23234 | MAT 1:21 | Za ta haifi Da, za ka kira sunansa Yesu, domin za ya ceci mutanensa daga zunubansu.” |
23236 | MAT 1:23 | “Duba, budurwa za ta sami juna biyu sannan za ta haifi da, za su kira sunansa Immanuel”-ma'ana, “Allah tare da mu.” |
23246 | MAT 2:8 | Ya aike su Baitalami, ya ce, ''Ku je ku binciko mani dan yaron da kyau. Idan kun same shi, ku kawo mani labari, don ni ma in je in yi masa sujada.” |
23251 | MAT 2:13 | Bayan sun tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, ''Tashi, ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu zuwa kasar Masar, ka zauna a can sai na fada maka, don Hirudus yana shirin binciko dan yaron ya hallaka shi.” |
23263 | MAT 3:2 | “Ku tuba, domin mulkin sama ya kusa.” |
23273 | MAT 3:12 | Kwaryar shikarsa na hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai, ya tara alkamarsa ya sa a rumbunsa, amma zai kona buntun da wutar da ba za a iya kashewa ba.” |
23276 | MAT 3:15 | Yesu ya amsa masa ya ce, “Bari ya zama haka a yanzu, domin a cika dukan adalci.” Sai Yahaya ya yarje masa. |
23281 | MAT 4:3 | Sai mai jarabtar nan ya zo, ya ce masa, “Idan kai Dan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama gurasa.” |
23294 | MAT 4:16 | Mutane mazauna duhu suka ga babban haske, sannan ga wadanda ke zaune a yankin da inuwar mutuwa, haske ya keto masu.” |
23295 | MAT 4:17 | Daga lokacin nan, Yesu ya fara wa'azi, yana cewa, “Ku tuba domin mulkin sama ya kusa.” |
23297 | MAT 4:19 | Yesu ya ce masu, “Ku zo, ku biyo ni, zan mai da ku masuntan mutane.” |
23366 | MAT 6:15 | In kuwa ba ku yafe wa mutane laifuffukansu ba, Ubanku ma ba zai yafe muku laifuffukanku ba.” |
23369 | MAT 6:18 | don kada mutane su gane kuna azumi, sai dai Ubanku da yake a asirce. Kuma Ubanku da ke ganin abinda ke a asirce, zai saka maku.” |
23416 | MAT 8:2 | Sai wani kuturu ya zo gunsa ya yi masa sujada, ya ce, “Ubangiji, in dai ka yarda, za ka iya tsarkake ni.” |
23417 | MAT 8:3 | Yesu ya mika hannunsa ya taba shi, ya ce, “Na yarda, ka tsarkaka.” Nan da nan aka tsarkake shi daga kuturtarsa. |
23420 | MAT 8:6 | Ya ce, Ubangiji, bawana na kwance shanyayye a gida, yana shan azaba kwarai.” |
23421 | MAT 8:7 | Yesu ya ce masa, “Zan zo in warkar da shi.” |
23426 | MAT 8:12 | Amma 'ya'yan mulkin kuwa sai a jefa su cikin matsanancin duhu. Can za su yi kuka da cizon hakora.” |
23431 | MAT 8:17 | Ta haka kuwa maganar annabi Ishaya ta samu cika cewa, “Shi da kansa ya debe rashin lafiyar mu, ya dauke cututtukan mu.” |
23433 | MAT 8:19 | Sai wani marubuci ya zo ya ce masa, “Malam, zan bi ka duk inda za ka je.” |
23434 | MAT 8:20 | Yesu ya ce masa, “Yanyawa suna da ramukansu, tsuntsayen sama kuma da shekunan su, amma Dan mutum ba shi da wurin da zai kwanta.” |
23435 | MAT 8:21 | Wani cikin almajiran ya ce masa, “Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne mahaifina.” |
23436 | MAT 8:22 | Amma Yesu ya ce masa, “Bari matattu su binne matattunsu.” |
23445 | MAT 8:31 | Sai al'janun suka roki Yesu suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan.” |
23446 | MAT 8:32 | “Yesu ya ce masu, “To, ku je.” Sai aljanun suka fita, suka shiga cikin aladun. Sai kuwa duk garken suka rugungunta ta gangaren, suka fada cikin tekun, suka hallaka a ruwa. |
23552 | MAT 11:24 | Amma ina ce maku, za a saukaka wa Sodom a ranar shari'a fiye da ku.” |
23558 | MAT 11:30 | Gama karkiyata mai sauki ce, kaya na kuma ba shi da nauyi.” |
