23244 | MAT 2:6 | 'Ke kuma, Baitalami, ta kasar Yahudiya, ba ke ce mafi kankanta ba a cikin shugabanin Yahudiya, domin daga cikin ki mai mulki zai fito wanda zai zama makiyayin jama'a ta Isra'ila.''' |
23254 | MAT 2:16 | Da Hirudus ya ga masanan nan sun shashantar da shi, sai ya hasala kwarai, ya aika a karkashe dukan 'yan yara maza da suke Baitalami da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa kasa, gwargwadon lokacin da ya tabbatar a gun masanan. |
23264 | MAT 3:3 | Wannan shine wanda annabi Ishaya ya yi maganarsa, ya ce, “Muryar wani mai kira a jeji yana cewa, 'Ku shirya wa Ubangiji hanyarsa, ku daidaita tafarkunsa.'' |
23270 | MAT 3:9 | Kada kuwa ku dauka a ranku cewa, 'Ibrahim ne ubanmu.' Domin ina gaya maku, Allah yana da iko ya ta da wa Ibrahim 'ya'ya daga cikin duwatsun nan. |
23282 | MAT 4:4 | Amma Yesu ya amsa ya ce masa, “A rubuce yake cewa, 'Ba da gurasa kadai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace magana da ta ke fitowa daga wurin Allah.''' |
23284 | MAT 4:6 | ya ce masa, “In kai Dan Allah ne, to dira kasa. Domin a rubuce yake cewa, 'Zai ba mala'ikunsa umarni game da kai,' kuma, 'Za su daga ka da hannuwansu, domin kada ka yi tuntube da dutse.''' |
23285 | MAT 4:7 | Yesu ya ce masa, “kuma a rubuce yake, 'Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.''' |
23288 | MAT 4:10 | Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, Shaidan! Domin a rubuce yake, 'Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kadai za ka bauta wa.''' |
23324 | MAT 5:21 | Kun ji dai an ce wa mutanen da, 'Kada ka yi kisan kai,' kuma 'Duk wanda ya yi kisan kai yana cikin hatsarin hukunci.' |
23325 | MAT 5:22 | Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da dan'uwansa, yana cikin hatsarin hukunci. Kuma duk wanda ya ce da dan'uwansa, 'Kai mutumin banza!' yana cikin hatsarin tsayawa gaban majalisa, kowa kuma ya ce da dan'uwan sa 'Kai wawa!' yana cikin hatsarin shiga wutar jahannama. |
23330 | MAT 5:27 | Kun dai ji an ce, 'Kada ka yi zina'. |
23334 | MAT 5:31 | An sake fada, 'Duk wanda ya kori matarsa, sai ya ba ta takaddar saki.' |
23336 | MAT 5:33 | Kun sake ji an ce wa wadan da suke a zamanin da, 'Kada ku yi rantsuwar karya, amma ku yi rantsuwar ku ga Ubangiji.' |
23346 | MAT 5:43 | Kun ji abin da aka fada, 'Za ka kaunaci makwabcin ka ka ki magabcin ka.' |
23360 | MAT 6:9 | Saboda haka sai ku yi addu'a kamar haka: 'Ubanmu da ke sama, bari a tsarkake sunanka. |
23382 | MAT 6:31 | Don haka kada ku damu, kuna cewa, 'Me za mu ci? ko, Me za mu sha?' ko kuwa, 'Wadanne tufafi za mu sa?' |
23389 | MAT 7:4 | Ko kuwa yaya za ka iya ce wa dan'uwanka, 'Bari in cire maka dan hakin da ke idon ka,' alhali ga gungume a cikin naka idon? |
23408 | MAT 7:23 | Sa'annan zan ce masu 'Ni ban taba saninku ba! Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!' |
23418 | MAT 8:4 | Yesu ya ce masa, 'Ka tabbata, ba ka gaya wa kowa komai ba. Sai dai ka je ka nuna kan ka ga firist, ka kuma bayar da baiko da Musa ya umarta domin shaida garesu? |
