23216 | MAT 1:3 | Yahuza shine mahaifin Farisa da Zera, ta wurin Tamar. Farisa kuma shine mahaifin Hasruna, Hasruna kuma shine mahaifin Aram. |
23230 | MAT 1:17 | Tun daga Ibrahim zuwa Dauda, an yi tsara goma sha hudu ne, daga Dauda zuwa lokacin da aka kwashe su zuwa Babila, tsara goma sha hudu ne, sannan daga lokacin da aka kwashe su zuwa Babila zuwa Almasihu tsara goma sha hudu ne |
23231 | MAT 1:18 | Ga yadda haihuwar Yesu Almasihu ta kasance. Mahaifiyarsa, Maryamu, tana tashi da Yusufu, amma kafin su yi aure, sai aka same ta da juna biyu ta wurin Ruhu Mai Tsarki. |
23233 | MAT 1:20 | Yana cikin tunanin wadannan al'amura, sai mala'ikan Ubangiji ya bayyana gareshi a mafarki, ya ce masa, “Yusufu, dan Dauda, kada ka ji tsoron daukar Maryamu a matsayin matarka. Gama abinda ke cikinta, ta wurin Ruhu Mai Tsarki aka same shi. |
23251 | MAT 2:13 | Bayan sun tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, ''Tashi, ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu zuwa kasar Masar, ka zauna a can sai na fada maka, don Hirudus yana shirin binciko dan yaron ya hallaka shi.” |
23258 | MAT 2:20 | ''Tashi ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka tafi kasar Isra'ila, domin masu neman ran dan yaron sun mutu.'' |
23272 | MAT 3:11 | Na yi maku baftisma da ruwa, zuwa tuba. Amma mai zuwa baya na, ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in dauka ba. Shi ne zai yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta. |
23288 | MAT 4:10 | Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, Shaidan! Domin a rubuce yake, 'Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kadai za ka bauta wa.''' |
23290 | MAT 4:12 | To, da Yesu ya ji an kama Yahaya, sai ya tashi zuwa kasar Galili. |
23303 | MAT 4:25 | Taro masu yawa suka bi shi daga kasar Galili, da Dikafolis, da Urushalima, da kasar Yahudiya, har ma daga hayin Urdun. |
23315 | MAT 5:12 | Ku yi murna da matukar farin ciki, domin sakamakonku mai yawan gaske ne a sama. Ta haka ne mutane suka tsananta wa annabawa da suka yi rayuwa kafin ku. |
23379 | MAT 6:28 | To, don me kuke damuwa a kan tufafi? Ku dubi furannin jeji, yadda suke girma. Ba su aiki, kuma ba su sakar kaya. |
23431 | MAT 8:17 | Ta haka kuwa maganar annabi Ishaya ta samu cika cewa, “Shi da kansa ya debe rashin lafiyar mu, ya dauke cututtukan mu.” |
23444 | MAT 8:30 | To akwai wani garken aladu masu yawa na kiwo, babu nisa da su. |
23446 | MAT 8:32 | “Yesu ya ce masu, “To, ku je.” Sai aljanun suka fita, suka shiga cikin aladun. Sai kuwa duk garken suka rugungunta ta gangaren, suka fada cikin tekun, suka hallaka a ruwa. |
23453 | MAT 9:5 | Wanne ya fi sauki, a ce, 'An gafarta maka zunubanka,' ko kuwa a ce, 'Tashi ka yi tafiya'? |
23454 | MAT 9:6 | Amma domin ku sani Dan mutum yana da ikon gafarta zunubai a duniya...'' Sai ya ce wa shanyayyen, ''Tashi, ka dauki shimfidarka ka tafi gida.'' |
23488 | MAT 10:2 | To yanzu ga sunayen manzanin nan goma sha biyu. Na farkon shine, Saminu, wanda ake kira Bitrus, da dan'uwansa Andarawas, da Yakubu dan Zabadi, da dan'uwansa Yahaya; |
23489 | MAT 10:3 | Filibus, da Bartalamawus, da Toma da Matiyu mai karbar haraji da Yakubu dan Halfa, da Taddawus; |
23540 | MAT 11:12 | Tun daga kwanakin Yahaya mai baftisma zuwa yanzu, mulkin sama yana shan gwagwarmaya, masu husuma kuma su kan kwace shi da karfi. |
23549 | MAT 11:21 | “Kaiton ki Korasinu, kaiton ki Batsaida! In da an yi irin ayuka masu ban mamaki a Taya da Sidon! Yadda aka yi a cikinku, da tuni sun tuba suna sanye da tsumma da yafa toka. |
