23231 | MAT 1:18 | Ga yadda haihuwar Yesu Almasihu ta kasance. Mahaifiyarsa, Maryamu, tana tashi da Yusufu, amma kafin su yi aure, sai aka same ta da juna biyu ta wurin Ruhu Mai Tsarki. |
23233 | MAT 1:20 | Yana cikin tunanin wadannan al'amura, sai mala'ikan Ubangiji ya bayyana gareshi a mafarki, ya ce masa, “Yusufu, dan Dauda, kada ka ji tsoron daukar Maryamu a matsayin matarka. Gama abinda ke cikinta, ta wurin Ruhu Mai Tsarki aka same shi. |
23260 | MAT 2:22 | Amma da ya ji Arkilayus ya gaji mahaifinsa Hirudus, yana mulkin kasar Yahudiya, sai ya ji tsoron isa can. Bayan da Allah ya yi masa gargadi a mafarki, sai ya ratse zuwa kasar Galili |
23274 | MAT 3:13 | Sai Yesu ya zo daga kasar Galili, ya je Kogin Urdun wurin Yahaya, domin ya yi masa baftisma. |
23290 | MAT 4:12 | To, da Yesu ya ji an kama Yahaya, sai ya tashi zuwa kasar Galili. |
23291 | MAT 4:13 | Ya bar Nazarat, ya koma Kafarnahum da zama, can bakin tekun Galili, kan iyakar kasar Zabaluna da Naftali. |
23293 | MAT 4:15 | “Kasar Zabaluna da kasar Naftali, ta bakin teku, da hayin Kogin Urdun, Galili ta al'ummai! |
23296 | MAT 4:18 | Yana tafiya a bakin tekun Galili, sai ya ga wadansu 'yan'uwa biyu, Saminu da ake kira Bitrus, da dan'uwansa Andarawas, suna jefa taru a teku, domin su masunta ne. |
23301 | MAT 4:23 | Yesu ya zazzaga dukan kasar Galili, yana koyarwa a majami'unsu, yana shelar bisharar mulkin, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya a cikin mutane. |
23303 | MAT 4:25 | Taro masu yawa suka bi shi daga kasar Galili, da Dikafolis, da Urushalima, da kasar Yahudiya, har ma daga hayin Urdun. |
23323 | MAT 5:20 | Gama ina gaya maku cewa idan adalcin ku bai zarce adalcin marubuta da Farisawa ba, babu yadda za ku shiga mulkin sama. |
23329 | MAT 5:26 | Gaskiya ina gaya maka, ba za ka taba fita daga can ba sai ko ka biya dukan kudin da ya ke binka. |
23353 | MAT 6:2 | Saboda haka, in za ku yi sadaka, kada ku busa kaho yadda munafukai suke yi a majami'u da kuma akan tituna domin mutane su yabesu. Gaskiya ina gaya maku, sun samu ladansu. |
23356 | MAT 6:5 | Sa'adda za ku yi addu'a kuma, kada ku zama kamar munafukai, domin sun cika son yin addu'a a tsaye a majami'unsu da kuma a gefen tituna, domin mutane su gansu. Gaskiya ina gaya maku, sun sami ladarsu kenan. |
23364 | MAT 6:13 | Kuma kada ka kawo mu cikin jaraba, amma ka kubutar da mu daga Mugun.' [Gama mulki da iko da daukaka naka ne har abada. Amin] |
23367 | MAT 6:16 | Haka kuma, in za ku yi azumi, kada ku zama da fuska kamar masu makoki yadda munafukai ke yi, domin sukan yankwane fuskokinsu, domin su bayyana ga mutane kamar suna azumi. Gaskiya, ina gaya maku, sun sami ladansu ke nan. |
23424 | MAT 8:10 | Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki, har ya ce wa mabiyansa, “Gaskiya, ina gaya maku, ko a cikin isra'ila ban taba samun bangaskiya mai karfi irin wannan ba. |
23432 | MAT 8:18 | Sa'adda Yesu ya ga taro masu yawa kewaye da shi, sai ya ba da umarni su tafi su koma wancan hayi na tekun Galili. |
23442 | MAT 8:28 | Da Yesu ya zo daga wancan hayin a kasar Garasinawa, mutane biyu masu al'janu suka fito suka same shi. Suna fitowa daga makabarta kuma suna da fada sosai, har ma ba mai iya bin ta wannan hanya. |
23485 | MAT 9:37 | Sai ya ce wa almajiransa, ''Girbin yana da yawa, amma ma'aikatan kadan ne. |