23423 | MAT 8:9 | Domin ni ma ina karkashin ikon wani ne, ina kuma da sojoji a karkashina, sai in ce wa wannan, 'je ka,' sai ya je, wani kuma in ce masa, 'zo,' sai ya zo, in ce wa bawa na, 'yi abu kaza,' sai ya yi,” |
23453 | MAT 9:5 | Wanne ya fi sauki, a ce, 'An gafarta maka zunubanka,' ko kuwa a ce, 'Tashi ka yi tafiya'? |
23461 | MAT 9:13 | Sai ku fahimci ma'anar wannan tukuna, 'Ni kam, ina bukatar jinkai ba hadaya ba.' Ba domin in kira masu adalci su tuba na zo ba, sai dai masu zunubi. |
23466 | MAT 9:18 | Yesu kuwa yana cikin yi masu magana sai ga wani shugaban jama'a ya zo ya yi masa sujada, ya ce, ''Yanzun nan 'yata ta rasu, amma ka zo ka dora mata hannu, za ta rayu.'' |
23493 | MAT 10:7 | Sa'adda kuna tafiya, kuna wa'azi, kuna cewa, 'Mulkin Sama ya kusato'. |
23515 | MAT 10:29 | Ba 'yan tsuntsaye biyu ake sayarwa akan kobo ba? Ba ko daya a cikin su da zai fadi kasa ba tare da yardar Ubanku ba. |
23521 | MAT 10:35 | Domin na zo ne in hada mutum da ubansa gaba, 'ya da uwatarta, mata da kuma surukarta. |
23523 | MAT 10:37 | Dukan wanda ya fi son mahaifinsa ko mahaifayarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma ya fi son dansa ko 'yarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. |
23528 | MAT 10:42 | Kowa ya ba daya daga cikin 'yan kananan nan, ko da kofin ruwan sanyi ya sha, domin shi almajirina ne, hakika, Ina gaya maku, ba zai rasa ladarsa ba.'' |
23565 | MAT 12:7 | In da kun san ma'anar wannan 'Na fi son jinkai fiye da hadaya,' da baku shari'anta wa marar laifi ba. |
23595 | MAT 12:37 | Gama ta wurin maganganun ku, za a 'yantar da ku, ta wurin maganganun ku kuma za a kashe ku.” |
23602 | MAT 12:44 | Sai ya ce, 'zan koma gidana inda na fito'. Bayan ya dawo, sai ya tarar da gidan nan an share shi ya zama da tsabta. |
23619 | MAT 13:11 | Yesu ya amsa ya ce masu, “An baku 'yanci ku fahimci asiran mulkin sama, amma gare su ba a bayar ba. |
23636 | MAT 13:28 | Ya ce masu, “Magabci ne ya yi wannan”. Sai bayin suka ce masa, 'kana so mu je mu tuge su ne?' |
23706 | MAT 15:4 | Domin Allah ya ce, 'Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka; 'Shi wanda ya yi muguwar magana ga mahaifinsa ko mahaifiyarsa, lallai zai mutu. |
23724 | MAT 15:22 | Sai wata mace Bakan'aniya ta zo daga wannan yanki. Ta daga murya ta ce,” Ka yi mani jinkai, Ubangiji, Dan Dauda; 'yata tana cikin bakar azaba da aljani.” |
23736 | MAT 15:34 | Yesu ya ce masu, “Gurasa nawa ku ke da ita?” Suka ce, “Bakwai da 'yan kifi marasa yawa.” |
23743 | MAT 16:2 | Amma ya amsa ya ce masu, “Lokacin da yamma ta yi, sai ku ce, 'Za a yi yanayi mai kyau, domin sama ta yi ja,' |
23744 | MAT 16:3 | Kuma da safe ku ce, 'Zai zama yanayi mara kyau a yau, domin sama ta yi ja ta kuma gama gari, kun san yadda za ku bayyana kammanin sararin sama, amma ba ku iya bayyana alamun lokaci ba. |
23789 | MAT 17:20 | Yesu ya ce masu, “Saboda karancin bangaskiyarku. Domin hakika, ina gaya maku, in kuna da bangaskiya ko da kamar kwayar mastad, za ku ce wa wannan dutse, 'Matsa daga nan ka koma can,' zai kuwa matsa kuma ba abin da zai gagare ku. |