23560 | MAT 12:2 | Amma da Farisawa suka gan su, sai su ka ce wa Yesu. “Duba, almajiranka su na yin abin da doka ta haramta a ranar Asabaci.” |
23566 | MAT 12:8 | Gama Dan mutum shine Ubangijin Asabaci.” |
23570 | MAT 12:12 | Yaya za a kwatanta darajar mutum da tunkiya! Saboda haka ya halarta a yi alheri ranar Asabaci.” |
23571 | MAT 12:13 | Sai Yesu ya ce wa mutumin nan “Mika hannun ka.” Ya mike hannunsa, sai hannun nan ya dawo lafiyaye kamar dayan hannunsa. |
23582 | MAT 12:24 | Amma da Farisawa su ka ji wannan al'ajibi, sai su ka ce, “Mutumin nan yana fitar da aljannu ta wurin Bahalzabuba sarkin aljannu ne.” |
23595 | MAT 12:37 | Gama ta wurin maganganun ku, za a 'yantar da ku, ta wurin maganganun ku kuma za a kashe ku.” |
23596 | MAT 12:38 | Sa'annan wadansu Malaman Attaura, da Farisawa suka amsa suka ce wa Yesu, “Mallam, muna so mu ga wata alama daga gare ka.” |
23608 | MAT 12:50 | Gama duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda ya ke cikin sama, shine dan'uwana, da 'yar'uwata da mahaifiyata.” |
23631 | MAT 13:23 | Shi wanda aka shuka a kasa mai kyau, wannan shine wanda ya ji maganar, ya kuma fahimce ta. Wannan shine wanda ba da 'ya'ya da gaske; wadansu ribi dari, wadansu sittin, wasu kuma talatin.” |
23640 | MAT 13:32 | Wannan iri shine mafi kankanta cikin dukan iri. Amma bayan ya yi girma, sai ya fi dukan ganyaye dake lambun. Ya zama itace, har ma tsuntsayen sama su yi sheka a rassansa.” |
23641 | MAT 13:33 | Yesu ya sake fada masu wani misali. “Za a kwatanta mulkin sama da yisti da mace takan dauka ta kwaba gari da shi mudu uku har sai ya yi kumburi.” |
23643 | MAT 13:35 | Wannan ya kasance ne domin abinda annabin ya fada ya zama gaskiya, da ya ce, “Zan buda bakina da misali. In fadi abubuwan da ke boye tun daga halittar duniya.” |
23660 | MAT 13:52 | Sai Yesu ya ce masu, “Saboda haka kowane malamin attaura da ya zama almajirin mulkin sama, yana kamar mutum mai gida wanda ya zaro tsoho da sobon abu daga taskarsa.” |
23670 | MAT 14:4 | Ya ce masa, “Bai kamata ka dauke ta a matsayin matarka ba.” |
23681 | MAT 14:15 | Da maraice ya yi, almajiransa su ka zo su ka ce masa, “Wannan wuri jeji ne, dare kuwa ya riga ya yi. Ka sallami taron domin su je cikin kauyukan nan, su sayo wa kansu abinci.” |
23682 | MAT 14:16 | Amma Yesu ya ce masu, “Babu amfanin tafiyar su, ku basu abin da za su ci.” |
23683 | MAT 14:17 | Suka ce masa, “Muna da gurasa guda biyar da kifi biyu ne kawai.” |
23684 | MAT 14:18 | Yesu ya ce, “Ku kawo mani su.” |
23693 | MAT 14:27 | Amma Yesu yayi magana da su nan da nan yace, “Ku yi karfin hali! Ni ne! Kada ku ji tsoro.” |
23694 | MAT 14:28 | Bitrus ya amsa masa cewa, “Ubangiji, idan kai ne, ka umarce ni in zo wurin ka bisa ruwan.” |
23699 | MAT 14:33 | Sai almajiran dake cikin kwale-kwalen su ka yi wa Yesu sujada suna cewa, “Hakika kai Dan Allah ne.” |
23704 | MAT 15:2 | “Meyasa almajiranka suke karya al'adar dattawa? Don ba su wanke hannayen su kafin su ci abinci.” |
23711 | MAT 15:9 | Suna mani sujada a banza, domin suna koyar da dokokin mutane a matsayin rukunansu.” |
23713 | MAT 15:11 | ba abin da ke shiga baki ke kazantar da mutum ba. Sai dai, abin da ke fitowa daga baki, wannan shi ya ke kazantar da mutum.” |
23716 | MAT 15:14 | Ku kyale su kawai, su makafin jagora ne. In makaho ya ja wa wani makaho gora dukan su za su fada rami.” |
