23376 | MAT 6:25 | Saboda haka ina gaya maku, kada ku damu a kan rayuwarku, game da abin da za ku ci, da abin da za ku sha- ko kuwa jikinku, abin da za ku yi tufafi da shi. Ashe rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba? |
23976 | MAT 22:35 | Daya daga cikinsu, masanin shari'a, yayi masa tambaya, yana gwada shi- |
23980 | MAT 22:39 | Doka ta biyu kuma kamar ta take- 'Ka kaunaci makwabcinka kamar kanka.' |
24788 | MRK 13:2 | Ya ce masa, ka ga wadannan kyawawan gine- ginen? babu wani dutsen da za a bar shi akan dan'uwansa, da ba za a rushe shi ba.” |
24793 | MRK 13:7 | In kuka ji labarin yake- yake, da jita-jitarsu kada ku damu, wannan zai faru, amma karshen duniya bai gabato ba. |
26700 | JHN 13:1 | Kamin bukin idin ketarewa, sa'adda Yesu ya san lokaci ya yi da zai tashi daga wannan duniya zuwa wurin Uba, da yake ya kaunaci nasa wadanda ke duniya- ya kaunace su har karshe. |
28228 | ROM 9:5 | Dukkan ubanni nasu ne daga cikinsu Almasihu ya fito bisa ga jiki- wanda shi ke Allah bisa kowa. Yabo ya tabbata a gare shi har abada. Amin. |
28509 | 1CO 4:8 | Kun rigaya kun sami dukkan abubuwan da kuke bukata! Kun rigaya kun zama mawadata! Kun rigaya kun fara mulki- kuma ba tare da mu ba! Hakika, marmarina shine ku yi mulki, domin mu yi mulki tare da ku. |
28565 | 1CO 7:10 | Ga masu aure kwa, ina bada wannan umarni- ba ni ba, amma Ubangiji: “Kada mace ta rabu da mijinta.” |
28591 | 1CO 7:36 | Amma idan wani yana tunani da cewa baya yin abinda ya dace ga budurwarsa- idan ta wuce shekarun aure, kuma hakan ya zama dole- sai yayi abinda yake so. Ba zunubi yake yi ba. Sai suyi aure. |
28897 | 2CO 2:5 | Idan wani ya kawo sanadin bacin rai, ba ni kadai ya kawo wa wannan abin ba, amma ta wani fannin- domin kada a tsananta- har a gare ku duka. |
28916 | 2CO 3:7 | To hidimar da ta haifar da mutuwa- wadda aka rubuta bisa duwatsu- ta zo cikin irin wannan daukaka da har Israila ba su iya kallon fuskar Musa kai tsaye ba. Wannan kuwa saboda daukakar da ke fuskarsa ne, daukaka mai shudewa. |
29093 | 2CO 12:3 | Kuma na san wannan mutumin-ko cikin jiki ko kuma ba cikin jiki ba, ban sani ba, Allah ya sani- |
29870 | 1TI 6:15 | Allah zai nuna bayyanuwarsa a daidai lokaci- Allah, mai albarka, Makadaicin iko, Sarkin da ke sarauta, Ubangiji mai mulki. |
30014 | PHM 1:9 | duk da haka sabo da kauna, na fi so in roke ka- Ni, Bulus, dattijo, a yanzu kuma ga ni dan kurkuku domin Almasihu Yesu. |
30229 | HEB 10:29 | Wanne irin hukunci kuke tsammani ya dace ga wadanda suka raina Dan Allah, duk wadanda suka maida jinin alkawarin nan kamar ba tsarkakakke ba, wanda ta wurin jinin nan ne aka kebe shi ga Allah- wadanda suka wulakantar da Ruhun alheri? |
30774 | REV 1:9 | Ni, Yahaya- dan'uwan ku da wanda ke tarayya daku cikin shan wahala, da mulki da tsawon jimrewa wadanda ke cikin Yesu - ina tsibirin da ake kira Batmusa saboda maganar Allah da kuma shaida game da Yesu. |
31119 | REV 20:12 | Na ga matattu manya da kanana- suna tsaye gaban kursiyin, aka bude litattafai. Sai aka bude wani littafi - Littafin rai. Aka yi wa matattu shari'a bisa ga abinda aka rubuta cikin litattafan, gwargwadon ayyukansu. |