23802 | MAT 18:6 | Amma duk wanda ya sa daya daga cikin 'yan yaran nan da suka gaskanta da ni zunubi, gwamma a rataya dutsen nika a wuyansa a jefa shi cikin zurfin teku. |
23824 | MAT 18:28 | Amma bayan an saki wannan baran, ya je ya sami wani baran kamar sa da yake bi bashin dinari dari. Ya cafke shi, ya shake shi a wuya, ya ce, 'Ka biya bashin da nake bin ka.' |
23862 | MAT 20:1 | Gama mulkin sama yana kama da wani mai gona, wanda ya fita da asuba ya nemi 'yan kwadago da za su yi aiki a gonarsa. |
23865 | MAT 20:4 | Sai ya ce masu, 'Kuzo kuyi aiki a gonar, duk abinda ya wajaba, zan ba ku,' Sai suka tafi su yi aikin. |
23867 | MAT 20:6 | Ya kuma sake yin haka a sa'a ta sha daya, da ya fita sai ya ga wasu a tsaye da ba sa yin kome. Sai ya ce masu, 'Me yasa kuke tsaye ba ku yin kome dukan yini?' |
23868 | MAT 20:7 | Sai suka ce masa, 'Ai babu wanda ya dauke mu aiki, shi yasa.' Sai ya ce masu, 'ku ma, kuje cikin gonar. |
23869 | MAT 20:8 | Da yamma ta yi, sai mai gonar ya ce wa manajansa, 'Ka kira ma'aikatan nan ka biya su hakkin su, amma ka fara da wadanda suka zo a karshe, zuwa na farkon.' |
23873 | MAT 20:12 | Suka ce, 'Wadannan da suka zo a karshe, sa'a guda ce kadai suka yi aiki, amma ka ba su daidai da mu, mu da muka yi fama da aiki cikin zafin rana.' |
23874 | MAT 20:13 | Amma mai gonar ya amsa wa daya daga cikin su, ya ce, 'Aboki na, ban yi maku laifi ba. Ai mun shirya zan biya ku yadda ake biya a yini, ko ba haka ba? |
23898 | MAT 21:3 | Idan wani ya gaya maku wani abu game da haka, sai ku ce, 'Ubangiji ne yake bukatarsu,' mutumin kuwa zai aiko ku da su nan da nan.” |
23908 | MAT 21:13 | Ya ce masu, “A rubuce yake, 'Za a kira gidana gidan addu'a,' amma kun mayar dashi kogon 'yan fashi.” |
23911 | MAT 21:16 | Suka ce masa, kana jin abinda wadannan mutanen ke fadi?'' Yesu ya ce masu, “I! Amma ba ku taba karantawa ba, 'daga bakin jarirai da masu shan mama ka sa yabo'?” |
23920 | MAT 21:25 | Daga ina baftismar Yahaya ta fito, daga sama ko kuma daga mutune?” Sai suka yi shawara a tsakanin su, suka ce, “In munce, 'daga sama,' zai ce mana, 'don me bamu gaskanta dashi ba?' |
23924 | MAT 21:29 | Yaron ya amsa yace, 'bazan yi ba,' amma daga baya ya canza tunaninsa ya tafi. |
23932 | MAT 21:37 | Bayan wannnan, sai mai gonar ya aika da dansa wurin su yana cewa, 'za su yi wa dana biyayya.' |
23933 | MAT 21:38 | Amma da manoman suka ga dan, sai suka ce a tsakanin su, 'wannan shine magajin. Kuzo, mu kashe shi mu gaji gonar.' |
23937 | MAT 21:42 | Yesu yace masu, “Baku taba karantawa a nassi ba,'' 'Dutsen da magina suka ki ya zama dutse mafi amfani. Wannan daga Ubangijine, kuma abin mamaki ne a idanunmu?' |
23949 | MAT 22:8 | Sai ya ce wa bayinsa, 'An gama shirya bikin, amma wadanda aka gayyata ba su cancanta ba. |
23954 | MAT 22:13 | Sai sarkin ya ce wa bayinsa, 'Ku daure mutumin nan hannu da kafa, ku jefa shi cikin duhun, inda za ayi kuka da cizon hakora.' |