23550 | MAT 11:22 | Amma zai zama da sauki a kan Taya da Sidon a ranar shari'a fiye da ku. |
23589 | MAT 12:31 | Saboda haka ina ce maku, kowanne zunubi da sabo, za a gafarta wa mutum, amma sabon Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta shi ba. |
23590 | MAT 12:32 | Duk wanda yayi batanci ga Dan Mutum, za a gafarta masa. Amma duk wanda yayi batanci game da Ruhu Mai Tsarki ba za a gafarta masa ba, a nan duniya da har abada. |
23600 | MAT 12:42 | Sarauniyar Kudu za ta tashi da mutanen wannan zamani ta kuma kashe su. Ta zo daga karshen duniya domin ta ji hikimar Sulaimanu, kuma duba, wanda ya fi Sulaimanu yana nan. |
23610 | MAT 13:2 | Taro mai yawan gaske kuwa suka kewaye shi, sai ya shiga cikin kwalekwale ya zauna. Dukan taron kuwa na tsaye a bakin tekun. |
23664 | MAT 13:56 | Ba 'yan'uwansa mata na tare da mu ba? To daga ina wannan mutumin ya sami dukan wadannnan abubuwa? |
23708 | MAT 15:6 | wannan mutum ba ya bukatar ya girmama mahaifinsa. Ta wannan hanya kun maida maganar Allah wofi saboda al'adunku. |
23723 | MAT 15:21 | Sai Yesu ya tafi daga nan ya nufi yankin biranen Taya da Sidon. |
23724 | MAT 15:22 | Sai wata mace Bakan'aniya ta zo daga wannan yanki. Ta daga murya ta ce,” Ka yi mani jinkai, Ubangiji, Dan Dauda; 'yata tana cikin bakar azaba da aljani.” |
23729 | MAT 15:27 | Ta ce, “I, Ubangiji, amma ko kananan karnuka suna cin barbashin da ke fadowa daga teburin maigida.” |
23732 | MAT 15:30 | Taro mai yawa suka zo gunsa. Suka kawo masa guragu, makafi, bebaye da nakasassun mutane da yawa, da wadansu marasa lafiya. Suka kawo su gaban Yesu, sai ya warkar da su. |
23781 | MAT 17:12 | Amma ina gaya maku, Iliya ya riga ya zo, amma ba su gane shi ba. A maimakon haka, suka yi masa abin da suka ga dama. Ta irin wanan hanya, Dan Mutum kuma zai sha wuya a hannunsu. |
23833 | MAT 19:2 | Taro mai yawa suka bi shi, ya kuma warkar da su a wurin. |
23838 | MAT 19:7 | Sai suka ce masa, ''To me yasa Musa ya umarcemu mu bada takardar saki, mu kuma kore ta?'' |
23858 | MAT 19:27 | Sai Bitrus ya amsa ya ce masa, ''Duba, mun bar kome da kome mun bi ka. To me za mu samu?'' |
23881 | MAT 20:20 | Sai uwar 'ya'yan Zabadi ta zo wurin Yesu tare da 'ya'yanta. Ta rusuna a gabansa tana neman alfarma a wurinsa. |
23904 | MAT 21:9 | Taron jama'a da suke gabansa da wadanda suke bayansa, suka ta da murya suna cewa, “Hossana ga dan Dauda! mai albarka ne shi wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji. Hossana ga Ubangiji!” |
23935 | MAT 21:40 | To idan me gonar ya zo, me zai yiwa manoman? |
23958 | MAT 22:17 | To gaya mana, menene tunaninka? Ya halarta a biya haraji ga Kaisar ko a'a?” |
23962 | MAT 22:21 | Suka ce masa, “Na Kaisar.” Sai Yesu ya ce masu, “To ku ba Kaisar abubuwan dake na Kaisar, Allah kuma abubuwan dake na Allah.” |
23969 | MAT 22:28 | To a tashin matattu, matar wa zata zama a cikin su bakwai din? Don duk sun aure ta.” |
23984 | MAT 22:43 | Yesu yace masu, “To ta yaya kuma Dauda cikin Ruhu ya kira shi Ubangiji, yana cewa, |
24071 | MAT 24:45 | To wanene amintaccen bawannan mai hikima, wanda maigidan sa ya sa ya kula mar da gida, domin ya ba su abinci a kan lokaci? |
24082 | MAT 25:5 | To da angon ya makara, dukkan su sai suka fara gyangyadi sai barci ya dauke su. |
24086 | MAT 25:9 | “Amma masu hikimar suka ce 'Tun da man ba zai ishe mu tare da ku ba, sai ku je gun ma su sayarwa ku sayo wa kanku. |
