Wildebeest analysis examples for:   hau-hauulb   M    February 11, 2023 at 18:42    Script wb_pprint_html.py   by Ulf Hermjakob

23223  MAT 1:10  Hezekiya shine mahaifin Manassa, Manassa shine mahaifin Amon, sannan Amon shine mahaifin Yosiya.
23228  MAT 1:15  Aliyudu shine mahaifin Ali'azara, Ali'azara shine mahaifin Matana, sannan Matana shine mahaifin Yakubu.
23229  MAT 1:16  Yakubu shine mahaifin Yusufu maigidan Maryamu, wadda ta wurin ta ne aka haifi Yesu, wanda ake ce da shi Almasihu.
23231  MAT 1:18  Ga yadda haihuwar Yesu Almasihu ta kasance. Mahaifiyarsa, Maryamu, tana tashi da Yusufu, amma kafin su yi aure, sai aka same ta da juna biyu ta wurin Ruhu Mai Tsarki.
23232  MAT 1:19  Mijinta, Yusufu, adalin mutum ne, amma ba ya so ya kunyatar da ita a sarari. Sai ya yi shawara ya sake ta a asirce.
23233  MAT 1:20  Yana cikin tunanin wadannan al'amura, sai mala'ikan Ubangiji ya bayyana gareshi a mafarki, ya ce masa, “Yusufu, dan Dauda, kada ka ji tsoron daukar Maryamu a matsayin matarka. Gama abinda ke cikinta, ta wurin Ruhu Mai Tsarki aka same shi.
23240  MAT 2:2  ''Ina wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Mun ga tauraronsa a gabas mun kuma zo mu yi masa sujada.''
23249  MAT 2:11  Sai suka shiga gidan, suka ga dan yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka rusuna gabansa suka yi masa sujada. Sa'an nan suka kwance kayansu, suka mika masa kyautar su ta zinariya da lubban, da mur.
23251  MAT 2:13  Bayan sun tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, ''Tashi, ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu zuwa kasar Masar, ka zauna a can sai na fada maka, don Hirudus yana shirin binciko dan yaron ya hallaka shi.”
23252  MAT 2:14  A wannan dare fa Yusufu ya tashi ya dauki dan yaron da mahafiyarsa ya tafi Masar.
23253  MAT 2:15  Ya zauna a can har mutuwar Hirudus. Wannan kuwa domin a cika abin da Ubangiji ya fada ne ta bakin annabin, ''Daga Masar na kirawo Da na.''
23257  MAT 2:19  Sa'adda Hirudus ya mutu, sai ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki a Masar ya ce,
23262  MAT 3:1  A kwanakin nan Yahaya Mai baftisma ya zo, yana wa'azi a jejin Yahudiya yana cewa,
23264  MAT 3:3  Wannan shine wanda annabi Ishaya ya yi maganarsa, ya ce,Muryar wani mai kira a jeji yana cewa, 'Ku shirya wa Ubangiji hanyarsa, ku daidaita tafarkunsa.''
23272  MAT 3:11  Na yi maku baftisma da ruwa, zuwa tuba. Amma mai zuwa baya na, ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in dauka ba. Shi ne zai yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta.
23294  MAT 4:16  Mutane mazauna duhu suka ga babban haske, sannan ga wadanda ke zaune a yankin da inuwar mutuwa, haske ya keto masu.”
23314  MAT 5:11  Masu albarka ne ku sa'adda mutane suka zage ku, suka kuma tsananta maku, ko kuwa suka zarge ku da dukan miyagun abubuwa iri iri na karya, saboda ni.
23318  MAT 5:15  Mutane ba za su kunna fitila su sa ta karkashin kwando ba, sai ko a dora ta a mazaunin ta, domin ta ba da haske ga kowa da ke gidan.
23364  MAT 6:13  Kuma kada ka kawo mu cikin jaraba, amma ka kubutar da mu daga Mugun.' [Gama mulki da iko da daukaka naka ne har abada. Amin]
23371  MAT 6:20  Maimakon haka, ku tara wa kanku dukiya a sama, inda babu asu da tsatsa da za su bata, inda kuma ba barayi da za su fasa su yi sata.
23382  MAT 6:31  Don haka kada ku damu, kuna cewa, 'Me za mu ci? ko, Me za mu sha?' ko kuwa, 'Wadanne tufafi za mu sa?'
23387  MAT 7:2  Mudun da kukan auna, da shi za a auna maku.
23401  MAT 7:16  Za ku gane su ta irin ''ya'yansu. Mutane na cirar inabi a jikin kaya, ko kuwa baure a jikin sarkakkiya?
23418  MAT 8:4  Yesu ya ce masa, 'Ka tabbata, ba ka gaya wa kowa komai ba. Sai dai ka je ka nuna kan ka ga firist, ka kuma bayar da baiko da Musa ya umarta domin shaida garesu?
