23224 | MAT 1:11 | Yosiya shine mahaifin Yekoniya da 'yan'uwansa, dai dai locacin da aka kwashe su zuwa kasar Babila. |
23256 | MAT 2:18 | ''An ji wata murya a Rama, tana kuka da bakin ciki mai zafi, Rahila ce take kuka saboda 'ya'yanta, kuma ta ki ta ta'azantu, domin ba su. |
23340 | MAT 5:37 | Amma bari maganarku ta zama 'I, I', ko kuwa 'A'a, a'a.' Duk abin da ya wuce wannan, daga mugun yake. |
23396 | MAT 7:11 | Saboda haka, idan ku da ku ke miyagu, kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga 'ya'yanku, ina kimanin yadda Ubanku na sama zai ba da abubuwa masu kyau ga duk wadanda suke rokon sa? |
23402 | MAT 7:17 | Haka kowanne itace mai kyau yakan haifi kyawawan 'ya'ya, amma mummunan itace kuwa yakan haifi munanan 'ya'ya. |
23637 | MAT 13:29 | Mai gonar ya ce, 'A'a, kada a garin tuge ciyayin, ku tuge tare da alkamar. |
23860 | MAT 19:29 | Duk wanda ya bar gidaje, 'yan'uwa maza, 'yan'uwa mata, mahaifi, mahaifiya, 'ya'ya, ko gonaki, saboda sunana, zai sami ninkin su dari, ya kuma gaji rai madawwami. |
23965 | MAT 22:24 | cewa, “Mallam, Musa yace, 'Idan mutum ya mutu, bashi da 'ya'ya, dole dan'uwansa ya auri matarsa ya kuwa haifawa dan'uwansa 'ya'ya. |
24979 | LUK 1:17 | Zai yi tafiya a gaban Unbangiji a cikin ruhu da ikon Iliya. Zai yi haka domin ya juya zuciyar Ubanni zuwa ga 'ya'yansu, domin marasa biyayya su yi tafiya a cikin tafarkin adalai. Don ya shirya wa Ubangiji mutanen da aka shirya dominsa.” |
25257 | LUK 6:42 | Don me za ka ce wa dan'uwanka, 'Dan'uwa, bari in cire dan hakin da ke a idonka', bayan kai da kanka ba ka iya ganin gungumen da ke a idonka ba? Kai munafuki! Ka fara cire gungumen da ke a idonka, sa'annan za ka gani da kyau yadda zaka cire hakin da ke a idon dan'uwanka. |
25258 | LUK 6:43 | Domin babu itace mai kyau da ke haifar rubabbun 'ya'ya, ko rubabben itace da zai haifi kyawawan 'ya'ya. |
25333 | LUK 8:19 | Sai mahafiyar Yesu da 'yan'uwansa, su ka zo wurinsa, amma ba su iya zuwa ko kusa da shi ba saboda taron jama'a. |
25334 | LUK 8:20 | Sai wani ya gaya masa, “Ga mahaifiyarka da 'yan'uwanka, su na tsayuwa a waje, su na son ganin ka.” |
25634 | LUK 14:12 | Yesu ya ce wa mutumin da ya gayyace shi, “Idan za ka gayyaci mutum cin abinci ko biki, kada ka gayyaci abokanka, ko 'yan'uwanka, ko danginka, ko makwabtanka masu arziki, kamar yadda suna iya gayyatar ka, sai ya zama an maida maka. |
25648 | LUK 14:26 | “Duk mai zuwa wurina amma bai ki mahaifinsa da mahaifiyarsa, da matarsa, da 'ya'yansa, da 'yan'uwansa maza da mata ba - I, har da ransa ma, ba zai iya zama almajirina ba. |
25719 | LUK 16:30 | Sai mai arziki ya amsa, 'A'a, Baba Ibrahim, idan wani daga cikin matattu ya je wurinsu, zasu tuba.' |
25786 | LUK 18:29 | Yesu ya ce masu, “Hakika, ina gaya maku, ba wanda zai bar gida, ko matarsa, ko 'yan'uwansa, ko iyayensa, ko kuma 'ya'yansa, saboda mulkin Allah, |
26770 | JHN 15:2 | Yakan cire duk wani rashe a cikina da ba ya bada 'ya'ya, mai bada 'ya'ya kuwa ya kan gyara shi domin ya kara bada 'ya'ya. |
