Wildebeest analysis examples for:   hau-hauulb   K    February 11, 2023 at 18:42    Script wb_pprint_html.py   by Ulf Hermjakob

23244  MAT 2:6  'Ke kuma, Baitalami, ta kasar Yahudiya, ba ke ce mafi kankanta ba a cikin shugabanin Yahudiya, domin daga cikin ki mai mulki zai fito wanda zai zama makiyayin jama'a ta Isra'ila.'''
23246  MAT 2:8  Ya aike su Baitalami, ya ce, ''Ku je ku binciko mani dan yaron da kyau. Idan kun same shi, ku kawo mani labari, don ni ma in je in yi masa sujada.”
23263  MAT 3:2  Ku tuba, domin mulkin sama ya kusa.”
23264  MAT 3:3  Wannan shine wanda annabi Ishaya ya yi maganarsa, ya ce, “Muryar wani mai kira a jeji yana cewa, 'Ku shirya wa Ubangiji hanyarsa, ku daidaita tafarkunsa.''
23266  MAT 3:5  Sai mutanen Urushalima, da na dukan Yahudiya, da na duk kasashen bakin Kogin Urdun, suka yi ta zuwa wurin sa.
23267  MAT 3:6  Ya yi masu baftisma a Kogin Urdun, yayinda suke furta zunubansu.
23268  MAT 3:7  Amma da ya ga Farisawa da Sadukiyawa da yawa, suna fitowa domin a yi masu baftisma, sai ya ce masu,Ku 'ya'yan macizai masu dafi, wa ya gargade ku ku guje wa fushi mai zuwa?
23269  MAT 3:8  Ku ba da 'ya'ya da za su nuna tubanku.
23270  MAT 3:9  Kada kuwa ku dauka a ranku cewa, 'Ibrahim ne ubanmu.' Domin ina gaya maku, Allah yana da iko ya ta da wa Ibrahim 'ya'ya daga cikin duwatsun nan.
23271  MAT 3:10  Ko yanzu ma an sa gatari a gindin bishiyoyin. Saboda haka duk bishiyar da ba ta ba da 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare ta a jefa a wuta.
23273  MAT 3:12  Kwaryar shikarsa na hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai, ya tara alkamarsa ya sa a rumbunsa, amma zai kona buntun da wutar da ba za a iya kashewa ba.”
23274  MAT 3:13  Sai Yesu ya zo daga kasar Galili, ya je Kogin Urdun wurin Yahaya, domin ya yi masa baftisma.
23285  MAT 4:7  Yesu ya ce masa,kuma a rubuce yake, 'Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.'''
23286  MAT 4:8  Kuma, sai Ibilis ya kai shi kan wani dutse mai tsawo kwarai, ya nuna masa dukan mulkokin duniya da darajarsu.
23288  MAT 4:10  Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, Shaidan! Domin a rubuce yake, 'Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kadai za ka bauta wa.'''
23291  MAT 4:13  Ya bar Nazarat, ya koma Kafarnahum da zama, can bakin tekun Galili, kan iyakar kasar Zabaluna da Naftali.
23293  MAT 4:15  Kasar Zabaluna da kasar Naftali, ta bakin teku, da hayin Kogin Urdun, Galili ta al'ummai!
23295  MAT 4:17  Daga lokacin nan, Yesu ya fara wa'azi, yana cewa,Ku tuba domin mulkin sama ya kusa.”
23297  MAT 4:19  Yesu ya ce masu,Ku zo, ku biyo ni, zan mai da ku masuntan mutane.”
23315  MAT 5:12  Ku yi murna da matukar farin ciki, domin sakamakonku mai yawan gaske ne a sama. Ta haka ne mutane suka tsananta wa annabawa da suka yi rayuwa kafin ku.
23316  MAT 5:13  Ku ne gishirin duniya, amma idan gishiri ya sane yaya za a mai da dandanonsa? Ba zai kara anfani ga komai ba, sai ko a zubar da shi, a tattake a karkashin kafafun mutane.
23317  MAT 5:14  Ku ne hasken duniya, birnin da ke kan tudu ba shi boyuwa.
23320  MAT 5:17  Kada ku yi tsammanin na zo ne domin in rushe shari'a ko annabawa. Ban zo domin in rushe su ba, amma domin in cika su.