23965 | MAT 22:24 | cewa, “Mallam, Musa yace, 'Idan mutum ya mutu, bashi da 'ya'ya, dole dan'uwansa ya auri matarsa ya kuwa haifawa dan'uwansa 'ya'ya. |
23973 | MAT 22:32 | 'Nine Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku, da Allah na Yakubu'? Allah ba Allah na matattu bane, amma na rayayyu.” |
23980 | MAT 22:39 | Doka ta biyu kuma kamar ta take- 'Ka kaunaci makwabcinka kamar kanka.' |
24005 | MAT 23:18 | Kuma, 'Kowa ya rantse da bagadi, ba komai bane. Amma duk wanda ya rantse da baikon da aka dora a kai, sai rantsuwarsa ta kama shi.' |
24017 | MAT 23:30 | Kuna cewa, 'Da muna nan a zamanin Ubanninmu, da bamu basu goyon baya ba wajen zubar da jinin annabawa.' |
24024 | MAT 23:37 | Urushalima, Urushalima, keda kika kashe annabawa kika kuma jejjefi wadanda aka turo maki da duwatsu! Sau nawa ne naso in tattaro ki kamar yadda kaza take tattara 'yan tsakinta cikin fukafukanta, amma kin ki. |
24026 | MAT 23:39 | Ina dai gaya maku, ba za ku kara gani na ba, sai ran da kuka ce, 'Albarka ta tabbata ga mai zuwa cikin sunan Ubangiji.”' |
24083 | MAT 25:6 | Amma da tsakkar dare sai aka yi shela, 'Ga ango ya iso! Ku fito taryensa. |
24085 | MAT 25:8 | Wawayen su ka ce da masu hikimar, 'Ku sammana kadan daga manku gama fitilunmu su na mutuwa.' |
24086 | MAT 25:9 | “Amma masu hikimar suka ce 'Tun da man ba zai ishe mu tare da ku ba, sai ku je gun ma su sayarwa ku sayo wa kanku. |
24088 | MAT 25:11 | Bayan dan lokaci kadan sauran budurwan suka dawo suna cewa, 'Mai gida, mai gida, bude mana kofar.' |
24089 | MAT 25:12 | Amma ya amsa ya ce, 'A gaskiya ina gaya maku, ni ban san ku ba.' |
24111 | MAT 25:34 | Sa'annan sarkin zai ce wa na hannun damarsa, 'Ku zo ku da Ubana ya albarkata, ku gaji mulkin da aka shirya maku kafin a kafa duniya. |
24117 | MAT 25:40 | Sa'annan Sarkin zai amsa masu yace, 'Hakika Ina gaya maku, duk abinda kuka yi wa daya mafi kakanta daga cikin 'yan'uwana a nan ni kuka yi wa.' |
24118 | MAT 25:41 | Sa'annan zai cewa wadanda suke hannunsa na hagu, 'Ku rabu da ni, ku la'anannu, ku tafi cikin wutar jahannama da aka shirya wa Shaidan da aljannunsa, |
24122 | MAT 25:45 | Sa'annan zai amsa ya ce masu, 'Ina gaya maku hakika abin da baku iya yiwa mafi karanta daga cikin wadannan ba, ba ku yi mani ba.' |
24141 | MAT 26:18 | Yace, “Ku shiga cikin birnin zaku sami wani mutum sai kuce masa, 'Mallam yace, “lokaci na ya kusa. Zan ci idin ketarewa a gidanka, da almajiraina.”''' |
24182 | MAT 26:59 | A wannan lokaci manyan firistoci da duk 'yan majalisar suka fara neman shaidar karya akan Yesu, domin su samu su kashe shi. |
24236 | MAT 27:38 | An gicciye shi da 'yanfashi guda biyu, daya ta damansa dayan kuma ta hagunsa. |
24242 | MAT 27:44 | Hakan nan ma 'yanfashin guda biyu da aka gicciye su tare suka zage shi. |
24271 | MAT 28:7 | Ku hanzarta ku gaya wa almajiransa, 'Ya tashi daga matattu. Duba, ya tafi Galili, can zaku same shi.' Gashi ni kuwa na fada maku.” |