23433  MAT 8:19  Sai wani marubuci ya zo ya ce masa, Malam, zan bi ka duk inda za ka je.”
23441  MAT 8:27  Mutanen suka yi al'ajibi, suka ce, “Wanne irin mutum ne wannan, wanda har iska da teku ma suke masa biyayya?”.
23447  MAT 8:33  Mutanen masu kiwon aladun suka gudu, suka shiga gari, suka yi ta ba da labarin komai da komai, musamman abin da ya faru da masu al'janun.
23455  MAT 9:7  Mutumin kuwa ya tashi ya tafi gida.
23457  MAT 9:9  Da Yesu ya yi gaba, ya ga wani mutum mai suna Matiyu a zaune, yana aiki a wurin karbar haraji. Yace masa, ''Ka biyo ni.'' Ya tashi ya bi shi.
23463  MAT 9:15  Sai Yesu ya ce masu, ''Masu hidimar buki za su yi bakin ciki tun ango yana tare da su? Ai, lokaci yana zuwa da za a dauke masu angon. A sa'annan ne fa za su yi azumi.''
23465  MAT 9:17  Mutane kuma ba su dura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. Idan sun yi haka, sai salkunan kuma su fashe inabin ya tsiyaye, sai salkunan su lalace. A maimakon haka, ana sa sabon inabi cikin sababbin salkuna, ta haka an tsirar da duka biyun kenan.''
23489  MAT 10:3  Filibus, da Bartalamawus, da Toma da Matiyu mai karbar haraji da Yakubu dan Halfa, da Taddawus;
23493  MAT 10:7  Sa'adda kuna tafiya, kuna wa'azi, kuna cewa, 'Mulkin Sama ya kusato'.
23509  MAT 10:23  In sun tsananta maku a wannan gari, ku gudu zuwa na gaba. Hakika ina gaya maku, kafin ku gama zazzaga dukan garuruwan Isra'ila, Dan Mutum zai zo.
23533  MAT 11:5  Makafi suna samun ganin gari, guragu na tafiya, ana tsarkake kutare, kurame na jin magana kuma, ana tada matattu, mabukata kuma ana ba su bishara.
23535  MAT 11:7  Bayan wadannan sun tafi, sai Yesu ya fara wa jama'a jawabi game da Yahaya mai baftisma, yana cewa,Me ake zuwa gani a jeji - ciyawa ce da iska ke busawa?
23571  MAT 12:13  Sai Yesu ya ce wa mutumin nanMika hannun ka.” Ya mike hannunsa, sai hannun nan ya dawo lafiyaye kamar dayan hannunsa.
23573  MAT 12:15  Da Yesu ya fahimci wannan, sai ya janye kan sa daga nan. Mutane da dama su ka bi shi, ya warkar da su duka.
23582  MAT 12:24  Amma da Farisawa su ka ji wannan al'ajibi, sai su ka ce,Mutumin nan yana fitar da aljannu ta wurin Bahalzabuba sarkin aljannu ne.”
23589  MAT 12:31  Saboda haka ina ce maku, kowanne zunubi da sabo, za a gafarta wa mutum, amma sabon Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta shi ba.
23590  MAT 12:32  Duk wanda yayi batanci ga Dan Mutum, za a gafarta masa. Amma duk wanda yayi batanci game da Ruhu Mai Tsarki ba za a gafarta masa ba, a nan duniya da har abada.
23593  MAT 12:35  Mutumin kirki daga ajiyar zuciyarsa ya kan fitar da abubuwa masu kyau, mugun mutum kuma daga mummunar ajiyar zuciyarsa ya kan fitar da abubuwan mugunta.
23596  MAT 12:38  Sa'annan wadansu Malaman Attaura, da Farisawa suka amsa suka ce wa Yesu,Mallam, muna so mu ga wata alama daga gare ka.”
23597  MAT 12:39  Amma Yesu ya amsa ya ce masu, Mugun zamani da mazinaciyar tsara, su na bukutar alama. Amma babu alamar da za a ba su, sai dai alamar annabi Yunusa.
23598  MAT 12:40  Gama yadda Yunusa ya yi kwana uku da dare uku a cikin babban kifi, haka ma Dan Mutum zaya yi kwana uku da dare uku a cikin zuciyar kasa.
23599  MAT 12:41  Mutanen Nineba za su tsaya a ranar shari'a da wannan zamani sannan su kashe su. Domin sun tuba da suka ji wa'azin Yunusa, amma duba wanda ya fi Yunusa yana nan.