23722 | MAT 15:20 | Wadannan su ne abubuwan da ke kazantar da mutum. Amma ci da rashin wanke hannu baya kazantar da mutum.” |
23724 | MAT 15:22 | Sai wata mace Bakan'aniya ta zo daga wannan yanki. Ta daga murya ta ce,” Ka yi mani jinkai, Ubangiji, Dan Dauda; 'yata tana cikin bakar azaba da aljani.” |
23725 | MAT 15:23 | Amma Yesu bai ce mata kome ba. Almajiransa suka zo suka roke shi, suna cewa, “Ka sallame ta, domin tana bin mu da ihu.” |
23727 | MAT 15:25 | Amma ta zo ta durkusa a gabansa, tana cewa, “Ubangiji ka taimake ni.” |
23729 | MAT 15:27 | Ta ce, “I, Ubangiji, amma ko kananan karnuka suna cin barbashin da ke fadowa daga teburin maigida.” |
23734 | MAT 15:32 | Yesu ya kira almajiransa zuwa gun sa sai ya ce, “Ina jin tausayin taron, sun kasance tare da ni kwana uku ke nan kuma ba su da abin da za su ci. Bana so in sallame su ba tare da sun ci abinci ba, domin kada su suma a hanya.” |
23735 | MAT 15:33 | Almajiran suka ce masa, “A ina zamu sami isasshiyar gurasa a wannan wuri da babu kowa har ta ishi babban taron nan.” |
23736 | MAT 15:34 | Yesu ya ce masu, “Gurasa nawa ku ke da ita?” Suka ce, “Bakwai da 'yan kifi marasa yawa.” |
23745 | MAT 16:4 | Mugun zamani, maciya amana suna neman alama, amma babu wata alama da za a nuna sai ta Yunusa.” Daga nan sai Yesu ya tafi. |
23747 | MAT 16:6 | Yesu ya ce masu, “Ku kula ku kuma mai da hankali da yisti na Farisawa da Sadukiyawa.” |
23748 | MAT 16:7 | Sai almajiran suka fara magana da junansu suka ce, “Ko saboda bamu kawo gurasa bane.” |
23752 | MAT 16:11 | Yaya kuka kasa fahimta cewa ba game da gurasa nake yi maku magana ba? Ku yi hankali ku kuma lura da yistin Farisawa da Sadukiyawa.” |
23755 | MAT 16:14 | Suka ce, “Wadansu suna cewa Yahaya mai baftisma; wadansu Iliya, saura suna cewa Irmiya, ko daya daga cikin annabawa.” |
23757 | MAT 16:16 | Sai Saminu Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Almasihu, Dan Allah mai rai.” |
23763 | MAT 16:22 | Sai Bitrus ya kai shi a gefe ya tsauta masa, cewa, “Wannan ya yi nesa da kai, Ubangiji; wannan ba zai taba faruwa da kai ba.” |
23764 | MAT 16:23 | Amma Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Ka koma bayana, Shaidan! Kai sanadin tuntube ne gare ni, domin ba ka damuwa da abubuwan da suke na Allah, amma sai abubuwan mutane.” |
23769 | MAT 16:28 | Gaskiya ina gaya maku, akwai wadansun ku da ke tsaye a nan, da ba za su dandana mutuwa ba sai sun ga Dan Mutum na zuwa cikin mulkinsa.” |
23773 | MAT 17:4 | Bitrus ya amsa ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ya yi kyau da muke a wurin nan. In kana so, zan yi bukkoki uku daya dominka, daya domin Musa, daya domin Iliya.” |
23774 | MAT 17:5 | Sa'adda yake cikin magana, sai, girgije mai haske ya rufe su, sai murya daga girgijen, tana cewa, “Wannan kaunattacen Dana ne, shi ne wanda yake faranta mani zuciya. Ku saurare shi.” |
23776 | MAT 17:7 | Sai Yesu ya zo ya taba su ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.” |
23778 | MAT 17:9 | Yayin da suke saukowa daga dutsen, Yesu ya umarce su, ya ce, “Kada ku fadawa kowa wannan wahayin, sai Dan Mutum ya tashi daga matattu.” |
23785 | MAT 17:16 | Na kawo shi wurin almajiran ka, amma ba su iya su warkar da shi ba.” |
23786 | MAT 17:17 | Yesu ya amsa ya ce, “Marasa bangaskiya da karkataccen zamani, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan jure da ku? Ku kawo shi nan a wurina.” |
