24542 | MRK 7:10 | Koda shike Musa ya rubuta cewa, “ka girmama Ubanka da Uwarka”, kuma, “duk wanda ya zagi Ubansa ko Uwatasa, ya cancanci mutuwa nan take”. |
26728 | JHN 13:29 | Wadansu sun yi tsamanin cewa, tun da Yahuza ne ke rike da jakkar kudi, Yesu ya ce masa, “Ka sayi abinda muke bukata don idin”, ko kuma ya bada wani abu domin gajiyayyu. |
26898 | JHN 19:4 | Sai Bilatus ya sake fita waje yace masu, “Dubi, zan kawo maku mutumin domin ku sani ban same shi da wani laifi ba”, |
28359 | ROM 14:11 | Domin a rubuce yake, “ Na rantse, “inji Ubangiji”, kowacce gwiwa zata rusuna mani, kowanne harshe kuwa zai yabi Allah.” |
28547 | 1CO 6:12 | Dukkan abu halal ne a gare ni”, amma ba kowanne abu ne mai amfani ba. “Dukan abu halal ne a gare ni,” amma ba zan yarda wani abu ya mallake ni ba. |
28548 | 1CO 6:13 | “Abinci don ciki ne, kuma ciki don abinci ne”, amma Allah za ya kawar da su duka. Ba a yi jiki saboda fasikanci ba. Maimakon haka, jiki don Ubangiji ne, kuma Ubangiji zai yi wa jiki tanaji. |
28767 | 1CO 14:21 | A rubuce yake a shari'a cewa, “zan yi magana da mutanen nan ta wurin mutane masu bakin harsuna, da kuma lebunan baki. Duk da haka kuwa ba za su saurare ni ba”, in ji Ubangiji. |
29307 | EPH 2:11 | Saboda haka ku tuna da ku al'ummai ne a dabi'ar jiki. Ana kiranku “marasa kaciya”, abin da ake kira kaciya cikin jiki wadda hannayen mutane ke yi. |
29364 | EPH 4:25 | Saboda haka ku watsar da karya. “Fadi gaskiya ga makwabcin ka”, domin mu gabobin juna ne. |
30690 | 1JN 4:20 | Idan wani ya ce,”Ina kaunar Allah”, amma yana kin dan'uwansa, makaryaci ne. Domin wanda baya kaunar dan'uwansa da yake gani, ba zai iya kaunar Allah da bai taba gani ba. |
30773 | REV 1:8 | “Nine na farko da na karshe”, in ji Ubangiji Allah, “Wanda yake shine a yanzu, shine wanda ya kasance a da, kuma shi ne mai zuwa nan gaba, Mai iko duka.” |