26784 | JHN 15:16 | Ba ku kuka zabe ni ba, amma Ni ne na zabe ku, na aike ku don ku je ku bada 'ya'ya, 'ya'yanku kuma su tabbata. Wannan ya zama domin duk abinda kuka roki Uba a cikin sunana, zai baku. |
26919 | JHN 19:25 | Sojojin suka yi wadannan abubuwa. Uwar Yesu, da 'yar'uwarta, da Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magadaliya. Wadannan mataye suna tsaye kusa da gicciyen Yesu. |
27007 | ACT 1:15 | A cikin wadannan kwanaki Bitrus ya tashi tsaye a tsakiyar 'yan'uwa, kimanin mutane dari da ashirin, ya ce, |
27008 | ACT 1:16 | '' 'Yan'uwa, akwai bukatar Nassi ya cika, wanda Ruhu Mai Tsarki ya fada a baya ta bakin Dauda game da Yahuza, wanda ya jagoranci wadanda suka kama Yesu |
27047 | ACT 2:29 | 'Yan'uwa, zan yi magana da ku gabagadi game da baba Dauda: ya mutu kuma aka bizne shi, kuma kabarinsa na nan tare da mu har yau. |
27082 | ACT 3:17 | Ya ku 'yan'uwa, na san kun yi haka ne cikin rashin sani, yadda shugabaninku suka yi. |
27208 | ACT 7:23 | Amma lokacin da yakai shekara arba'in, sai ya yi niyyar ya ziyarci 'yan'uwansa, Isra'ilawa. |
27469 | ACT 13:38 | 'Yan'uwa, ku sani cewa ta wurin mutumin nan aka yi maku wa'azin gafarar zunubai. |
27512 | ACT 15:1 | Wadansu mutane suka zo daga Yahudiya suka koyar da 'yan'uwa, cewa, “Idan ba yi maku kaciya bisa ga al'addar Musa ba, ba za ku sami ceto ba.” |
27546 | ACT 15:35 | Amma Bulus da Barnaba suka tsaya a Antakiya da sauran 'yan'uwa, suna koyar da maganar Ubangiji. |
27592 | ACT 16:40 | Da hakanan ne Bulus da Sila suka fita daga kurkuku, sun je gidan Lidiya. Da Bulus da Sila sun ga 'yan'uwa, sun karfafa su, sa'annan suka bar birnin. |
27601 | ACT 17:9 | Bayan da sun amshi kudi daga wurin Yason da sauran 'yan'uwan, sai suka sake su. |
27739 | ACT 21:7 | Da muka gama tafiyarmu a Taya muka iso Talamayas. A nan ne muka gaisa da 'yan'uwa, muka zamna kwana daya da su. |
27806 | ACT 23:4 | Wanda suka tsaya a gefe suka ce, ''Kada ka zage babban firis na Allah.'' Bulus yace, ''Ban sani ba, 'yan'uwa, cewa shi babban firis ne. |
28160 | ROM 7:1 | 'Yan'uwa, ko baku sani ba (domin ina magana da wadanda suka san shari'a), cewar shari'a na mulkin mutum muddin ransa? |
28163 | ROM 7:4 | Domin wannan, 'yan'uwana, ku ma an sa kun mutu ga shari'a ta wurin jikin Almasihu, saboda a hada ku aure da wani, wato, ga wanda aka tashe shi daga matattu, domin mu haifawa Allah 'ya'ya. |
28226 | ROM 9:3 | Dama ace, a la'anta ni, in rabu da Almasihu saboda 'yan'uwana, wato dangina da suke zuriyata bisa ga jiki. |
28257 | ROM 10:1 | 'Yan'uwana, muradin zuciyata da dukkan addu'oi na ga Allah dominsu shine don su sami ceton. |
28314 | ROM 12:1 | Ina rokon ku 'yan'uwa, saboda yawan jinkan nan na Allah, da ku mika jikunanku hadaya mai rai, mai tsarki kuma abar karba ga Allah. wannan itace hidimarku ta zahiri. |
28332 | ROM 12:19 | 'Yan'uwa, kada ku yi ramako, ku bar Allah ya rama maku. A rubuce yake, '' 'Ramako nawa ne; zan saka wa kowa,' in ji Ubangiji.'' |
28405 | ROM 16:1 | Ina gabatar muku da fibi 'yar'uwarmu, wanda take hidima a Ikilisiya dake cikin Kankiriya. |
28532 | 1CO 5:10 | Ba ina nufin fasikan mutane na wannan duniya ba, ko masu zari, ko 'yan'damfara, ko masu bautar gumaka, tunda kafin ku rabu da su sai kun bar wannan duniya. |