23636  MAT 13:28  Ya ce masu, Magabci ne ya yi wannan”. Sai bayin suka ce masa, 'kana so mu je mu tuge su ne?'
23637  MAT 13:29  Mai gonar ya ce, 'A'a, kada a garin tuge ciyayin, ku tuge tare da alkamar.
23645  MAT 13:37  Yesu ya amsa kuma ya ce, “Shi wanda ya shuka iri mai kyau Dan Mutum ne.
23649  MAT 13:41  Dan Mutum zai aiki mala'ikunsa, kuma su tara dukan abubuwan da ke sa zunubi daga cikin mulkinsa, da kuma wadanda su ka yi aikin mugunta.
23652  MAT 13:44  Mulkin sama kamar dukiya ce da ke boye a gona. Mutum ya samu sai ya boye ta, ya tafi cikin murna, ya sayar da mallakarsa kuma ya sayi filin.
23657  MAT 13:49  Haka zai kasance a karshen duniya. Mala'iku za su zo su ware miyagu daga cikin masu adalci.
23663  MAT 13:55  Wannan mutumin ba dan masassakin nan ba ne? Ba kuma sunan mahaifiyarsa Maryamu ba? Ba Kuma 'yan'uwansa sune, Yakubu da Yusufu da Saminu da kuma Yahuza ba?
23683  MAT 14:17  Suka ce masa, Muna da gurasa guda biyar da kifi biyu ne kawai.”
23704  MAT 15:2  Meyasa almajiranka suke karya al'adar dattawa? Don ba su wanke hannayen su kafin su ci abinci.”
23730  MAT 15:28  Sai Yesu ya amsa ya ce mata, Mace, bangaskiyarki tana da girma. Bari ya zamar maki yadda ki ke so.”'Yarta ta warke a lokacin.
23741  MAT 15:39  Sai Yesu ya sallami taron ya shiga cikin jirgin ruwa ya tafi yankin Magadan.
23745  MAT 16:4  Mugun zamani, maciya amana suna neman alama, amma babu wata alama da za a nuna sai ta Yunusa.” Daga nan sai Yesu ya tafi.
23754  MAT 16:13  A lokacin da Yesu ya zo yankin Kaisariya Filibbi, ya tambayi almajiransa, cewa, “Wa mutane ke cewa Dan Mutum yake?
23758  MAT 16:17  Yesu ya amsa ya ce masa, Mai albarka ne kai, Saminu dan Yunusa, don ba nama da jini ba ne ya bayyana maka wannan, amma Ubana wanda ke cikin sama.
23767  MAT 16:26  Domin wace riba mutum zai samu in ya sami dukan duniya ya rasa ransa? Me mutum zai iya bayarwa a maimakon ransa?
23768  MAT 16:27  Domin Dan Mutum zai zo ne cikin daukakar Ubansa tare da mala'ikunsa. Sa'annan ne zaya biya kowane mutum bisa ga ayyukansa.
23769  MAT 16:28  Gaskiya ina gaya maku, akwai wadansun ku da ke tsaye a nan, da ba za su dandana mutuwa ba sai sun ga Dan Mutum na zuwa cikin mulkinsa.”
23772  MAT 17:3  Sai ga Musa da Iliya sun bayyana garesu suna magana da shi.
23773  MAT 17:4  Bitrus ya amsa ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ya yi kyau da muke a wurin nan. In kana so, zan yi bukkoki uku daya dominka, daya domin Musa, daya domin Iliya.”
23778  MAT 17:9  Yayin da suke saukowa daga dutsen, Yesu ya umarce su, ya ce, “Kada ku fadawa kowa wannan wahayin, sai Dan Mutum ya tashi daga matattu.”
23781  MAT 17:12  Amma ina gaya maku, Iliya ya riga ya zo, amma ba su gane shi ba. A maimakon haka, suka yi masa abin da suka ga dama. Ta irin wanan hanya, Dan Mutum kuma zai sha wuya a hannunsu.
23786  MAT 17:17  Yesu ya amsa ya ce,Marasa bangaskiya da karkataccen zamani, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan jure da ku? Ku kawo shi nan a wurina.”
23788  MAT 17:19  Sai almajiran suka zo wurin Yesu a asirce suka ce,Me ya sa muka kasa fitar da shi?”
23789  MAT 17:20  Yesu ya ce masu, “Saboda karancin bangaskiyarku. Domin hakika, ina gaya maku, in kuna da bangaskiya ko da kamar kwayar mastad, za ku ce wa wannan dutse, 'Matsa daga nan ka koma can,' zai kuwa matsa kuma ba abin da zai gagare ku.
