23726 | MAT 15:24 | Amma Yesu ya amsa ya ce, “Ba a aike ni gun kowa ba sai dai ga batattun tumakin gidan Isra'ila.” |
24159 | MAT 26:36 | Sa'anna Yesu ya tafi tare da su, wurin da ake kira Getsaimani sai yace wa almajiransa, ''Ku zauna a nan ni kuma zan je gaba in yi addu'a.” |
24636 | MRK 9:29 | Ya ce masu, “Ai, irin wannan ba ya fita sai da addu'a.” |
24987 | LUK 1:25 | “Wannan shi ne abin da Allah ya yi mani da ya dube ni domin ya dauke kunyata a gaban jama'a.” |
25074 | LUK 2:32 | Haske ne na wahayi ga al'ummai, kuma daukakar mutanenka Isra'ila.” |
25202 | LUK 5:26 | Kowa yana ta mamaki kuma suka daukaka Allah. Suna cike da tsoro, suna cewa, “Yau mun ga abubuwan al'ajibi.” |
25223 | LUK 6:8 | Amma ya san abin da suke tunani, sai ya ce wa mai shanyeyen hannun, “Tashi, ka tsaya a nan tsakiyar jama'a.” Sai mutumin ya tashi ya tsaya a nan. |
25430 | LUK 9:60 | Amma Yesu ya ce masa, “Ka bar matattu su bizine matattunsu; amma kai ka tafi ka yi wa mutane shelar mulkin Allah a ko'ina.” |
26409 | JHN 7:12 | Akwai maganganu dayawa a kansa cikin taron. Wadansu suna cewa, “shi mutumin kirki ne.” Wadansu kuma suna cewa,”A'a yana karkatar da hankalin jama'a.” |
27632 | ACT 18:6 | Lokacin da Yahudawa suka tayar masa suna zarginsa. Bulus ya kakkabe rigansa a gabansu yana cewa, “Alhakin jininku yana kanku; daga yanzu zan koma wurin al'ummai.” |
27914 | ACT 26:23 | wato lallai Almasihu zai sha wahala, ya kuma zama na farko da za'a rayar daga matattu ya kuma yi shelar haske zuwa ga mutanen Yahudawa da Al'ummai.” |
27989 | ACT 28:22 | Amma muna so mu ji daga gare ka abin da kayi tunani ka kuma gani game da wannan darikar, gama mun sani ana kushenta a ko'ina.” |
28063 | ROM 3:4 | Bazai taba zama haka ba. Maimakon haka, bari Allah ya zama mai gaskiya, ko da kowanne mutum makaryaci ne. Kamar yadda aka rubuta, “Domin a nuna kai mai adalci cikin maganganunka, kuma kayi nasara a lokacin da aka kawo ka gaban shari'a.” |
30230 | HEB 10:30 | Domin mun san wanda yace, “Ramako nawa ne; Zan yi sakayya.'' Sa'annan kuma, “Ubangiji zai hukumta jama'arsa.” |
30466 | 1PE 1:25 | amma maganar Ubangiji tabbatacciya ce har abada. “Wannan ita ce maganar bishara wadda akayi maku wa'azinta.” |
30837 | REV 4:1 | Bayan wadannan abubuwa na duba, sai ga budaddiyar kofa a sama. Muryar fari da na ji kamar kakaki, na cewa hauro in nuna maka abubuwan da dole za su faru bayan wadannan al'amura.” |