23324  MAT 5:21  Kun ji dai an ce wa mutanen da, 'Kada ka yi kisan kai,' kuma 'Duk wanda ya yi kisan kai yana cikin hatsarin hukunci.'
23325  MAT 5:22  Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da dan'uwansa, yana cikin hatsarin hukunci. Kuma duk wanda ya ce da dan'uwansa, 'Kai mutumin banza!' yana cikin hatsarin tsayawa gaban majalisa, kowa kuma ya ce da dan'uwan sa 'Kai wawa!' yana cikin hatsarin shiga wutar jahannama.
23328  MAT 5:25  Ka yi sulhu da mai karar ka tun kana hanyar zuwa gaban shari'a, domin kada mai karar ka ya mika ka ga alkali, alkali kuwa ya mika ka ga dogarai, za a kuwa jefa ka a kurkuku.
23330  MAT 5:27  Kun dai ji an ce, 'Kada ka yi zina'.
23333  MAT 5:30  Ko kuwa idan hannunka na dama zai sa ka tuntube, ka yanke shi ka jefar daga gare ka. Domin gara daya daga cikin gabobin ka ya halaka, da a jefa dukan jikinka a jahannama.
23335  MAT 5:32  Amma ina gaya maku ko wa ya saki matarsa, idan ba a kan laifin lalata ba, ya mai da ita mazinaciya kenan. Kuma duk wanda ya aure ta bayan sakin, ya yi zina kenan.
23336  MAT 5:33  Kun sake ji an ce wa wadan da suke a zamanin da, 'Kada ku yi rantsuwar karya, amma ku yi rantsuwar ku ga Ubangiji.'
23339  MAT 5:36  Ko ma ace ku yi rantsuwa da kanku, domin ba za ku iya mai da gashin kanku baki ko fari ba.
23341  MAT 5:38  Kun dai ji an ce, “Ido a maimakon ido, hakori kuma a maimakon hakori.'
23345  MAT 5:42  Ku ba kowa da ya tambaye ku, kuma kada ku hana kowa da ke neman rance a wurinku.
23346  MAT 5:43  Kun ji abin da aka fada, 'Za ka kaunaci makwabcin ka ka ki magabcin ka.'
23350  MAT 5:47  Kuma in kun gaida 'yan'uwanku kadai, me kuke yi fiye da sauran? Ba hakanan al'ummai ma suke yi ba?
23352  MAT 6:1  Ku yi hankali kada ku yi ayyukan adalcinku gaban mutane domin su ganku, idan kun yi haka, ba za ku sami sakamako a wurin Ubanku da yake sama ba.
23357  MAT 6:6  Amma ku, idan za ku yi addu'a, sai ku shiga cikin daki. Ku rufe kofa, ku yi addu'a ga Ubanku wanda yake a asirce, Ubanku kuwa da ke ganin abin da ake yi a asirce, zai saka maku.
23362  MAT 6:11  Ka ba mu yau abincinmu na kullum.
23363  MAT 6:12  Ka gafarta mana basussukanmu, kamar yadda mu ma muke gafarta ma wadanda muke bi bashi.
23364  MAT 6:13  Kuma kada ka kawo mu cikin jaraba, amma ka kubutar da mu daga Mugun.' [Gama mulki da iko da daukaka naka ne har abada. Amin]
23369  MAT 6:18  don kada mutane su gane kuna azumi, sai dai Ubanku da yake a asirce. Kuma Ubanku da ke ganin abinda ke a asirce, zai saka maku.”
23370  MAT 6:19  Kada ku tara wa kanku dukiya a duniya, inda asu da tsatsa ke batawa, inda barayi kuma ke fasawa su yi sata.
23377  MAT 6:26  Ku dubi tsuntsayen da ke sararin sama. Ai, ba su shuka, balle girbi, ba su kuma tarawa a cikin rumbuna, amma Ubanku na Sama na ciyar da su. Ashe, ba ku fi su martaba ba?
23378  MAT 6:27  Kuma wanene a cikinku, don damuwarsa, zai iya kara ko taki ga tsawon rayuwarsa?
23379  MAT 6:28  To, don me kuke damuwa a kan tufafi? Ku dubi furannin jeji, yadda suke girma. Ba su aiki, kuma ba su sakar kaya.