28636 | 1CO 10:1 | Ina son ku sani, 'yan'uwa, cewa ubaninmu duka suna karkashin gajimarai kuma sun bi ta cikin teku. |
28701 | 1CO 11:33 | Saboda haka, ya ku 'yan'uwana, idan kuka tattaru don cin abinci, sai ku jira juna. |
28703 | 1CO 12:1 | Game da baye bayen Ruhu Mai Tsarki 'yan'uwa, bana so ku zama da jahilci. |
28715 | 1CO 12:13 | Gama ta Ruhu daya aka yi wa kowa baftisma cikin jiki daya, ko Yahudawa ko al'ummai, ko bayi ko 'ya'ya, dukan mu kuwa an shayar da mu Ruhu daya. |
28752 | 1CO 14:6 | Amma yanzu, 'yan'uwa, in na zo wurin ku ina magana da harsuna, ta yaya zaku karu dani? ba zaya yiwu ba, sai idan nayi maku magana da wahayi, ko sani, ko anabci, ko koyarwa. |
28766 | 1CO 14:20 | 'Yan'uwa, kada ku zama yara cikin tunani, sai dai a wajen aikin mugunta, ku yi halin jarirai, amma a tunaninku ku girma. |
28785 | 1CO 14:39 | Saboda haka, 'yan'uwa, ku yi marmarin yin annabci sosai, sa'an nan kada ku hana kow yin magana da harsuna. |
28787 | 1CO 15:1 | Yanzu ina tunashshe ku 'yan'uwa, game da bisharar nan da nake shelarwa, wadda kuka karba kuke kuma dogara da ita. |
28817 | 1CO 15:31 | Ina mutuwa kullum. Wannan nake furtawa ta wurin fahariya, 'yan'uwa, wadda nake da ita cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu. |
28836 | 1CO 15:50 | To wannan na fada, 'yan'uwa, cewa nama da jini ba za su gaji mulkin Allah ba. Haka kuma mai lalacewa ba za ya gaji marar lalacewa ba. |
28859 | 1CO 16:15 | Kun dai sani iyalin gidan Sitefanas su suka fara tuba a Akaya, kuma sun bada kansu ga yi wa masu bi hidima. Yanzu ina rokonku, 'yan'uwa, |
28876 | 2CO 1:8 | Gama ba mu so ku rasa sani, 'yan'uwa, game da tsananin da ya same mu a Asiya. An murkushe mu gaba daya har fiye da karfin mu, har ma mun fidda zuciya za mu rayu. |
29001 | 2CO 8:1 | Muna so ku sani, 'yan'uwa, game da alherin Allah da aka bayar ga Ikkilisiyoyin Makidoniya. |
29122 | 2CO 13:11 | A karshe, 'yan'uwa, ku yi farinciki, ku yi aiki don sabuntuwa, ku karfafa, ku yarda da juna, ku zauna cikin salama. Kuma Allahn kauna da salama zai kasance tare da ku. |
29135 | GAL 1:11 | Ina son ku sani fa 'yan'uwa, cewa bisharar da nake shelar ta ba daga mutane take ba. |
29184 | GAL 3:15 | 'Yan'uwa, ina magana bisa ga ka'idojin mutane. Idan mutane sun yi yarjejeniya, babu mai kawar da shi ko a kara shi. |
29210 | GAL 4:12 | Ina rokon ku 'yan'uwa, ku zama kamar yadda nake, domin ni ma na zama kamar ku. Ba ku yi mani laifin komai ba. |
29226 | GAL 4:28 | Yanzu fa, 'yan'uwa, kamar yadda Ishaku yake, haka muke, wato 'ya'yan alkawari. |
29229 | GAL 4:31 | Saboda haka 'yan'uwa, mu ba 'ya'yan baiwa ba ne, a maimakon haka, mu 'ya'yan macen nan ne da ke 'yantacciya. |
29240 | GAL 5:11 | 'Yan'uwa, idan har yanzu wa'azin kaciya nake yi, don me har yanzu ake tsananta mani? Inda haka ne dutsen sanadin tuntube game da gicciye da ya ragargaje. |
29242 | GAL 5:13 | 'Yan'uwa, domin Allah ya kira ku zuwa ga yanci, kada dai ku mori yancin nan ya zama zarafi domin jiki. A maimakon haka ta wurin kauna ku yi wa juna hidima. |