23500 | MAT 10:14 | Ga wadanda su ka ki karbar ku ko sauraron ku, idan za ku fita garin ko gidan, sai ku karkade kurar kafafunku. |
23501 | MAT 10:15 | Hakika, ina gaya maku, a ranar shari'a za a fi rangwanta wa kasar Saduma da ta Gwamrata a kan wannan birni. |
23517 | MAT 10:31 | Kada ku ji tsoro. Gama darajarku ta fi ta tsuntsaye masu yawa. |
23541 | MAT 11:13 | Gama dukan annabawa da shari'a sun yi annabci har zuwa lokacin Yahaya. |
23546 | MAT 11:18 | Gama Yahaya ya zo, baya cin gurasa ko shan ruwan inabi, sai aka ce, “Yana da aljannu”. |
23551 | MAT 11:23 | Ke kafarnahum, kina tsammani za a daukaka ki har zuwa sama? A'a za a saukar da ke kasa zuwa hades. Gama in da an yi irin al'ajiban da aka yi a cikin ki a Sodom, da tana nan har yanzu. |
23558 | MAT 11:30 | Gama karkiyata mai sauki ce, kaya na kuma ba shi da nauyi.” |
23566 | MAT 12:8 | Gama Dan mutum shine Ubangijin Asabaci.” |
23592 | MAT 12:34 | Ku 'ya'yan macizai, tun da ku miyagu ne, yaya za ku iya fadin abubuwa nagari? Gama daga cikar zuciya baki ke magana. |
23595 | MAT 12:37 | Gama ta wurin maganganun ku, za a 'yantar da ku, ta wurin maganganun ku kuma za a kashe ku.” |
23598 | MAT 12:40 | Gama yadda Yunusa ya yi kwana uku da dare uku a cikin babban kifi, haka ma Dan Mutum zaya yi kwana uku da dare uku a cikin zuciyar kasa. |
23608 | MAT 12:50 | Gama duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda ya ke cikin sama, shine dan'uwana, da 'yar'uwata da mahaifiyata.” |
23622 | MAT 13:14 | A gare su ne annabcin Ishaya ya cika, wanda yake cewa, “Game da sauraro zaku saurara, amma ba za ku fahimta ba. Game da gani kuma za ku kalla, amma ba za ku gane ba. |
23646 | MAT 13:38 | Gonar kuwa duniya ce; iri mai kyau kuma sune 'ya'yan mulkin. Ciyayin kuma sune 'ya'yan mugun, |
23647 | MAT 13:39 | magabcin da ya shuka su kuma shaidan ne. Girbin shine karshen duniya, kuma masu girbin sune mala'iku. |
23731 | MAT 15:29 | Yesu ya bar wurin ya tafi kusa da tekun Galili. Sai ya hau tudu ya zauna a can. |
23736 | MAT 15:34 | Yesu ya ce masu, “Gurasa nawa ku ke da ita?” Suka ce, “Bakwai da 'yan kifi marasa yawa.” |
23769 | MAT 16:28 | Gaskiya ina gaya maku, akwai wadansun ku da ke tsaye a nan, da ba za su dandana mutuwa ba sai sun ga Dan Mutum na zuwa cikin mulkinsa.” |
23791 | MAT 17:22 | Suna zaune a Galili, Yesu ya ce wa almajiransa, “Za a bada Dan Mutum ga hannun mutane. |
23832 | MAT 19:1 | Sai ya zama sa'adda Yesu ya gama wadannan maganganu, sai ya bar Galili ya zo kan iyakokin Yahudiya, ketaren kogin Urdun. |
23862 | MAT 20:1 | Gama mulkin sama yana kama da wani mai gona, wanda ya fita da asuba ya nemi 'yan kwadago da za su yi aiki a gonarsa. |
23875 | MAT 20:14 | Ku karbi abin da ke na ku, ku tafi. Ganin dama ta ne, in ba wadannan da suka zo a karshe daidai da ku. |
23906 | MAT 21:11 | Sai jama'a suka amsa, “Wannan shine Yesu annabi, daga Nazaret ta Galili.” |
23927 | MAT 21:32 | Gama Yahaya ya zo maku a hanyar adalci, amma ba ku gaskata da shi ba, a yayinda masu karbar haraji da karuwai suka gaskata da shi. Ku kuwa, bayan kun ga abin da ya faru, baku ma tuba daga baya ba don ku gaskata da shi. |
23955 | MAT 22:14 | Gama mutane dayawa aka kira, amma kadan aka zaba.”' |
24020 | MAT 23:33 | macizai, Ku 'ya'yan ganshekai, Yaya zaku tsere wa hukuncin Gidan wuta? |