24096 | MAT 25:19 | To bayan tsawon lokaci sai ubangidan barorin nan ya dawo, domin yayi lissafin kudinsu. |
24104 | MAT 25:27 | To da ba sai ka kai kudina a banki ba, da bayan na dawo da sai in karbi abina da riba. |
24133 | MAT 26:10 | Amma da yake Yesu ya san tunaninsu, sai yace masu, “Don me kuke damun matar nan? Ta yi abu mai kyau domina. |
24140 | MAT 26:17 | To a rana ta fari na idin ketarewa almajiran suka zo wurin Yesu suka ce, ''Ina kake so mu shirya maka da zaka ci abincin idin ketarewa?” |
24171 | MAT 26:48 | To mutumin da zai bada Yesu ya rigaya ya basu alama, cewa, ''Duk wanda na sumbata, shine. Ku kama shi.'' |
24192 | MAT 26:69 | To Bitrus kuwa na zaune a farfajiyar, sai wata yarinya baiwa ta zo wurinsa tana cewa, “Kaima kana tare da Yesu na Galili.” |
24213 | MAT 27:15 | To lokacin bikin idi, al'adar gwamna ne ya saki mutum guda wanda jama'a suka zaba. |
24215 | MAT 27:17 | To da suka tattaru, sai Bilatus yace masu, “Wa kuke so a sakar maku? Barabbas, ko Yesu wanda ake kira Almasihu?” |
24239 | MAT 27:41 | Ta haka ma manyan firistocin suka rika yi masa ba'a, tare da marubuta da shugabannin, suna cewa, |
24241 | MAT 27:43 | Tun da ya yarda da Allah. Bari Allahn ya cece shi mana, saboda yace, “Ni dan Allah ne.” |
24243 | MAT 27:45 | To tun da tsakar rana sai duhu ya rufe kasar gaba daya har karfe uku na yamma. |
24283 | MAT 28:19 | Sai kuje ku almajirantar da dukan al'ummai. Kuna yi masu baftisma cikin sunan Uba da na Da da na Ruhu Mai Tsarki. |
24292 | MRK 1:8 | Ni ina yi maku baptisma da ruwa, amma mai zuwa a bayana zai yi maku baptisma da Ruhu Mai Tsarki''. |
24308 | MRK 1:24 | Yana cewa Ina ruwan mu da kai, Yesu Banazarat? Ka zo ne domin ka halakar da mu? Na san wanene kai. Kai ne Mai Tsarki na Allah”. |
24365 | MRK 3:8 | Daga Urushalima da Edom gaba da Urdun da kewayan Taya da Sidon, da baban taro, ya ji abinda yake yi. suka zo wurinsa. |
24375 | MRK 3:18 | da Andarawus da Filibus da Bartalamawus da Matta da Toma da Yakubu dan Halfa, da Taddawus da Saminu Ba-kananiye, |
24377 | MRK 3:20 | Sa'adda ya shiga gida, Taron kuwa ya sake haduwa, har ya hana su cin abinci, |
24386 | MRK 3:29 | amma fa duk wanda yayi sabon Ruhun Mai Tsarki baza a gafarta masa ba ko kadan, ya zama mai zunubi har abada.” |
24389 | MRK 3:32 | Taro kuwa na zaune kewaye da shi, sai suka yi magana da shi da cewa, ga uwarka da yan-uwanka suna nan a waje, suna nemanka.” |
24459 | MRK 5:26 | Ta sha wahala kwarai da gaske ta je wurin likitoci da yawa ta kashe kudi sosai, amma ba ta warke ba abin ma sai karuwa ya ke yi. |
24460 | MRK 5:27 | Ta ji labarin Yesu. Sai ta biyo bayansa yana tafiya cikin taro, ta taba habar rigarsa. |
24474 | MRK 5:41 | Ya kama hannun yarinyar ya ce da ita “Tilatha koum” wato yarinya na ce ki tashi” |
24558 | MRK 7:26 | Matar yar kasar Girka ce, kuma asalinta daga Fonishiya take. Ta roke shi da ya fitar da mugun ruhun nan daga diyarta. |
24562 | MRK 7:30 | Ta koma gida sai ta iske diyarta na kwance akan gado, aljanin ya fice daga jikinta. |
24628 | MRK 9:21 | Yesu ya tambayi mahaifin yaron, Tun yaushe wannan abu ya same shi? Mahaifin yaron ya ce tun yana karami. |
24703 | MRK 10:46 | Sa'adda suka iso Yariko, yana fita daga Yariko kenan, shi da almajiransa, da wani babban taro, sai ga wani makaho mai bara, mai suna Bartimawas dan Timawas yana zaune a gefen hanya. |
24740 | MRK 11:31 | Sai suka yi mahuwara da juna, suka ce, “in kuwa muka ce, 'daga sama take,' za ya ce, “To, don me ba ku gaskata shi ba? |