23385  MAT 6:34  “Saboda haka kada ku damu don gobe, ai, gobe za ta damu da kanta. Kowace rana ta na cike da wahalarta”.
23386  MAT 7:1  Kada ku yi hukunci, domin ku ma kada a hukunta ku. Domin da irin hukuncin da ku kan hukunta da shi za a hukunta ku.
23389  MAT 7:4  Ko kuwa yaya za ka iya ce wa dan'uwanka, 'Bari in cire maka dan hakin da ke idon ka,' alhali ga gungume a cikin naka idon?
23390  MAT 7:5  Kai munafiki! Ka fara cire gungumen da ke idonka, sa'annan za ka iya gani sosai yadda za ka cire dan hakin da ke idon dan'uwanka.
23391  MAT 7:6  Kada ku ba karnuka abin da ke tsattsarka. Kada kuma ku jefa wa aladu, lu'u lu'anku. Idan ba haka ba za su tattake su a karkashin sawunsu, su kuma juyo su kekketa ku.
23392  MAT 7:7  Roka, kuma za a ba ku. Nema, kuma za ku samu. Kwankwasa kuma za a bude maku.
23394  MAT 7:9  Ko, kuwa wane mutum ne a cikin ku, dan sa zai roke shi gurasa, ya ba shi dutse?
23395  MAT 7:10  Ko kuwa in ya roke shi kifi, zai ba shi maciji?
23398  MAT 7:13  Ku shiga ta matsattsiyar kofa, don kofar zuwa hallaka na da fadi, hanyar ta mai saukin bi ce, masu shiga ta cikin ta suna da yawa.
23400  MAT 7:15  Ku kula da annabawan karya, wadanda su kan zo maku da siffar tumaki, amma a gaskiya kyarketai ne masu warwashewa.
23403  MAT 7:18  Kyakkyawan itace ba zai taba haifar da munanan 'ya'ya ba, haka kuma mummunan itace ba zai taba haifar da kyawawan 'ya'ya ba.
23408  MAT 7:23  Sa'annan zan ce masu 'Ni ban taba saninku ba! Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!'
23418  MAT 8:4  Yesu ya ce masa, 'Ka tabbata, ba ka gaya wa kowa komai ba. Sai dai ka je ka nuna kan ka ga firist, ka kuma bayar da baiko da Musa ya umarta domin shaida garesu?
23443  MAT 8:29  Sai suka kwala ihu suka ce, “Ina ruwanka da mu, kai dan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?”
23457  MAT 9:9  Da Yesu ya yi gaba, ya ga wani mutum mai suna Matiyu a zaune, yana aiki a wurin karbar haraji. Yace masa, ''Ka biyo ni.'' Ya tashi ya bi shi.
23469  MAT 9:21  Domin ta ce a ran ta, ''Ko da mayafinsa ma na taba, sai in warke.''
23472  MAT 9:24  Sai ya ce, ''Ku ba da wuri, ai, yarinyar ba matacciya take ba, barci ta ke yi.'' Sai suka yi masa dariyar raini.
23476  MAT 9:28  Da Yesu ya shiga wani gida sai makafin suka zo gareshi. Yesu ya ce masu,Kun gaskata ina da ikon yin haka?'' Sai suka ce masa. ''I, ya Ubangiji.''
23478  MAT 9:30  Sai idanunsu suka bude. Amma Yesu ya umarce su kwarai, ya ce, ''Kada fa kowa ya ji labarin nan.''
23481  MAT 9:33  Bayan da an fitar da aljanin, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki, su ka ce, ''Kai, ba a taba ganin irin wannan a cikin Isra'ila ba!''
23491  MAT 10:5  Sha biyun nan su ne Yesu ya aika, ya yi masu umarni ya ce, ''Kada ku shiga wajen al'ummai, ko kuma kowane garin Samariyawa.
23494  MAT 10:8  Ku warkar da marasa lafiya, ku tada matattu, ku tsarkake kutare, ku kuma fitar da aljanu. Kyauta kuka samu ku ma ku bayar kyauta.
23495  MAT 10:9  Kada ku rike zinariya, ko azurfa, ko tagulla a jakarku.
23496  MAT 10:10  Kada kuma ku dauki zabira a tafiyarku, ko taguwa biyu, ko takalma, ko sanda, don ma'aikaci ya cancanci abincin sa.