24338 | MRK 2:9 | Me yafi sauki a cewa shanyayyen mutumin, 'An gafarta maka zunuban ka' ko kwa a ce masa, 'tashi, ka dauki shinfidarka, ka yi tafiyarka'? |
24479 | MRK 6:3 | Wannan ba kafintan nan ba ne dan Maryamu, dan'uwan Yakubu da Yosi da Yahuza da Saminu? Ba ga 'yan'uwan sa 'yan mata mu na tare da su ba? Ba su ji dadi ba a ransu saboda Yesu. |
24538 | MRK 7:6 | Amma ya amsa masu cewa, “Ishaya ya yi anabci akan ku masu bautan ganin ido, da ya rubuta cewa 'wadanan mutane suna girmama ni a baka amma zuciyar su tana nesa da ni. |
24543 | MRK 7:11 | Amma kun ce, 'idan mutum ya ce wa iyayensa, “duk taimakon da ya cacanci ku samu daga guna ya zama kebabbe (wato, 'na mika wa Allah)”'. |
24550 | MRK 7:18 | Sai Yesu yace, 'ashe baku da ganewa? ko baku sani cewa abin da ya shiga cikin mutum daga waje ba zai iya gurbatar da shi ba, |
24597 | MRK 8:28 | Suka amsa masa suka ce, Yahaya mai Baftisma. Wasu suka ce, “Iliya”. wadansu kuma, 'Daya daga cikin anabawa”. |
24663 | MRK 10:6 | Amman tun daga farkon halitta, 'Allah ya halicci namiji da ta mata.' |
24712 | MRK 11:3 | In wani ya ce maku, “Don me kuke haka? ku ce, 'Ubangiji ne yake bukatarsa, zai kuma komo da shi nan da nan.”' |
24724 | MRK 11:15 | Suka iso Urushalima, da shigar su, ya kori masu saye da sayarwa, ya watsar da taburan 'yan canjin kudi, da kujerun masu sayar da tantabaru. |
24740 | MRK 11:31 | Sai suka yi mahuwara da juna, suka ce, “in kuwa muka ce, 'daga sama take,' za ya ce, “To, don me ba ku gaskata shi ba? |
24749 | MRK 12:7 | Amma manoman nan suka ce wa juna, “ai, wannan shine magajinsa, 'ku zo mu kashe shi, gadon ya zama namu.” |
24771 | MRK 12:29 | Yesu ya amsa yace, “ mafi girma shine, 'ku saurara ya Isra'ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji daya ne. |
24773 | MRK 12:31 | ta biyu itace, 'ka kaunaci makwabcinka kamar kanka, Ba wata doka da ta fi wadannan.'' |
24807 | MRK 13:21 | To, in wani ya ce maku, kun ga Almasihu nan!' ko, 'kun gan shi can, kada ku gaskata. |
24878 | MRK 14:55 | Sai, manyan firistoci da duk 'yan majalisa Yahudawa suka nemi shaidar da za a tabbatar a kan Yesu, don su samu su kashe shi. Amma basu samu ba. |
25049 | LUK 2:7 | Ta haifi da, dan farinta kuwa, ta nade shi da kyau da 'yan tsummoki. Ta sa shi cikin wani kwami na dabbobi, gama babu daki dominsu a masaukin. |
25054 | LUK 2:12 | Wannan itace alama da za a ba ku. Za ku ga dan jariri nade cikin 'yan tsummoki kwance cikin kwamin dabbobi.” |
25066 | LUK 2:24 | Suka kuma zo su mika hadaya bisa ga yadda aka fada a shari'ar Ubangiji, “Kurciyoyi biyu ko 'yan tantabaru biyu.” |
25098 | LUK 3:4 | Kamar yadda aka rubuta a cikin littafin annabi Ishaya, “Ga muryan wani yana kira a cikin jeji, 'Shirya hanyar Ubangiji, ka daidaita tafarkunsa! |
25102 | LUK 3:8 | Ku ba da 'ya'ya da sun cancanci tuba, kada ku kuma fara cewa a cikinku, 'Muna da Ibrahim a matsayin Ubanmu', domin ina gaya maku, Allah yana iya ta da wa Ibrahim 'ya'ya daga cikin wadannan duwatsu. |
25136 | LUK 4:4 | Yesu ya amsa masa, “A rubuce yake, 'Ba da gurasa kadai Mutum zai rayu ba.'” |