a tabarma. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, ''Da, ka yi farin ciki. An gafarta maka zunuban ka.'' |
23452 | MAT 9:4 | Yesu kuwa da yake ya san tunaninsu, yace, ''Don me kuke mugun tunani a zuciyarku? |
23454 | MAT 9:6 | Amma domin ku sani Dan mutum yana da ikon gafarta zunubai a duniya...'' Sai ya ce wa shanyayyen, ''Tashi, ka dauki shimfidarka ka tafi gida.'' |
23456 | MAT 9:8 | Da taron suka ga haka sai suka yi mamaki, suka daukaka Allah, wanda ya ba mutane irin wannan iko. |
23457 | MAT 9:9 | Da Yesu ya yi gaba, ya ga wani mutum mai suna Matiyu a zaune, yana aiki a wurin karbar haraji. Yace masa, ''Ka biyo ni.'' Ya tashi ya bi shi. |
23459 | MAT 9:11 | Da Farisawa suka ga haka, sai suka ce wa almajiransa, ''Don me malamin ku ya ke ci tare da masu karbar haraji da masu zunubi?'' |
23462 | MAT 9:14 | Sai almajiran Yahaya suka zo wurinsa, suka ce, ''Don me mu da Farisawa mu kan yi azumi a kai a kai, amma naka almajiran ba su yi?'' |
23469 | MAT 9:21 | Domin ta ce a ran ta, ''Ko da mayafinsa ma na taba, sai in warke.'' |
23471 | MAT 9:23 | Da Yesu ya isa gidan shugaban jama'ar, ya kuma ga masu busar sarewa da taro suna ta hayaniya sosai. |
23475 | MAT 9:27 | Da Yesu ya yi gaba daga nan, sai wadansu makafi biyu suka bi shi, suna daga murya suna cewa, ''Ya Dan Dauda, ka ji tausayinmu.'' |
23476 | MAT 9:28 | Da Yesu ya shiga wani gida sai makafin suka zo gareshi. Yesu ya ce masu, “Kun gaskata ina da ikon yin haka?'' Sai suka ce masa. ''I, ya Ubangiji.'' |
23480 | MAT 9:32 | Da makafin biyu suka tafi, sai aka kawo wa Yesu wani bebe mai aljani. |
23502 | MAT 10:16 | ''Duba, na aike ku kamar tumaki a tsakiyar kyarketai, don haka sai ku zama masu wayo kamar macizai, da kuma marasa barna kamar kurciyoyi. |
23506 | MAT 10:20 | Domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhun Ubanku ne yake magana ta bakinku. |
23507 | MAT 10:21 | Dan'uwa zai ba da dan'uwansa a kashe shi, uba kuwa dansa. 'Ya'ya kuma za su tayarwa iyayensu, har su sa a kashe su. |
23509 | MAT 10:23 | In sun tsananta maku a wannan gari, ku gudu zuwa na gaba. Hakika ina gaya maku, kafin ku gama zazzaga dukan garuruwan Isra'ila, Dan Mutum zai zo. |
23511 | MAT 10:25 | Dai dai ne almajiri ya zama kamar malaminsa, bawa kuma kamar ubangijinsa. In har sun kira mai gida Ba'alzabuba, za su kuma bata mutanen gidansa! |
23512 | MAT 10:26 | Don haka kada kuji tsoron su, domin ba abin da yake boye da ba za a bayyana ba. |
23521 | MAT 10:35 | Domin na zo ne in hada mutum da ubansa gaba, 'ya da uwatarta, mata da kuma surukarta. |
23523 | MAT 10:37 | Dukan wanda ya fi son mahaifinsa ko mahaifayarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma ya fi son dansa ko 'yarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. |
23525 | MAT 10:39 | Dukan mai son ya ceci ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, yana ceton sa ne. |
23530 | MAT 11:2 | Da Yahaya mai baftisma ya ji daga kurkuku irin ayyukan da Yesu ke yi, sai ya aika sako ta wurin almajiransa. |
23538 | MAT 11:10 | Wannan shine wanda aka rubuta game da shi, 'Duba, ina aika manzona, wanda za ya tafi gabanka domin ya shirya maka hanya inda za ka bi'. |
23544 | MAT 11:16 | Da me zan kwatanta wannan zamani? Ya na kamar yara masu wasa a kasuwa, sun zauna suna kiran juna |
23547 | MAT 11:19 | Dan mutum ya zo yana ci yana sha, sai aka ce, 'Duba, ga mai hadama, mashayi kuma, abokin masu karbar haraji da masu zunubi!' Amma hikima, ta wurin aikin ta ake tabbatar da ita. |
23555 | MAT 11:27 | An mallaka mani dukan abu daga wurin Ubana. Sannan babu wanda ya san Dan, sai Uban, babu kuma wanda ya san Uban, sai Dan, da duk wanda ya so ya bayyana masa. |
23560 | MAT 12:2 | Amma da Farisawa suka gan su, sai su ka ce wa Yesu. “Duba, almajiranka su na yin abin da doka ta haramta a ranar Asabaci.” |
23561 | MAT 12:3 | Amma Yesu ya ce masu, “Baku karanta abin da Dauda ya yi ba, lokacin da ya ke jin yunwa, tare da mazan da ke tare da shi? |
23566 | MAT 12:8 | Gama Dan mutum shine Ubangijin Asabaci.” |
23568 | MAT 12:10 | Sai ga wani mutum wanda hannun sa ya shanye, sai Farisawa suka tambayi Yesu, cewa, “Doka ta halarta a yi warkarwa a ranar Asabaci?” Domin su zarge shi a kan zunubi. |
23573 | MAT 12:15 | Da Yesu ya fahimci wannan, sai ya janye kan sa daga nan. Mutane da dama su ka bi shi, ya warkar da su duka. |
23576 | MAT 12:18 | “Dubi, bawa na zababbe; kaunatacce na, wanda ya ke faranta mani raina sosai. Zan sa Ruhu na bisan sa, za ya furta hukunci zuwa al'ummai. |
23581 | MAT 12:23 | Jama'a su ka yi mamaki kwarai, su na cewa, “Ko wannan ne Dan Dawuda?” |
23583 | MAT 12:25 | Amma Yesu ya san tunanin su, sai ya ce. “Duk mulkin da ya rabu gaba da kan sa, ba zaya tsaya ba, duk wani birni da ya rabu ba zai tsaya ba, ko gida da ya tsage, za ya rushe. |