23497  MAT 10:11  Kowanne birni, ko kauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a cikinsa, ku kuma zauna a wurin har lokacin da za ku tashi.
23503  MAT 10:17  Ku yi hankali da mutane, don za su kai ku gaban majalisa, su kuma yi maku bulala a majami'unsu.
23508  MAT 10:22  Kowa kuma zai ki ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har karshe, zai tsira.
23514  MAT 10:28  Kada ku ji tsoron masu kisan jikin mutum, amma ba sa iya kashe rai. Sai dai ku ji tsoron wannan da yake da ikon kashe jiki ya kuma jefa rai cikin jahannama.
23517  MAT 10:31  Kada ku ji tsoro. Gama darajarku ta fi ta tsuntsaye masu yawa.
23520  MAT 10:34  ''Kada ku zaci na zo ne in kawo salama a duniya. Ban zo domin in kawo salama ba, sai dai takobi.
23528  MAT 10:42  Kowa ya ba daya daga cikin 'yan kananan nan, ko da kofin ruwan sanyi ya sha, domin shi almajirina ne, hakika, Ina gaya maku, ba zai rasa ladarsa ba.''
23531  MAT 11:3  Ya ce masa.Kai ne mai zuwa”? ko mu sa ido ga wani.
23532  MAT 11:4  Yesu ya amsa ya ce masu,Ku je ku gaya wa Yahaya abin da ku ka gani da abin da ku ka ji.
23534  MAT 11:6  Kuma mai albarka ne wanda baya tuntube sabili da ni.
23549  MAT 11:21  Kaiton ki Korasinu, kaiton ki Batsaida! In da an yi irin ayuka masu ban mamaki a Taya da Sidon! Yadda aka yi a cikinku, da tuni sun tuba suna sanye da tsumma da yafa toka.
23551  MAT 11:23  Ke kafarnahum, kina tsammani za a daukaka ki har zuwa sama? A'a za a saukar da ke kasa zuwa hades. Gama in da an yi irin al'ajiban da aka yi a cikin ki a Sodom, da tana nan har yanzu.
23556  MAT 11:28  Ku zo gare ni, dukanku masu wahala da fama da nauyin kaya, ni kuma zan ba ku hutawa.
23557  MAT 11:29  Ku dauki karkiya ta ku koya daga gare ni, gama ni mai tawali'u ne da saukin hali a zuciya, sannan zaku sami hutawa ga rayukanku.
23581  MAT 12:23  Jama'a su ka yi mamaki kwarai, su na cewa,Ko wannan ne Dan Dawuda?”
23587  MAT 12:29  Kuma ta yaya mutum za ya shiga gidan mai karfi ya kwashe masa kaya ba tare da ya fara daure shi ba? Sa'annan ne za ya iya satar masa kaya daga gidansa.
23591  MAT 12:33  Ko dai a mai da itace mai kyau 'ya'yansa kuma su yi kyau, ko a mai da itace marar kyau 'ya'yansa kuma marasa kyau, gama ana sanin itace ta wurin 'ya'yansa.
23592  MAT 12:34  Ku 'ya'yan macizai, tun da ku miyagu ne, yaya za ku iya fadin abubuwa nagari? Gama daga cikar zuciya baki ke magana.
23600  MAT 12:42  Sarauniyar Kudu za ta tashi da mutanen wannan zamani ta kuma kashe su. Ta zo daga karshen duniya domin ta ji hikimar Sulaimanu, kuma duba, wanda ya fi Sulaimanu yana nan.
23606  MAT 12:48  Amma Yesu ya amsa ya ce wa shi wanda ya gaya masa, “Wacece mahaifiyata? Kuma su wanene 'yan'uwana?”
23615  MAT 13:7  Wasu irin kuwa suka fada a cikin kayayuwa. Kayayuwan kuwa suka shake su.
23621  MAT 13:13  Saboda haka na yi masu magana cikin misalai, amma ko da ya ke sun gani, duk da haka ba su gani ba. Kuma ko da yake sun ji, hakika ba su ji ba, balle ma su fahimta.
23626  MAT 13:18  Ku saurari misalin nan na mai shuka.