23791  MAT 17:22  Suna zaune a Galili, Yesu ya ce wa almajiransa, “Za a bada Dan Mutum ga hannun mutane.
23793  MAT 17:24  Da suka iso Kafarnahum, mutane masu karbar haraji na rabin shekel suka zo wurin Bitrus suka ce,Malaminku na ba da rabin shekel na haraji?”
23794  MAT 17:25  Sai ya ce, “I.” Amma da Bitrus ya shiga cikin gida, Yesu ya fara magana da shi yace,Menene tunaninka Saminu? Sarakunan duniya, daga wurin wa suke karbar haraji ko kudin fito? Daga talakawansu ko daga wurin baki?”
23807  MAT 18:11  [Dan Mutum ya zo ya ceci abinda ya bata].
23808  MAT 18:12  Menene tunaninku? Idan mutum na da tumaki dari, sa'annan daya ta bata, ashe ba zai bar tassa'in da tara a gefen tudu ya tafi neman wadda ta bata ba?
23822  MAT 18:26  Sai baran ya fadi kasa, ya rusuna a gaban ubangidansa ya ce,Maigida, kayi mani hakuri, zan biya duk abin da na karba.”
23838  MAT 19:7  Sai suka ce masa, ''To me yasa Musa ya umarcemu mu bada takardar saki, mu kuma kore ta?''
23839  MAT 19:8  Sai ya ce masu, ''Saboda taurin zuciyarku, shi yasa Musa ya yarda maku ku saki matanku, amma da farko ba haka yake ba.
23847  MAT 19:16  Sai wani mutum ya zo wurin Yesu, ya ce, ''Malam, wanne ayyuka nagari ne zan yi domin in sami rai madawwami?''
23848  MAT 19:17  Yesu ya ce masa, ''Me yasa kake tambaya ta game da abin da ke nagari? Daya ne kawai ke nagari, amma idan kana so ka shiga cikin rai, ka kiyaye dokokin.''
23849  MAT 19:18  Mutumin ya ce masa, ''Wadanne dokokin?'' Yesu ya ce masa, ''Kada kayi kisa, kada kayi zina, kada kayi sata, kada kayi shaidar zur,
23851  MAT 19:20  Saurayin nan ya ce masa, ''Ai na kiyaye duk wadannan. Me nake bukata kuma?''
23859  MAT 19:28  Yesu ya ce masu, ''Hakika ina gaya maku, ku da kuka bi ni, a sabuwar haihuwa, lokacin da Dan Mutum ya zauna a kursiyin daukakarsa, ku ma zaku zauna a kursiyoyi goma sha biyu, kuna shari'anta kabilu goma sha biyu na Isra'ila.
23864  MAT 20:3  Misalin sa'a ta uku sai ya sake fita, sai ya ga wasu ma'aikata suna tsaye a bakin kasuwa, babu aiki.
23867  MAT 20:6  Ya kuma sake yin haka a sa'a ta sha daya, da ya fita sai ya ga wasu a tsaye da ba sa yin kome. Sai ya ce masu, 'Me yasa kuke tsaye ba ku yin kome dukan yini?'
23879  MAT 20:18  “Ku duba fa, zamu tafi Urushalima, kuma za a bada Dan Mutum ga manyan firistoci da marubuta. Za su kuma yanke masa hukuncin kisa,
23882  MAT 20:21  Yesu ya ce mata, Me kike so in yi maki?'' Sai ta ce masa, ''Ina so ka ba 'ya'yana izinin zama a mulkinka, daya a hannun damanka, daya kuma a hannun hagunka.
23893  MAT 20:32  Sai Yesu ya tsaya cik, ya sa aka kira su, sai ya ce masu, ''Me kuke so in yi maku?''
23943  MAT 22:2  Mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya shirya wa dansa liyafar aure.
23953  MAT 22:12  Sai sarkin ya ce masa, 'Aboki, ta yaya ka shigo nan ba tare da kayan aure ba?' Mutumin kuwa ya rasa ta cewa.
23957  MAT 22:16  Suka tura masa almajiransu, da Hirudiyawa. Suka ce ma Yesu,Mallam, mun san kai mai gaskiya ne, kuma kana koyar da hanyar Ubangiji da gaskiya. Ba ka damu da ra'ayin kowa ba, kuma ba ka nuna bambanci a tsakanin mutane.
23965  MAT 22:24  cewa,Mallam, Musa yace, 'Idan mutum ya mutu, bashi da 'ya'ya, dole dan'uwansa ya auri matarsa ya kuwa haifawa dan'uwansa 'ya'ya.
23971  MAT 22:30  Domin a tashin matattu basu aure, ba kuma a bada su aure. Maimaikon haka, suna kama da mala'ikun sama.