24025 | MAT 23:38 | Ga shi an bar maku gidan ku a yashe! |
24031 | MAT 24:5 | Gama da yawa za su zo da sunana. Za su ce, “ni ne almasihu,” kuma za su sa da yawa su kauce. |
24033 | MAT 24:7 | Gama al'umma zata tayarwa al'umma, kuma mulki zai tayarwa mulki. Za'a yi yunwa da girgizar kasa a wurare dabam dabam. |
24050 | MAT 24:24 | Gama annabawan karya da almasihan karya za su zo suna nuna alamu da al'ajibai, don su yaudari masu yawa zuwa ga bata, in ya yiwuma har da zababbun. |
24083 | MAT 25:6 | Amma da tsakkar dare sai aka yi shela, 'Ga ango ya iso! Ku fito taryensa. |
24092 | MAT 25:15 | Ga wani ya ba shi talanti biyar, ga wani ya ba shi biyu, ga wani kuma ya ba shi talanti daya. kowa an bashi gwargwadon iyawarsa, sai wannan mutum ya yi tafiyar sa |
24099 | MAT 25:22 | Bawan da ya karbi talanti biyun, ya zo yace, 'Maigida, ka ba ni talanti biyu. Gashi kuwa na sami karin ribar wasu biyun.' |
24106 | MAT 25:29 | Gama ga wanda yake da shi za'a kara masa har ma a yalwace za'a kara bashi. Amma ga wanda bashi da komai abinda ke nasa ma za'a kwace. |
24112 | MAT 25:35 | Gama na ji yunwa kuka bani abinci; Na ji kishi kuka bani ruwa; Na yi bakunci kun bani masauki; |
24147 | MAT 26:24 | Dan mutum zai tafi, kamar yadda aka rubuta akan sa. Amma kaiton mutumin da ta wurin sa za'a bada Dan mutum! Gwamma da ba'a haifi mutumin nan ba.” |
24151 | MAT 26:28 | “Gama wannan jinina ne na alkawari wanda aka zubar domin gafarar zunuban mutane da yawa. |
24155 | MAT 26:32 | Amma bayan an tashe ni, zan riga ku zuwa Galili.” |
24159 | MAT 26:36 | Sa'anna Yesu ya tafi tare da su, wurin da ake kira Getsaimani sai yace wa almajiransa, ''Ku zauna a nan ni kuma zan je gaba in yi addu'a.” |
24172 | MAT 26:49 | Nan da nan ya kaiga Yesu ya ce, “Gaisuwa, Mallam!” sai ya sumbace shi. |
24192 | MAT 26:69 | To Bitrus kuwa na zaune a farfajiyar, sai wata yarinya baiwa ta zo wurinsa tana cewa, “Kaima kana tare da Yesu na Galili.” |
24231 | MAT 27:33 | Suka iso wani wuri da ake kira Golgotta, wanda ke nufin,”Wurin kwalluwa.” |
24253 | MAT 27:55 | Mata dayawa da suka bi Yesu daga Galili domin su lura da shi suka tsaya suna kallo daga nesa. |
24271 | MAT 28:7 | Ku hanzarta ku gaya wa almajiransa, 'Ya tashi daga matattu. Duba, ya tafi Galili, can zaku same shi.' Gashi ni kuwa na fada maku.” |
24274 | MAT 28:10 | Sai Yesu yace masu, “Kada ku ji tsoro. Ku je ku fada wa 'yan'uwana su je Galili. Can zasu ganni.” |
24280 | MAT 28:16 | Amma almajiran sha daya suka tafi Galili, kan dutsen da Yesu ya umarcesu. |
24293 | MRK 1:9 | Sai ya kasance a kwanakin nan Yesu ya zo daga Nazarat ta Galili, sai Yahaya ya yi masa baptisma a kogin urdun. |
24298 | MRK 1:14 | Bayan da aka kama Yahaya, Yesu ya shiga kasar Galili yana wa'azin bisharar Allah. |
24300 | MRK 1:16 | Sa'adda ya ke wucewa a gefen takun Galili, sai ya ga Saminu da Andarawus, dan'uwansa suna jefa taru a teku, domin su masunta ne. |
24312 | MRK 1:28 | Nan da nan labarinsa ya bazu ko'ina a dukkan kewayen kasar Galili. |
24323 | MRK 1:39 | Ya tafi dukan kasar Galili, yana wa'azi a majimi'un su yana kuma fitar da aljanu. |
24364 | MRK 3:7 | Sai Yesu da almajiransa, suka tafi bakin teku. sai mutane dayawa suka bi shi, daga Galili da Yahudiya |
24391 | MRK 3:34 | Sai ya waiwayi wadanda suke zaune kewaye da shi, yace, “Ga uwa-ta da yan-uwana anan! |