29256 | GAL 6:1 | 'Yan'uwa, idan an kama mutum yana yin wani laifi, ku da kuke da ruhaniya sai ku dawo da mutumin a hanya cikin ruhun tawali'u, ka lura da kanka don kada kai ma ka fada a cikin gwaji. |
29405 | EPH 6:1 | 'Ya'ya, ku yi biyayya ga iyayenku chikin Ubangiji, domin wannan daidai ne. |
29427 | EPH 6:23 | Bari salama ta kasance tare da 'yan'uwa, kauna da bangaskiya daga wurin Allah Uba da Ubangiji Yesu Almasihu. |
29440 | PHP 1:12 | Yanzu ina so ku sani, 'yan'uwa, cewa al'amuran da suka faru da ni sun zama dalilan cin gaban bishara kwarai da gaske. |
29489 | PHP 3:1 | A karshe, 'yan'uwana, ku yi farin ciki cikin Ubangiji. In sake rubuta maku wadannan abubuwa ba wani abu mai nauyi ba ne a gare ni. Wadannan abubuwa zasu tsare ku. |
29501 | PHP 3:13 | 'Yan'uwa, ban dauka cewa na riga na cafka ba tukuna. Amma akwai abu daya da nake yi: ina mantawa da abin da ke baya, ina kutsawa zuwa ga abin da ke gaba. |
29517 | PHP 4:8 | A karshe, 'yan'uwa, duk abin da ke mai gaskiya, duk abin da ya isa ban girma, duk abin da ke mai adalci, duk abin da ke mai tsabta, duk abin da ke karbabbe, duk abin da ke kawo kauna, duk abin da ke da kyakkyawan ambato, idan akwai yabo, yi tunani a kan wadannan abubuwan. |
29638 | 1TH 2:1 | Domin ku da kanku kun sani, 'yan'uwa, cewa zuwan mu gareku, ba a banza yake ba. |
29646 | 1TH 2:9 | Kufa tuna, 'yan'uwa, game da aikinmu da famarmu. Dare da rana muna aiki sosai domin kada mu nawaita wa kowane dayan ku. A lokacin da muke yi maku bisharar Allah. |
29648 | 1TH 2:11 | Don haka kun kuma sani yadda muka rika yi da kowannenku, kamar uba da 'ya'yansa, yadda muka yi ma ku garadi da kuma karfafa ku, mun kuma shaida. |
29651 | 1TH 2:14 | Domin ku 'yan'uwa, kun zama masu koyi da ikilisiyoyin Allah da ke Yahudiya cikin Almasihu Yesu. Domim kuma kun sha wahala irin tamu daga wurin mutanen kasarku kamar yadda suma suka sha a hannun Yahadawa. |
29654 | 1TH 2:17 | Mu kuma, 'yan'uwa, mun rabu daku na karamin lokaci, a zahiri, ba a zuciya ba, mun kuma yi iyakar kokarinmu da marmarin ganin fuskarku. |
29664 | 1TH 3:7 | Sabili da haka, 'yan'uwana, mun sami ta'aziyya tawurinku domin bangaskiyarku, a cikin dukkan bakin cikinmu da shan wuyamu. |
29671 | 1TH 4:1 | A karshe, 'yan'uwa, muna karfafa ku kuma muna yi maku gargadi cikin Ubangiji Yesu. Yadda kuka karbi umarni a garemu game da yadda dole za kuyi tafiya kuma ku gamshi Allah, kuma a cikin wannan hanya ku tafi, ku kuma wuce haka. |
29679 | 1TH 4:9 | Game da kaunar 'yan'uwa, baku bukatar wani ya sake rubuta maku, gama ku da kanku Allah ya koyar da ku kaunar 'yan'uwa. |
29680 | 1TH 4:10 | Ba shakka, kunayin haka ga dukkan 'yan'uwa wadanda ke cikin dukkan Makidoniya. Amma muna gargadin ku 'yan'uwa, kuyi haka bugu da kari. |
29683 | 1TH 4:13 | Bamu so ku zama da rashin fahimta ba, 'yan'uwa, game da wadanda sukayi barci, domin kada kuyi bacin rai kamar sauran wadanda basu da tabbacin abinda ke gaba. |
29689 | 1TH 5:1 | Yanzu fa game da zancen lokatai da zamanai 'yan'uwa, ba ku da bukatar a rubuta maku wani abu. |
29692 | 1TH 5:4 | Amma ku, 'yan'uwa, ai ba cikin duhu kuke ba har da wannan rana zata mamaye ku kamar barawo. |