24751 | MRK 12:9 | To, me mai gonar inabin zai yi? Sai ya zo ya hallaka manoman nan, ya ba wadansu gonar. |
24762 | MRK 12:20 | To an yi wadansu 'yan'uwa maza guda bakwai, na farko ya yi aure, ya mutu bai bar 'ya'ya ba. |
24765 | MRK 12:23 | To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Don duk bakwai din nan sun aure ta”. |
24778 | MRK 12:36 | Domin Dauda kansa, ta ikon Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ubangiji ya ce wa Ubangijina, zauna a hannun damana, har sai na kaskantar da makiyanka'. |
24779 | MRK 12:37 | Dauda da kansa ya kira shi 'Ubangiji; To, ta yaya ya Almasihu zai zama Dan Dauda?” Babban taron jama'ar suka saurare shi da murna. |
24807 | MRK 13:21 | To, in wani ya ce maku, kun ga Almasihu nan!' ko, 'kun gan shi can, kada ku gaskata. |
24811 | MRK 13:25 | Taurari za su fado daga sararin sama, za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama. |
24821 | MRK 13:35 | To, ku zauna a fadake don ba ku san lokacin da maigidan zai zo ba, ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko da carar zakara ne, ko da safe ne. |
24884 | MRK 14:61 | Amma yayi shiru abinsa, bai ce kome ba. Sai babban firist din ya sake tambayarsa “To, ashe kai ne Allmasihu Dan Madaukaki? |
24965 | LUK 1:3 | Sabili da haka, ni ma, bayan da na yi bincike da kyau akan yanayin wadannan abubuwa tun da farko na ga ya yi kyau in rubuta wadannan abubuwa bi da bi ya mafi girmaTiyofilas. |
24977 | LUK 1:15 | Domin zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba zai sha ruwan inabi ba ko wani abu mai sa maye, kuma zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun daga cikin cikin mahaifiyarsa. |
24980 | LUK 1:18 | Zakariya ya ce wa mala'ikan, “Ta yaya zan san wannan? Ga shi na tsufa kuma matata tana da shekaru da yawa.” |
24986 | LUK 1:24 | Bayan kwanakin nan, matarsa Alisabatu ta samu juna biyu. Ta boye kanta har na watani biyar. Ta ce, |
25000 | LUK 1:38 | Maryamu ta ce, “To, ni baiwar Ubangiji ce. Bari ya faru da ni bisa ga sakonka.” Sai mala'ikan ya bar ta. |
25002 | LUK 1:40 | Ta shiga gidan Zakariya ta kuma gai da Alisabatu. |
25003 | LUK 1:41 | Ya zama sa'adda Alisabatu ta ji gaisuwar Maryamu, sai dan da ke cikinta ya yi tsalle, an cika Alisabatu kuma da Ruhu Mai Tsarki. |
25004 | LUK 1:42 | Ta daga murya, ta ce, “Mai albarka kike a cikin mata, kuma mai albarka ne dan cikinki. |
25011 | LUK 1:49 | Domin shi madaukaki ya yi mani manyan abubuwa, kuma sunansa Mai Tsarki ne. |
25027 | LUK 1:65 | Tsoro ya kama dukan wadanda suke zama kewaye da su. Sai labarin ya bazu cikin dukan kasar duwatsu ta Yahudiya. |
25028 | LUK 1:66 | Kuma dukan wadanda suka ji su, sun ajiye su a cikin zuciyarsu, suna cewa, “To me wannan yaro zai zama ne?” Domin hannun Ubangiji yana nan tare da shi. |
25049 | LUK 2:7 | Ta haifi da, dan farinta kuwa, ta nade shi da kyau da 'yan tsummoki. Ta sa shi cikin wani kwami na dabbobi, gama babu daki dominsu a masaukin. |
25078 | LUK 2:36 | Wata annabiya mai suna Annatu ta na nan wurin. Ita diyar Fanuyila ce daga kabilar Ashiru. Ta riga ta manyanta a shekaru sosai. Ta kasance da maigidanta shekaru bakwai bayan auren ta, |
25080 | LUK 2:38 | A dadai lokacin nan, ta hau zuwa wurinsu ta fara yi wa Allah godiya. Ta gaya wa dukan wadanda ke jiran fansar Urushalima. |
25095 | LUK 3:1 | A cikin shekara ta goma sha biyar da Tibariyus Kaisar ke mulki, Bilatus Babunti kuma ke jagorar Yahudiya, Hirudus yana sarautar Galili, dan'uwansa Filibus yana sarautar yankin Ituriya da Tirakonitis, Lisaniyas kuma na sarautar yankin Abiliya, |