24392 | MRK 3:35 | Gama duk wanda ke yin abin da Allah yake so, shine dan'uwana da yar, uwata, da kuma uwa-ta.” |
24434 | MRK 5:1 | Da su ka zo daya ketaren tekun, wanda ya ke cikin yankin Garasinawa. |
24441 | MRK 5:8 | Gama Yesu ya ce masa kai aljani ka fito daga cikinsa.” |
24497 | MRK 6:21 | Amma sai dama ta samu inda Hirodiya za ta iya yin abin da ta ke so ta yi. A lokacin kewayowar ranar haihuwar sa, sai Hirudus ya shirya liyafa domin manyan da ke aiki tare da shi a cikin gwamnatin sa, da shugabannin da ke cikin Galili. |
24528 | MRK 6:52 | Gama basu gane batun dunkulen ba. Maimakon haka, sai zukatansu suka taurare. |
24558 | MRK 7:26 | Matar yar kasar Girka ce, kuma asalinta daga Fonishiya take. Ta roke shi da ya fitar da mugun ruhun nan daga diyarta. |
24563 | MRK 7:31 | Ya sake fita daga shiyar Sur, ya biyo ta Sidon, har zuwa tekun Galili a shiyar Dikafolis. |
24588 | MRK 8:19 | Da na kakkarya gurasar a cikin mutane dubu biyar, kwanduna nawa kuka samu ragowa? Suka ce masa, “Goma sha biyu.” |
24637 | MRK 9:30 | Sai suka ratsa cikin Galili, amma ba ya son kowa ya san inda suke. |
24657 | MRK 9:50 | Gishiri yana da kyau, amma idan ya rasa zakinsa, ta ya ya za ka sa shi yayi zaki kuma? Ku kasance da zaki, kuma ku yi zaman lafiya da kowa. |
24672 | MRK 10:15 | Gaskiya na ke fada maku duk mutumin da bai karbi mulkin Allah kamar karamin yaro ba, babu shakka ba zai shiga mulkin Allah ba. |
24684 | MRK 10:27 | Yesu ya dube su ya ce masu. Ga mutane a bu ne mai wuyar gaske, amma a wurin Allah komai yiwuwa ne. |
24686 | MRK 10:29 | Yesu ya ce. Gaskiya na ke fada maku, babu wanda zai bar gidansa, da yan'uwansa maza da mata, da mahaifiya ko mahaifi, ko 'ya'ya ko gona, saboda da ni da kuma bishara, |
24790 | MRK 13:4 | Gaya mana yaushe za a yi wadannan abubuwa? mecece zata zama alamar faruwar wadanna abubuwa da zasu faru?'' |
24808 | MRK 13:22 | Gama almasihan karya, da annabawan karya zasu bayyana kuma, zasu yi abubuwan al'ajibai masu ban mamaki. |
24813 | MRK 13:27 | Zai aiko da mala'ikunsa su tattaro zabbabunsa daga kusuwoyi hudu na duniya(watau Gabas da Yamma, kudu da Arewa) har zuwa karshen sama. |
24851 | MRK 14:28 | Amma bayan tashina, zai yi gaba in riga ku zuwa Galili. |
24855 | MRK 14:32 | Suka isa wani wuri da ake kira Getsamani, sai Yesu ya ce wa almajiransa “Ku dakata anan domin zan je inyi addu'a”. |
24893 | MRK 14:70 | Amma ya sake musawa, jim kadan sai na tsaitsayen suka ce wa Bitrus “Lalle kai ma dayansu ne don ba Galile ne kai”. |
24917 | MRK 15:22 | Sojojin suka kawo Yesu wurin da ake kira Golgota (wato kokon kai) |
24921 | MRK 15:26 | Sai aka rubuta alamar zargi da take cewa “Ga Sarkin Yahudawa” |
24936 | MRK 15:41 | Wadannan matan sune suka bishi sa'adda da yake Galilee suna yi masa hidima. Da wadansu mata da yawa suka zo Urushalima tare da shi. |
24949 | MRK 16:7 | Sai ku je, ku gaya wa almajiransa da Bitrus cewa ya rigaya ya yi gabanku zuwa Galili. A can zaku ganshi, kamar yadda ya fada maku.” |
24980 | LUK 1:18 | Zakariya ya ce wa mala'ikan, “Ta yaya zan san wannan? Ga shi na tsufa kuma matata tana da shekaru da yawa.” |
24988 | LUK 1:26 | A cikin watan ta na shidda, an aiki Mala'ika Jibra'ilu daga wurin Allah zuwa wani birni a Galili mai suna Nazarat, |
24999 | LUK 1:37 | Gama babu abin da ba shi yiwuwa a wurin Allah.” |