29700 | 1TH 5:12 | Muna rokon ku, 'yan'uwa, ku bada daraja ga wadanda suke aiki a tsakaninku wadanda kuma suke shugabanci a kan ku cikin Ubangiji, wadanda kuma suke horonku. |
29798 | 1TI 2:15 | Duk da haka, zata sami ceto ta wurin haifuwar 'ya'ya, idan suka ci gaba cikin bangaskiya, da kauna da tsarki da sahihiyar zuciya. |
29840 | 1TI 5:10 | A san ta da kyawawan ayyuka, ko ta kula da 'ya'yanta, ko tana mai karbar baki, ko mai wanke kafafun masubi, ko mai taimakon wadanda ake tsanantawa, mai naciya ga kowanne kyakkyawan aiki. |
29844 | 1TI 5:14 | Saboda haka ina so gwamraye masu kuruciya su yi aure, su haifi 'ya'ya, su kula da gida, domin kada a ba magabci zarafin zargin mu ga aikata mugunta. |
30286 | HEB 12:7 | Ku daure wahala a matsayin horo. Allah yana yi da ku kamar 'ya'yansa, domin kuwa wanne da ne wanda ubansa bazai yi masa horo ba? |
30330 | HEB 13:22 | 'Yan'uwa, yanzu dai ina karfafa ku, da ku jurewa takaitacciyar maganar karfafawar da na rubuto maku. |
30335 | JAS 1:2 | Ku dauke su duka da farin ciki, 'yan'uwana, duk sa'adda kuke fuskantar jarabobi. |
30361 | JAS 2:1 | Ya ku 'yan'uwana, muddin kuna rike da bangaskiyar ku ga Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangijin daukaka, kada ku nuna bambanci ga wadansu mutane. |
30374 | JAS 2:14 | Ina amfanin haka, 'yan'uwana, idan wani ya ce yana da bangaskiya, kuma ba shi da ayyuka? Wannan bangaskiyar ba za ta cece shi ba, ko za ta iya? |
30396 | JAS 3:10 | Bakin da ake sa albarka, da shi kuma ake la'antarwa. 'Yan'uwana, ai, wannan bai kamata ba. |
30428 | JAS 5:7 | Saboda haka ku yi hakuri, 'yan'uwa, har sai zuwan Ubangiji. Duba, yadda manomi ya kan jira kaka mai amfani daga gona. Da hakuri yake jiran ta har sai ta karbi ruwa na fari da na karshe. |
30430 | JAS 5:9 | Kada ku yi gunaguni, 'Yan'uwana, game da juna, don kada a hukunta ku. Duba, mai shari'a na tsaye a bakin kofa. |
30431 | JAS 5:10 | Dauki misali, 'yan'uwa, daga shan wuya da hakurin annabawa, wadanda suka yi magana a cikin sunan Ubangiji. |
30433 | JAS 5:12 | Fiye da komai duka, 'yan'uwana, kada ku yi rantsuwa, ko da sama, ko da kasa, ko da kowace irin rantsuwa ma. A maimakon haka bari “I” ya zama “I”, in kuwa kun ce “A'a”, ya zama “A'a”, don kada ku fada a cikin hukunci. |
30440 | JAS 5:19 | Ya ku 'yan'uwana, idan wanin ku ya baude wa gaskiya, wani kuma ya dawo da shi, |
30463 | 1PE 1:22 | Da shike kun tsarkake rayukanku cikin biyayyar ku ga gaskiya zuwa ga sahihiyar kauna ta 'yan'uwa, sai ku kaunaci junanku da zuciya mai gaskiya. |
30483 | 1PE 2:17 | Ku girmama dukkan mutane. Ku kaunaci 'yan'uwa, kuji tsoron Allah. Ku girmama sarki. |
30499 | 1PE 3:8 | Daga karshe, dukanku ku hada hankulanku, ku zama masu juyayi, masu kauna kamar 'yan'uwa, masu taushin zuciya, masu tawali'u. |
30553 | 2PE 1:7 | Ta wurin bin Allah, ku kara da kauna irin ta 'yan'uwa, ta wurin kauna irin ta 'yan'uwa, ku kara kauna. |
30556 | 2PE 1:10 | Saboda haka, 'yan'uwa, kuyi iyakacin kokari ku tabbatar da kiranku da zabenku. Idan kun yi wadannan abubuwan, baza ku yi tuntube ba. |