23792 | MAT 17:23 | Kuma za su kashe shi, a rana ta uku zai tashi.” Sai almajiransa suka yi bakin ciki kwarai. |
23822 | MAT 18:26 | Sai baran ya fadi kasa, ya rusuna a gaban ubangidansa ya ce, “Maigida, kayi mani hakuri, zan biya duk abin da na karba.” |
23898 | MAT 21:3 | Idan wani ya gaya maku wani abu game da haka, sai ku ce, 'Ubangiji ne yake bukatarsu,' mutumin kuwa zai aiko ku da su nan da nan.” |
23900 | MAT 21:5 | “Ku cewa diyar Sihiyona, duba, ga sarkinki na zuwa wurin ki, mai tawali'u ne, kuma akan jaki wanda aholaki ne.” |
23906 | MAT 21:11 | Sai jama'a suka amsa, “Wannan shine Yesu annabi, daga Nazaret ta Galili.” |
23908 | MAT 21:13 | Ya ce masu, “A rubuce yake, 'Za a kira gidana gidan addu'a,' amma kun mayar dashi kogon 'yan fashi.” |
23914 | MAT 21:19 | Da ya ga bishiyar baure a bakin hanya, sai yaje wurin amma bai sami kome ba sai dai ganye. Sai ya ce mata, “Kada ki kara yin 'ya'ya har abada.” Sai nan take bishiyar bauren ta bushe. |
23917 | MAT 21:22 | Kome kuka roka cikin addu'a, in dai kun gaskanta, za ku samu.” |
23921 | MAT 21:26 | Amma in munce, ' daga mutune,' muna tsoron jama'a, saboda sun san Yahaya annabi ne.” |
23922 | MAT 21:27 | Sai suka amsa ma Yesu suka ce, ''Bamu sani ba.” Shi ma yace masu, “Nima bazan gaya maku ko da wane iko nake yin abubuwan nan ba. |
23926 | MAT 21:31 | Wanene a cikin 'ya'ya biyun nan yayi nufin ubansa?” Suka ce, “na farkon.” Yesu ya ce masu, “Hakika ina gaya maku, masu karbar haraji da karuwai za su shiga mulkin Allah kafin ku. |
23936 | MAT 21:41 | Suka ce masa, “Zai hallaka mugayen manoman nan ta hanya mai tsanani, zai kuma bada gonar haya ga wadansu manoman, mutanen da za su biya, lokacin da inabin ya nuna.” |
23939 | MAT 21:44 | Duk wanda ya fadi akan dutsen nan zai ragargaje. Amma duk wanda dutsen ya fadawa, zai nike.” |
23945 | MAT 22:4 | Sai sarkin ya sake aiken wasu bayin, yace, “Ku gaya wa wadanda aka gayyata, “Duba, na shirya liyafata. An yanka bajimaina da kosassun 'yanmarukana, an gama shirya komai. Ku zo wurin bikin auren.” |
23960 | MAT 22:19 | Ku nuna mani sulen harajin.” Sai suka kawo masa sulen. |
23962 | MAT 22:21 | Suka ce masa, “Na Kaisar.” Sai Yesu ya ce masu, “To ku ba Kaisar abubuwan dake na Kaisar, Allah kuma abubuwan dake na Allah.” |
23969 | MAT 22:28 | To a tashin matattu, matar wa zata zama a cikin su bakwai din? Don duk sun aure ta.” |
23973 | MAT 22:32 | 'Nine Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku, da Allah na Yakubu'? Allah ba Allah na matattu bane, amma na rayayyu.” |
23981 | MAT 22:40 | Akan wadannan dokoki ne dukkan shari'a da annabawa suka rataya.” |
23983 | MAT 22:42 | Yace, “Me kuke tunani game da Almasihu? Shi dan wanene?” Suka ce masa, ''Dan Dauda ne.” |
23985 | MAT 22:44 | “Ubangiji ya cewa wa Ubangijina, zauna a hannun damana, har sai na mai da makiyanka matakin sawayenka.” |
24028 | MAT 24:2 | Amma ya amsa masu yace, “kun ga dukkan wadannan abubuwan? Ina gaya maku gaskiya, ba ko dutse daya da za'a bari akan dan'uwansa wanda ba za'a rushe shi ba.” |
24030 | MAT 24:4 | Yesu ya amsa yace dasu, “Ku kula kada wani yasa ku kauce.” |
24123 | MAT 25:46 | Wadannan kuwa zasu tafi cikin madawwamiyar azaba amma adalai zuwa rai madawwami.” |
24128 | MAT 26:5 | Amma suna cewa, “Ba a lokacin idin ba, domin kada tarzoma ta tashi daga cikin mutane.” |